NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Kabeer dake wani tako na isa ne ya nufi inda comp. take ya shiga danne danne, da sauri ya matsa zaiyi magana d’aya daga cikin k’artin nan ya shak’o wuyanshi ta baya ya matse a hammatarshi sosai, hankali kwance ya ci gaba da dannawa sai gashi kuwa hoton ya fito mishi a sanda abun ya faru, dan dama Richard ya gama bincikowa zai duba titin ne kawai suka shigo, yana ganin d’aukar yayi coche kawai ya danna gogewa, da k’arfi Richard yace “A’a dan Allah karka goge.”

Ko saurarenshi baiyi ba ya goge duk wata hujjar, yana idawa ya d’auki laptop d’in da iya k’arfinshi ya tarwatsa ta k’asa duk ta baje, k’ara Richard yayi dan jarinshi ce ya fasa mishi, cikin nutsuwa ya nufi hanyar fita ba tare daya ce komai ba kuma, sakinshi wannan k’aton yayi suka juya zasu fita, cikin jin haushi Richard yace “A ganinka ka lalata shedun kenan? To in baka sani ba ka sani Salahadeen yafi k’arfin tunaninka, duk yanda a yanzu zaka ga kamar kaine ke nasara akanshi idan ya juyo kanka ba zaka ji dad’i ba, kuma ni nan madatsi n’aura ne wanda zan iya kutse a kowace n’aura, a k’ank’anin lokaci zan sake samo mishi hujjar.”

A hankali Kabeer ya juyo ya kalleshi cikin sautin nutsuwa yace “Kafin lokacin aikina ya k’are nima, dama na mishi abinda na mishi ne dan ya gane tako wane fanni a gaba nake dashi, amma Sarah nan da k’ank’anin lokaci zata shigo hannuna, minti biyar ne? Minti goma ne ko sha biyar nima ban sani ba.”

Ko da ya fad’a ya juya suka fice daga d’akin, mota suka shiga har sun fara tafiya aka kira shi, yana d’auka a tak’aice aka ce “Yallab’ai an gama komai, yanzu haka tana hannunmu, ya zamuyi da ita?”

Wata dariya ya bushe da ita da k’arfi sosai kafin yace “Ku kai min ita gidan sarrafa madarata, gani nan zuwa nima yanzu.”

Waiwaye suna hanyarsu ta komawa gida cikin tsananin kuka ta kira lambar drivern jirginta ta umarceshi daya nemi izinin tashi, dan tana so yau ta bar k’asar kafin zuciyarta ta buga saboda tashin hankalin da take fuskanta, cikin girmamawa ya amsa mata da “To.” Kafin ta kashe wayar ta ci gaba da kuka har suka isa gida, a k’ofar shiga falon motar ta tsaya ta fita, kallon drivern tayi tace “Ka jira na fito zamu wuce a茅roport ne.”

Shima amsa mata yayi da to ya gyara parking motar alamar yana jiranta, ganin hakane yasa d’an lek’en asirin Kabeer ya koma gefe ya kirashi, yana d’auka yace mishi “Ya akayi?”

Murya k’asa k’asa yace “Yallab’ai yanzu Madame Sarah ta dawo gida, amma alamu sun nuna zata sake fita ne tare da driver.”

Cikin jin dad’i yace “To kaga ka ci gaba da saka ido akanta, idan ka tabbatar ta fita saika aiko min da sak’o, yau kam za’a yi ta ta k’are.”

Amsa mishi yayi da “Shikenan yallab’ai.”

Kashe wayar yayi ya sake lek’owa. Ita kuma tana shiga d’akinta ta wuce ta d’auki akwatinta k’irar Hello King, wadrob ta bud’a ta dinga kwaso kaya tana watsawa ciki tana yi tana shashek’ar kuka, ko da taga ta cika kawai ta rufe ta sauke k’asa ta jawota bayan ta d’auki wayarta da passeport. Saida ta bud’a wani d’an akwati mai kama dana kwalliya ta d’auki kud’i ta zuba k’aramar jakar hannunta kawai ta fita, yanzu ma falon babu kowa dan haka ta fice kawai, zata fita Linda kuma zata shigo sukayi karo, da sauri taja baya ta shiga bata hak’uri, da hannu kawai ta mata alamar ba komai ta wuce inda ta bud’a motar ta saka jakarta ta shiga suka fice.

Linda na kallo har suka fita daga gidan da sauri ta shiga ta sanarwa da Farha, da mamaki ta tambayi Linda to ina zata je? Ita ma dai bata sani ba shine amsar data bata.

