NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL


Kwace yake yana kallon rufin d’akin yana wasa da zoben yatsarshi, shiru d’akin yale na wasu tsawon mintuna kafin ya tashi zaune da sauri yana kallon Richard yace “Kana ganin bata cikin had’ari yanzu? Anya zan iya bacci nesa da ita bayan nasan wannan jarababben Kabeer d’in yana garin nan?”

Mik’ewa yayi ya fara kai da kawo a tsakiyar d’akin, da sauri Richard dake dagular comp. ya juyo yace “Kai maza yanzu haka fa tana amsa kiran Kabeer d’in nan ne.”

Da sauri ya maysa yana dafa kafad’arshi yace “Me suke tattaunawa akai?”

D’aga kafad’a yayi yace “Wannan kutsen kuma saina shiga n’aurar sadarwar kampanin layin, abune mai wuya gaskiya.”

Mik’ewa tayi tsaye yana fad’in “Amma ai a camarorin tsaron bai nuna mana ya sake dawowa gidan ba ko?”

Girgiza kai yayi alamar a’a, wani iska ya furzar yana d’aga kanshi sama, girgiza kai ya shiga yi yana fad’in “Taurin kai gareta, me yake fad’a mata? Had’uwa yake son yi da ita ko me?”

Sauke kanshi yayi daga kallon sama yana dafe k’ugu yaja dogon tsaki, kallon Richard yayi yace “Ka bud’e min layi na zanyi kira.”

Da kai ya amsa maasa da to ya shiga wani danne danne, baifi second shida zuwa bakwai ba ya kalleshi yace “An bud’e.”

Da sauri ya ciro wayar ya nemi lambar Farha, lokacin harta koma d’aki ita ma tana shirin kwantawa taji kiran, da sauri ta d’auki wayar ta d’ora a kunne, saida ya gama shan k’amshi da basarwa yace “Sannu.”

Da sauri tace “Yaya Salahadeen, kana ina ne ina ka shige tun rana baka dawo ba?”

A dakile yace “Nayi jiranki baki fito ba ai? Kina ina yanzun?”

Marairaicewa tayi tace “Kayi hak’uri yaya Salahadeen dan Allah ka dawo gida, wallahi na gane kuskure na kuma na ba ita ma Sarah hak’uri, kayi hak’uri dan Allah kaji?”

Can k’asan mak’oshi yace “Tana ina?”

A hankali tace “Tana d’akinta tun d’azu ta shiga tace bacci take ji.”

A hankali shima yace “Kin tabbatar baccin take? Farha ki taimaka ki duba min d’akinta ki gani, rayuwarta na cikin hatsari ita kuma hauka ne a kanta bata damu da kanta ba.”

A hankali ita tace “Lafiya yaya Salahadeen? Wani abu ya faru ne?”

Saida ya sauke ajiyar zuciyar data jita har kunne yana lumshe ido yace “Babu abinda ya faru yanzu, amma akwai yiwuwar ya faru nan gaba kad’an.”

Da sauri tace “Shikenan bara na duba na gani.” Fita tayi daga d’akin da sauri ta nufi b’angaren d’akin Sarah, tana bud’awa kan gabjejen gadon ta fara sauke idonta, k’ofar data bud’a bata shiga ta hanata ganin Sarah dake kwance k’asan sallaya, da mamaki ta k’ara wara ido kan gadon, cikin fad’uwar gaba da wani tsoro tace “Yaya Salahadeen bata d’akin fa, wallahi bata nan sai gadon kawai.”

Da wani irin k’arfi da manta a waya ne yace “Ohhh shiiiit, me yasa baki bita d’akin ba? Mtsssss.”

Kashe wayar yayi da gudun bala’i ya nufi hanyar fita yana fad’in “Richard ka sake duba min duk wata cctv cam茅ra dake zagaye da unguwar nan, gaban gidanta da baya da kuma cikin gidan, ina son sanin duk wani motsi na ma’aikatan har kai har da ma karnukan dake fitowa a daren nan.”

Fita yayi da gudu ya shiga motar ya bud’e mata wuta ya d’auki hanya, tsaki da cije leb’en da yayi ya kai cikin buhu, sitiyari kanshi yasha duka kamar shi yayi laifin.

Yana kashe wayar Farha ta bi wayar da kallo da mamaki, a hankali ta furta “Me yasa ban bita ba? Na kwana da ita ko me yake nufi?”

Jiki a sanyaye ta rufe k’ofar ta juya ta koma d’akin duk tana jin ba dad’i.

