NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Da wayar Kaka Joseph ya kira Daniel ya fad’a mishi tare da tambayar suna buk’atar a tafi da gawar can ne ko kuma a rufeta anan, abinda ya fad’a shine “Zan zo da kaina na tafi da gawar yer uwata.” Rai b’ace ya kashe wayar alamar zuciyarshi tafasa take.

Washe gari rashin baccin da bata samu da dare ba yasa bayan tayi sallah asuba ta kwanta bacci ya d’auketa, a cikin baccin ne taji hayaniya a sama sama kamar a mafarki, bud’a ido tayi ta sauko daga kan gadon, rigar bacci ce jikinta iya gwiwa mai sulbi da rawa a jiki, bud’e k’ofar tayi daidai da fitowar Farha da Salahadeen a d’akinsu suma saboda jin hayaniyar, Daniel ne a matuk’ar hassale yake k’wala kiran sunan Sarah ma’aikatan na k’ok’arin dakatar dashi, tana fitowa ganinshi yasa ta da sauri ta tunkareshi tana basu umarni su rabu dashi.

Bud’e hannaye tayi da nufin su rumgume juna kawai ya d’aga hannu ya wanketa da mari, saboda rashin tsammanin hakan yasa ta fad’uwa k’asa tana sakin k’ara, da gudu yayi kanta ya sunkuya ya kamata yana kallon fuskarta, da sauri ya tallabo hab’arta ya sake murtuke fuska sosai saboda ganin jini ta hancinta yana neman gangarowa, a fusace ya juyo ya kalli tsohon sosai yace “Waye kai?”

Mik’ewa yayi ya nufeshi rai a b’ace ya sake tambayar “Me tai maka? Akan me zaka mareta?”

Yana daf da kaiwa ga tsohon cikin k’arfin hali tace “Ka rabu dashi.”

Tsayawa yayi amma bai juyo ya kalleta ba sai tsohon daya k’ure da ido, wani k’ank’ance idon ne yake yana kuma bud’ewa ya dantse hak’ora sai karkarkar yake dasu ya jimk’e hannunshi kamar zai naushi wani. Tasowa tayi ta matsa kusa tana shanye kukanta ta kalli Daniel tace “I am sorry.”

Kaucewa yayi daga gaban Salahadeen dake binshi da kallon jin haushi cikin masifa yana fad’in “Yanzu kinga abinda kika jawo? Haka kawai yer uwata ba zata mutu ba idan ba ke ce kika kasheta ba, na jima da tsanarki ke da mahaifinki, ban yarda da gidan nan naku ba da ku kanku, da yer uwata taji maganata da bata yarda ta aurawa Sam wannan yaron ba, shi ba k’abilarmu ba hausarmu d’aya ba haka ba addininmu d’aya ba, haka kawai suka tashi suka had’ata dashi, kwana nawa auren nasu yayi ta mutu? Shi yasa na sake tsanarshi nake zargin shi ya kasheta saboda dukiyarta.”

Gyara tsayuwa yayi yace “Yanzu ina yer uwata take? A bani gawarta na tafi da ita tunda kin cinyeta.”

Cikin zubo da hawaye tace “Tana asibiti, amma ba…”

D’aga mata hannu yayi yana katseta da fad’in “Muje a saka hannu a bani ita.”

Kallon Salahadeen tayi saboda shine ya saka hannu a asibitin, juyowa yayi shima ya kalleta a take ya fahimci me take nufi, kallon Daniel yayi murya a dank’are yace “Muje, ka biyo ni.”

A fusace ya juya ya bi bayanshi zasu fita sai kuma ya tsaya ya juyo ya kalli Sarah dake kallonsu tana hawaye, cikin kallon tsana da muzantawa yace “Mayya kawai.”

Yana fad’a ya juya suka wuce a take ta fashe da kuka da gudu ta juya ta shige d’aki, da sauri Sandra da Farha suka bi bayanta cike da tausayinta, kan gado suka sameta suka shiga rarrashinta da maganganu masu taushi da kwantar da hankali, sun jima d’akin suna rarrashi kafin su barta da cewa ta shirya sai su taje wajen jana’izar kakarta karta kula da abinda ya fad’a.

Ta mik’e zata shiga wankan cike da kasala ga bacci a idonta ga ciwon kai tsabar kuka ga kuma yunwa da take ji, har zata shiga wayarta tayi ringin ta dawo ta d’auka da sauri saboda ganin bak’uwar lamba, tana d’auka ta d’ora a kunne taji an ce taje asibitin da gaggawa. Da mamaki ta bi wayar da kallo da tunanin me ya faru kuma? Da sauri dai ta canza kayan jikinta ko wankan ba tayi ba ta saka doguwar riga da baby hijab d’inta ta d’auki wayarta ta fita, driver ta samu suka fita tare.