Tazara kad’an ta rage ta sadata da filin jirgin mota biyu suka shiga gabansu suka tsaya, majiya k’arfi ne shida suka fito da fuskoki a rufe da bindigogi a hannu suka tunkaro motar kamar dai masu fashi da makami, driver ne yayi yunk’urin fitowa yana d’ora hannaye a kai, ba tsaya komai wani ya had’a kan driver da murfin motar inda ya fad’i a waje somamme. Daga ciki duk ta rud’e sai zazzaro ido take tana kallonsu suna nufota, inna lilliahi wa’inna ilaihi raju’un shine abinda ta fara ambata, sune bud’e k’ofar wani ya fincikota tare da manna mata hanki. a hanci, daga nan bata sake sanin me ke faruwa da ita ba.


Kabeer na fita Richard ya shiga kiran wayar Salahadeen amma abun takaici tana ta k’ara ba a d’aga ba, saida ya tsayar da motar zai shiga cikin falon ya lura da kiran dan wayar a silent take, d’auka yayi yana cikin shiga falon da sassarfa yana fad’in “Ina jinka Richard, ka samo wani abu ne?”

A firgice ya katseshi da cewa “Saurare ni Salahadeen, yanzun nan bayan fitarka wannan mutumin ya zo nan, ya lalata duk wata hujja dana samu yanzu, ya kamata kayi k’ok’ari ka kasance tare da Sarah a yanzu, dan da alama akwai abinda suke shiryawa akanta, kayi sauri kaji?”

Salahadeen daya tura k’ofar d’akin ya shiga bai damu da abinda zai faru ba ne ya tsaya ganin d’akin a wani hargitse, yanda wadrob ke bud’e da kaya a k’asa sun zube ya tabbatar mishi ta fita a d’akin ko ma gidan baki d’aya. Da sauri ya juyo yana kiran sunan “Sandra! Sandra.”

Linda dake d’akin Farha ne suka fito tare jin muryarshi, bai samu damar fahimtar yanayinshi ba ya jefo musu tambayar “Ina Sarah take?”

Girgiza kai Farha tayi sai Linda da tace “Baifi minti biyar ba data fita tare da driver, kuma na ganta da valise da alama tafiya zatayi.”

Da k’arfi ya jimk’e wayar hannunshi ya naushi iska yana fad’in “Shiiiit.” Da gudu ya sake fita daga d’akin dan yasan tunaninta kawai barin k’asar nan ne, hanyar filin jirgin sama ya nufa da matsiyacin gudu, yana daf da isa ne shima ya hangi motar da kuma driver da police a wurin har an saka alamar rufe wurin da abun ya faru.

Birki ya taka ya fito a haukace ya tunkari wurin bai damu da yan jarida da jami’an da ma motar asibiti dake kula da driven ya kutsa cikin taron…

Alhamdulillah

Kuyi hak’uri da wannan馃憦
13/04/2021 脿 04:21 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 5锔忊儯1锔忊儯

D’aga kariyar yayi ya duk’a ya isa wajen driver cikin tashin hankali ya kalleshi yace “Ina take? Ina Sarah? Me ya faru anan?”

Da sauri wani police ya dafa kafad’arshi yana fad’in “Malam fita anan, waye kai da zaka tsallake ka shigo wurin nan? Baka san ana bincike bane?”

Juyawa yayi a fusace idonshi har sunyi jajir yace “Ina so ne nasan me ya faru da matata, tana ina ne?”

Wani insp. dake gefe yana lure da abinda ke faruwa ne yayi saurin zuwa wajensu, hannu ya bashi suka gaisa yana fad’in “Sunana insp. James Fernandez, nine nake bincike akan kidnapping miss Sarah Shakoor, yanzu haka mun gama duk wani bincike amma bamu samu wata makama ba, yanzu dai muna ji..”

Da k’arfi Salahadeen yace “Kidnapping kuma? Su waye? Yanzu kuna nufin ku ce baku samu komai ba?”

Fizge hannunshi yayi daga na insp. d’in ya juya baya da k’arfi yana rik’e k’ugu da hannu biyu da bubbuga k’afa d’aya irin ya kai mak’ura d’in nan, juyowa ya sake yi daidai idonshi ya sauka cikin motar dake bud’e, kasancewar ya d’anyi baya yasa shi iya hango wayar Sarah a k’asan kujerar mai tuk’i, da sauri ya k’arasa ya zura hannu ya d’auka, bin bayanshi insp. d’in yayi yana fad’in “Wannan wayarta ce?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button