SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Saida ya bud’e k’ofar ya fita sannan ya juyo ya kalleshi yace “Anan kuna auren dole?”
Wata dariyar yayi yace “Ina! ai ko alama ba ayi.”
Jinjina kai yayi yace “To idan kaje neman lauyan ka had’a harda yan jaridu dan zasu ga yanda ake auren dole kula a zauna dan dole.”
Ficewa yayi ya barshi yana ta dariya ya mik’e ya nufi toilet, dan in bai same shi can ba ya kirashi kenan yana daddana mishi ashar, yana fita shima hanyar gidan ya d’auka, yayi tafiyar kusan awa d’aya dan ba gudu yake ba kafin ya isa, bud’e mishi akayi ya shige ciki ya paka mota inda ya saba, fita yayi ya tunkari shiga falon. har ya shiga ciki kuma saiya tuna da wayar Sarah daya samu, juyawa yayi da nufin d’aukowa ya fita, yana daf da kaiwa ga inda ya aje motar yaji ana fad’in “Eh yallab’ai, yanzun nan ya shigo.”
Yana isa wajen suka had’a ido tsoro yasa shi sakin wayar, a take kuma saiya basar yayi murmushi mai kama da kuka ya duk’a ya d’auki wayar, shima murmushin ya masa ya bud’a ya d’auki wayar kawai ya shige ciki.
Kai tsaye d’akinta ya wuce, kamar yanda ya santa kuwa ya samu ta koma ta kwanta bacci, zaune yayi bakin gadon yana kallon fuskarta,Sunkuyawa yayi ya sumbaci goshinta hakan yasa ta bud’a ido, da sauri ta tashi zaune tana fad’in “Yaya Salahadeen, yaushe ka shigo?”
Murmushi ya fara sakar mata kafin yace wani abu kuma wayarshi ta shiga vibration a aljihunshi, yana dubawa ya ga Leo ne, d’auka yayi daga b’angaren aka ce “Salah kayi sauri ka zo akwai matsala fa.”
Da sauri ya mik’e tsaye yana fad’in “Ok gani nan zuwa.”
Kashe wayar yayi ya mayar aljihu, sunkuyawa ya sakeyi ya sumbaci bakinta ya juya yana fad’in “Zan sake dawowa kinji, an kirani ne da gagggawa.”
Har zata mik’e tsaye kuma ta koma ta zauna tana kallonshi ya fice, ajiyar zuciya ta sauke dan bata raba d’ayan biyu cewa b’atan yer uwarta ne ya jawo wannan matsala, amma za tayi k’ok’ari ta danne ta kuma shanye komai ba tare data bari shaid’an ya sake cin galaba a kanta ba a karo na uku. Yana fita boot d’in mota ya fara bud’ewa, kamar yanda ya barshi kam ya same shi har yanzu a wurin yana yan zagaye zagaye, saida ya bari ya juya bayanshi da k’arfi sosai yasa tsintsiyar hannu ya daki wuyanshi da ita, ba wahala mutumin yayi luuu zai fad’i ya tareshi, saida ya sake juyawa bai ga kowa ba ya kuma tabbatar da kusurwar babu camara tsaro, janshi yayi kawai ya saka shi a boot d’in ya mayar ta rufe, shiga yayi ya tayar da motar ya fice a gidan ba wata matsala.
Yana zuwa can a kid’ime ya samu har Richard ma ya isa, wajen Leo ya nufa yana tambayarshi menene? Cikin rashin kuzari yace “Jiya da dare mun samu nasarar shiga kampanin nan bayan mun dak’ile duk tsaron dake zagaye da kampanin, lungu da sak’o mun duna na wurin nan har da wajen ajiyar kaya da ma wasu ofisoshin ma’aikatan, amma gaskiya bamu samu wani abu mai kama da mutum ba.”
Jinjina kai yayi ya kalli wani matashi dake tsaye da kulki a hannu yace “Ka bud’a boot d’ina akwai tsarabar dana kawo muku, kawo mana ita nan zamu samu wani abu daga gareshi.”
Girgiza kai Richard yayi yana murmushi dan ya san akwai wanda ya kwaso, yana zuwa kam sai gashi ya jawo wannan mutum da har yanzu bai motsa ba, tsakiyar wurin ya zube shi kamar wasu kaya ya koma gefe, cikin k’asaita ya taka ya isa wajen matasan nan na jiya dake d’aure har yanzu, kallon Leo yayi yace “Ina wayoyinsu?”
Da sauri wani matashin ya ciro wayoyin a aljihu ya mik’a mishi, murmushi yayi ya kalli d’aya daga ciki yace “Lambar bud’ewa?”
A matuk’ar jigace yace “20, 29.”
Ba tare daya daina murmushin ba ya saka lambar ya bud’e, sak’onnin da suka wakana tsakaninsu ne suka bayyanar mishi, sai dai lambar ba a b’oye take ba, dan haka ya tura gajeran sak’o kamar haka “Akwai matsala fa oga.”