Bayan fitarsu Salahadeen d’aya daga cikin masu tsaron gidan ne ya kira lambar Kabeer ya sanar masa, dan dama abinda ya rok’i ya masa kenan duk wani shige da ficen na gidan ya dinga sani, dan haka ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar masa daga maganganun da aka tattauna har marin daya ma Sarah. Sanin waye Salahadeen a sanda yake aiki wa Shakoor yasa Kabeer gaggawar kiran wasu yaranshi ya fad’a musu abinda yake so, sun je asibiti lafiya lau sun saka hannu sun d’auki hanyar filin jirgi da ambulance dake d’auke da gawar kawai wata mota ta daki ambulance d’in wanda hakan yayi kamar hatsari ne, duk tsayawa akayi kowa ya fito akashiga duba al’amarin, alamu dai sun nuna wanda ya daki motar a bige yake dan haka police suka tafi dashi.

Komawa sukayi mota zasu tafi amma sai Salahadeen ya rasa Daniel da suke tare a mota, dube dube ya shigayi amma babu alamarshi, har ambulance d’in saida ya duba amma babu shi nan, ganin kar ya dakatar da motar yasa suka wuce filin jirgin kawai da tunanin zai duba shi a baya, amma tashin hankali saida suka kai gawar ya sake dawowa ta hanya suka ga taron jama’a, tsayawa yayi dan ya gani sai kawai ya sauke ido akan Daniel wata ambulance na shiga dashi ciki za’a kaishi asibiti, jinin daya gani wurin ya sake tayar mishi da hankali a sukwane ya bisu.

Shine fa kuma Kabeer yasa aka kira Sarah aka fad’a mata ta zo asibitin, sanda ta zo ma k’asa tayi ta dube dube bata ga kowa ba, ta jima anan babu wani labari kafin wani dale zaune a gefe yace mata “Ki hau sama ki duba, tun d’azu aka wuce da wani da gaggawa.”

Da rashin fahimta kalamanshi kawai ta nufi wajen shiga lift dan ta rage wa kanta tsayuwar anan ma, tana fitowa daga lift d’in d’akin gefenta Salahadeen na tsaye, ta matso kusanshi zata tambayeshi aka bud’e k’ofar d’akin, likitoci biyu ne suka fito babban likitan na cire safar hannunshi, kallonsu yayi sosai ya girgiza kai cike da jimami yace “Ku ‘ya’yansa ne?”

Sarah da har yanzu bata fahimci komai ba Salahadeen ta kalla dan taji me zai ce, shima kallonta yake yana son jefo mata tambayar me ya kawota nan, kallon likitan yayi yace “Eh.”

Nuna musu d’akin yayi yana fad’in “Kuyi sauri ku shiga ku ganshi, rad’ad’in ciwon ya daki zuciyarshi sosai, a shekarunshi ba zai juri wannan zafin ba, munyi iya k’ok’arinmu akanshi sai dai kuma mu barwa ubangiji sauran.”

Da mamaki Sarah tayi saurin cewa “Wai me yake faruwa ne? Waye kuma babu lafiya yanzu?”

Kallonta likitan yayi bai ce komai ba kawai ya wuce, da sauri ta kutsa kai d’akin a take ta kuma tsaya tana kallon Daniel dake kwance, baki sake kamar wacce tsaka zata shiga ciki, juyawa tayi ta kalli Salahadeen tace “Wai me ya faru ne? Hatsari kukayi a hanyar taku?”

Daga k’ofar shigowa ne aka ce “Ba hatsari sukayi ba, ba kuma zai iya fad’a miki ba.”

A tare suka juya suna kallon Kabeer daya shigo, sake juyawa tayi ta matsa kusan Daniel dake ta zuro harshe, durk’usawa tayi tana shafa kanshi, kallon bakinshi take da jini jage jage, haka ma hannunshi na dama wanda ya mareta dashi amma gaba d’aya wuyan hannun a guntule yake an nad’eshi cikin bandeji, hawaye ne taji suna siraro mata sai bakinta dake ta rawa karkarkar har hak’oranta na had’uwa. Muryar Kaber ne taji ya sake fad’in “Wannan shine shaida zai fad’a miki komai.”

Juyowa tayi ta sauke ido akan wani mutum da suka shigo tare, kallon da take ma mutumin yasa shi d’an matsowa yana gyara rigarshi yace “Sannu madame, tabbas akan idanu na sanda mutumin nan ya yanke wa tsohon nan harshe, akan ganina yasa wuk’a ya datsa hannunshi yana fad’in wai yayi kuskure daya tab’a…ko bana ce ba dai amma akwai sunan daya ambata a lokacin.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button