Mai kula da k’ofar ga wanda ba ma’aikatan gidan ba suka bud’e mishi k’ofar daga d’akin dake nesa da k’ofar ya shigo, a daidai d’akin nasu yayi wani wawan birki ya fito rik’e da bindiga a hannu ya shiga cikin d’akin da k’arfin tsiya, zaune yake yana cin pizza rik’e da kwalin a hannunshi, girgiza kai yayi cikin b’acin rai ya shigo, desk d’in daya d’ora k’afarshi akai ya zura hannunshi ta k’asa ya danna wani madanni, a take gidan ya gauraye da jiniya alamar akwai babbar matsala, ko dai daga wajen mai gidan ya shiga wani tasku na rashin tsaro ko rashin lafiya, ko kuma gobara ko an samu wani bak’on haure da makamantan haka dan a d’akin Sarah dana mahaifinta da kuma d’akin karatunshi ma duk akwai, juyawa yayi zai fita sai kuma ya juyo ya kalleshi yace “Indai haka aikin naka yake ban ga anfaninka ba, dan wata rana gidan baki d’aya za’a d’auka akai baka sani ba.”

Fita yayi inda shi da sauran masu tsaron gidan suka shiga riga riga wajen shiga babban falon, babban mai bada tsaron kuma har ya umarci wasu da su zagaye gidan ciki da waje suga me ke faruwa, su kuma suka antaya ciki da gudu duk da bindigogi a hannu. Mata ma duk sun kid’ime sai fitowa suke da gudu suna san sanin me ke faruwa, a falon duk suka jibge sai kallon kallo ake, shima tsayawa yayi inda Farha ta fito tana tsaye a bayanshi tana kallon hannunshi dake rik’e da bindiga tana mamakin me ya kawota hannunshi? cirko cirko sukayi sai waiwaye suke, cikin tuhuma yace musu “Ina madame d’inku?”

Wani sabon waige waigen ne suka shiga yi, da sauri babban mai tsaron da wani ya mara masa baya da gudu suka nufi d’akinta, da wani k’arfi ido rufe yasha gabansu da hannun mai bindiga, bud’e ido yayi yana musu wani kallon raini yace “Wallahi wani abu ya sameta saina fasa kawunanku, na rantse muku da Allahn daya hallice ni.” Ya k’arashe yana nunasu da bakin bindigar, a sukwane ya nufi d’akin nata har da gudu gudu, bai tsaya komai ba ya bud’a d’akin ya shiga kamar an turashi.

Cak ya tsaya yana sauke wani irin numfashi yana rufe ido yana bud’ewa kuma dan ya tabbatar abinda ya gani gaskiya ne ko kuma gizo…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:20 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 4锔忊儯9锔忊儯

Tayi nisa a baccinta taji wannan jiniyar a duka gidan ta keta dodon kunnuwanta, cike da jin an takura mata tasa tafin hannu ta rufe kunnuwanta tana jan tsaki da fad’in “Ohhhhh Allah, me yake damun mutanen nan ne?”

Tayi fur da ciki tana sake gayyato wani baccin da tsiya sai kuma ta tuna da me kuwar nan ke nufi, a firgice ta mik’e tsaye da gudu har tana take hijab d’in dake d’an girma dan fita daga d’akin. Gani an bud’o k’ofar d’akin ne yasa ta tsayawa dan kar suyi karo da koma waye, kallon kallon suka shiga inda a zuciyarshi ya shiga godiya ga Allah, kallon hannunshi tayi d’auke da bindiga take taji wani fad’uwar gaba, cike da damuwar data ziyarceta lokaci d’aya a zuciyarta ta furta “Ya Allah.” A zahiri kuma nasarwa tayi da sauri ta sake tunkarar k’ofar tana fad’in “Me yake faruwa ne a waje? Da wata matsala ne?”

Tunda yaga ta kalli hannunshi ya d’an b’oyeshi bayanshi ya d’aga rigarshi ya soka bindigar, zata rab’ashi ta wuce ya rik’o hijab d’in nata ta tsaya cak amma bata juyo ba, kallonta yayi kamar wacce ya manta harshenshi ya shiga gurgira shi yana fad’in “Dan..Allah ki taimaka min wajen kula da lafiyarki, please Mom Waleed.”

Yatsina fuska tayi da alamar tambaya tace “Waleed? Who is that?”

Kafin ya bata amsa kuma ta gyara tsayuwarta tace “Mr., karka damu dani domin nasan yanda zanyi na kare kaina, karka nuna min ka fini damuwa dani kamar yanda nake da tabbacin ba kanayi bane saboda ni, understand?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button