NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Sake girgiza kai yayi yace “Na rantse maka bansan komai ba a game da b’atanta ba, ka yarda dani.”

Juyowa yayi ya kalli Leo ya tara mishi hannu, bindiga ya fito da ita a bayan rigarshi cikin d’amararshi ya d’ora mishi a hannu, rik’eta yayi da kyau ya d’anata sannan ya saitata a kanshi yace “Zan lissafa uku ka fad’a min gaskiya ko kuma nayi asarar alburushi d’aya yanzun nan.”

Cikin kakkarwa da tsoro sosai ya shiga fad’in “Yi hak’uri yallab’ai, yi hak’uri zan fad’a, zan fad’a maka gaskiya na rantse.”

Ba tare daya d’auke bindigar ba yace “Ina jinka.” Cikin rawar harshe yace “Ya fad’a min zai sa a saceta dan ta hakane masu son kasheta zasu bayyanar da kansu, amma wallahi ban san ina ya kaita ba, ka yarda dani yallab’ai karka kashe ni.”

Shiru yayi yana kallon fuskarshi yana ji kamar ya harbe kowa ma ya huta, dagiya ce kawai yake yana ta son ya shanye abinda yake ji, amma da alama mutane na son kaishi mak’ura. Richard ne ya dafa kafad’arshi ta baya hakan yasa shi sauke bindigar ya juyo yana tako a hankali, bin bayanshi Richard yayi yana fad’in “Salah ina ga kamar gaskiya ya fad’a, daya sani daya fad’a mana duba da yana da tsoro, to amma tambayar anan ita ce ina suka kaita bayan su prince sun tabbatar mana kampanin madara suka ajeta.”

Tsaye yayi ya rik’e k’ugu yana murza gaban goshinshi, iska kawai yake furzarwar bai ce komai ba, ya jima haka kafin ya d’ago kai ya kalleshi da sauri yace “Idan muka tashi aiki muna son rainawa hukuma hankali miye bama aikatawa?”

Cokin rashin fahimta Richard ya d’aga kafad’a yace “Komai yi muke saboda b’atar da sawu.”

Jinjina kai yayi yace “Haka yayi shima, baisan komai akan dalilin da yasa suke son kasheta ba, k’ungiya ce dasu ko kuma aljanu ne dasu, amma dai abu d’aya da muka tabbatar yanzu shine Kabeer ne ya sace ta, kuma zan gano inda ya kaita da yardar Allah.”

Gyara tsayuwa yayi yace “Na tabbata prince a kampanin madarar suka aje ta, amma saboda kawar da hankalin duk wani mai hannu a ciki ya canza mata wuri bayan barin kowa wajen, to ina ne ya kaita kenan?”

Cike da rashin tabbas Richard yace “Inda yafi nan tsaro, ko kuma inda ba’a tsammani, idan kuma k’ungiya ne dasu to tana wajen.”

Shiru yayi yana tunanin abun daki daki, sai yanzu ya fara yarda lallai suna aiki da sihiri ko yace rufa ido ko kuma shaid’anun aljanu, duba da b’atanta na k’asar mekka wanda kawai ya faru ne kamar mafarki, ya jima yana kai da kawowa haka kafin ya juyo, a sukwane ya juyo ga su Leo zaiyi magana sai kuma wayar prince daya karb’a tayi k’ara alamar shigowar sak’o, da sauri ya duba jiki na rawa ya bud’e, sak’o ne kamar haka “Oga yace ku zo yanzu ku same shi a gada ta 122 zaku ga allon sanarwa mai d’auke da alamar far away, a ta gefenshi zaku ga Bar.”

Kallonsu prince d’in yayi ya kalli Leo yace “Ku kwance su zamu fita yanzu.”

Da sauri suka kwance su yasa suka gyara jikinsu har da canza kaya, saida ya kafesu da ido yace “Ba kunce baku tab’a had’uwa da ogan ba? To yanzu zaku had’u, ku tabbatar kun cire min fuskar jimamin nan dan karya gane wani abu, kun fahimta?”

Jinjina masa kai sukayi alamar eh, d’orawa yayi da cewa “Idan kun had’u dashi ku ja shi da hira, ku nuna masa tabbas ni ne ke bibiyarku ina son gano inda kuka kaita, kun gane?”