Da gaggawa aka maido tambaya da cewa “Me ya faru? Ba mun gama aikinmu ba?”
Hankali kwance ya mayar da cewa “Hakane, amma ina tunanin kamar ana bibiyarmu.”
Ba jimawa aka maido da “Kunyi magana da wani ne akan shirin namu?”
“A’a, amma wacce muka yi aikin a kanta tana da alak’a da wani daya san mu, kuma mutum ne mai had’ari, yana zarginmu kuma gaskiya ba zamu iya ji dashi ba.”
A tak’aice aka maido da “Wanene?”
Shima a tak’aicen yace “Mijinta, Salah.”
Maido akayi da cewa “Ku samu wuri mai tsaro ku b’uya, zan fara yin magana da boss kafin mu san abunyi.”
Zai mayar da ok sai kuma Richard dake gefenshi ya d’an zungureshi, d’aga kai yayi ya kalleshi hakan uasa ya nuna mishi wannan mutumin daya fara motsawa alamar zai farka, takawa yayi har ya tsaya kusanshi yayi durk’uso irin na maza, ya tashi zaune yana waige waige dafe da wuyanshi suka had’a ido. Zabura yayi sosai yaja baya yana kallonshi da mamaki yace “Meya faru? Me ya kawoni nan? Me kake yi anan?”
Fuskarshi a had’e ya jawo nicktied d’inshi ba alamar wasa yace “Kafin na baka amsa zan so ka fara amsa min wasu tambayoyina tukuna, idan kayi gaggawar sanar dani saina barka ka tafi, idan kuma ka k’i saina tona rame anan na birneka da ranka, ka fahimta?”
Zazzaro ido yayi yana fad’in “Ban gane ba? Me nayi daka kawo ni nan? Kai ba mijin madame Sarah bane dama d’an daba ne?”
Wani murmushin gefen labb’a yayi masa yace “Ita ma Sarah a harkar dabar muka had’u da ita, yanzu kaja baki ka min shiru amsar tambayata kawai nake son ji daga bakinka.”
Sakin nick. d’in yayi yana d’an kallon yatsunshi yace “Wa kake wa aiki bayan Sarah?”
Cike da gatsali yace “Kai waye da zan fad’a maka? Malam baka san ko ni waye bane, kafin na ja maka bala’i ka gaggauta barina na bar wurin nan.”
Wani murmushin ya kuma saki ya mik’e tsaye ya kalli sauran matasan yace “Ba zai bayar da amsa cikin dad’in rai ba, ku canza masa wurin zama akwai buk’atar service d’insa ya fara kawo wuta.”
Kamar dama umarninsa suke jira kawai sukayi caaa akan mutumin, saida suka d’ora shi kan kujera ta k’arfe suka had’e hannayenshi ta baya suka d’aure tamau, wani kulki dake hannun su suka shiga jibga masa kamar wasu masu tambaya a k’abari, ko da ya fara fitar da jini ya dawo hayyacinshi da sauri ya shiga fad’in suyi hak’uri zai fad’i gaskiya. Dakatar dasu yayi suka ja baya shi kuma ya matso, tsaye ya sake yi gabanshi yana kallonshi yace “Ina jin, tambayata ta farko?”
A galabaice yana tofar da yawun da suka had’e da jini yace “Uncle d’in madame Sarah ne, shine yace na dinga saka mata ido saboda rayuwarta na cikin hatsari, yace muyi abun a sirrince ne saboda tayiwu akwai masu son kasheta ma a cikin gidan, shiyasa nake sanar dashi duk wani motsinta.”
Jinjina kai yayi yace “Idan na fahimceka dai kana sanar dashi komai a kanta ne saboda baka so wani abu ya same ta?”
D’aga masa kai yayi yana fad’in “Hakane, kuma yana biyana kud’i ne shiyasa bana k’asa a gwiwa wajen sanar dashi.”
“To amma me ye na bashi bayanai a kaina ni kuma? Ko nima ina cikin hatsarin ne?”
Girgiza kai yayi yace “Maganar gaskiya ban sani ba, ya dai ce na sanar dashi duk wani abu dake faruwa a gidan.”
Matsawa yayi kusanshi yana kallon idonshi yace “To ina yace maka ya kaita bayan ya saceta?”
A d’an firgice yace “Me? Ba gaskiya bane, sam ba shi ya sace ta, shi da yake neman kare rayuwarta.”
Wani bahagon mari ya watsa masa a kumcin dama, saida kujerar tayi baya kamar zai fad’a kuma ta tsaya kan k’afafunta, cikin d’aga murya yace “Karka raina min hankali malam, ka fad’a min ina ya kaita bayan ya d’auketa, idan ba haka ba kuma zaka rasa ranka.”