Nan ma jinjina masa kai sukayi kafin ya shiga gaba suna bayanshi, tare dashi da Richard da su suka tafi a mota, saida ya tsaya wani wuri suna kallonshi ya shiga ya fito suka wuce, daidai kwatancen ya tsaya kafin ya musu umarnin shiga, jiki a sanyaye suka nufi ciki a daidai k’ofar suka tsaya suka gaisa da wasu k’arti biyu wanda suka sace Sarah tare dasu, hakan ya tabbatar musu ogan na ciki kenan, wucewa sukayi amma saida gabansu ya fara fad’uwa dan bar d’in kamar ba safiya ba, babu mutane sai masu aiki a wurin guda biyu suna kai kawo sai kuma d’aya dake tsaye yana tarban masu zuwa da abun sha, ga kuma duhu a wurin dan fitilar dake kunne mai ja ce babu haske sosai. Haka suka k’arasa kusa da wanda suka gani shi kad’ai zaune kusa da window da hula (hana sallah) mai tambari nike yasa tafin hannunshi ya rufe rabin fuskarshi kamar wani mai tunani ko kuma hankalinshi ya tafi kan abinda yake kallo.

Tsaye sukayi suna gaisheshi da girmamawa, ba tare daya amsa ba ya nuna musu kujerun dake fuskantashi suka zauna, ba tare daya kallesu ba ko ya gyara zamanshi daga yanda yake ba yace “A ina yake? Ya kamaninshi suke? Kuma ya akayi ya fara zarginku?”

Kallon juna sukayi suna rarraba ido, ashe rubtamu yayi? Kallonshi sukayi sai prince ne yayi k’arfin halin cewa “Yallab’ai da yake shi d’in mai gidanmu ne a baya, yana da wayo sosai da basira, yana saka mana ido sosai ta yanda ba ma iya ha’intarshi…”

Shiru yayi sakamakon d’aya daga cikin ma’aikatan wurin daya zo gurinsu yana aje musu kofunan lemu, yana gama ajewa cikin ladabi yace “Yallab’ai da wani abu da kake buk’ata ne?”

Prince da abokinhi da sauri duk suka kalli mai maganar dan sun ji muryar ta muku kama data wani, wani? Ba kama bace kam Salahadeen ne da kanshi a cikin kayan ma’aikatan wurin da wata hula mai kama da kwali, su ba suyi dariya ba ba kuma sun bayyanar da mamakinsu ba dan tuni ya gargad’esu da ido cewa su basar kawai. Ba tare daya kalli mai magana ba ya d’auki kofin wanda yayi oder tun shigowarshi ya kurb’a sama da sau uku kafin ya aje, a hankali cikin isa ya juyo da kai ya sauke idonshi cikin na Salahadeen, k’uru k’uru shine kallon da suka ma juna, cikin kid’ima da razani Salahadeen ya furta ” Daniel.”

Da fuskarshi kam duk ta moje tsabar tsufa ya wani karkata masa kai wai hima hege ne nan馃榿, wani murmushi Salahadeen yayi yace “Kud’i ba?”

Shima murmushin yayi yace “Ka canka daidai.”

D’an gyara zama yayi yace “Muje mataki na gaba, me kake so?”

Gyara tsayuwa yayi yace “Nasan kana sane da wanda zaka had’u ka zo wurin nan, me yasa ka zo?”

Wani murmushi yayi yace ” Saboda na fad’a maka wani abu ne.”

Kallonsu prince yayi ya musu alama da hannu zasu iya tafiya, mik’ewa sukayi suna kallonsu da mamaki har suka fita, kallon Salahadeen yayi ya nuna masa gurin da suka tashi yace “Zauna.”

Ake farantin hannunshi yayi tare da cire hular ya aje kan desk d’in ya zauna cike da isa da aji da izza suna kallon juna, gyara zama Daniel yayi yace “Ina so ka fita harkar yarinyar nan dan ita ba budurwa bace kamar kowace, kadara a suffar mace kuma bilyoyin kud’i, kakarta ta gaji wata kadara mai girman gaske da daraja wacce ni ko rabinta ban gada a wajen mahaifinmu ba, wannan kadara ina ji ina gani ta d’auketa ta damk’a a hannun ‘yarta Samantha, lokacin dq nake tunanin had’a Sam aure da d’ana Barack sai kuma Shakoor ya gifta tsakani, saida na jure sosai na iya kallon aurensu, na rasa yanda akayi na zama marar sa’a haka, dan a lokacin da nake tunanin aika yan fashi a gidan su d’auko min takardun kadarar sai kawai a daren ta mutu, to me zanyi kuma daya wuce sakawa yarsu ido wacce nake da tabbacin ita ce magajiyar wannan kadara?”

Muskutawa yayi ya ci gaba da fad’in “A duniya babu wacce na tsana sama da yarinyar nan, domin kuwa ita ta mayar da wannan muhimmiyar kadara wajen k’era motoci, yanzu burina kawai naga na gadar da wannan wajen ga ‘ya’yana da jikokina. A k’arshe ina gargad’inka daka fita sabgarta kamar yanda na fad’a maka, inba haka ba kuma zaka rasa ranka a banza kaima, dan shirin zaune mukayi a kanta bana tsaye ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button