SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wani murmushi ya saki mai kama da kuka ya d’ora hannayenshi kan desk d’in cikin tausasa murya yace “Shi kuma Kabeer fa? Me yasa yake son kasheta?”
Jingina yayi a jikin kujerar yana kallon fuskarshi yace “Ban san nufinsa ba, amma dai fansa yake son d’auka shima.”
Shima d’ora hannaye yayi akan desk d’in yana fad’in “Ka ga, na zo gurin nan ne da niyyar kashe waccen yaran, amma bayan na zo sai naji ba buk’atar haka, dan indai akan ka ne na fahimci mutane dayawa zasu mutu wanda basu ji ba basu gani ba, ina so ka dakatar da matsawarka akan sai ka san me yake faruwa kuma tana ina? Karka matsanta sosai dan zaka iya hassala masu son kasheta su aikata da wuri.”
Tunda ya fara magana yake bin hannunshi da kallo hannun da ranar a asibiti suka ganshi a yanke, fahimta da yayi yana kallon hannunshi yasa shi yin dariya yana nuna mishi hannun yace “Kana al’ajabi ko? Kasan ta yanda abun ya faru?”
Girgiza kai yayi ya ci gaba da cewa “Ban san wace irin k’iyayya bace ta shiga tsakaninka da Kabeer, amma dai duk abinda ya faru yayi ne saboda ya k’untata maka.”
Gyara zama yayi ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yace “Abu mai sauk’i, wani mai kama dani ne aka yankewa hannu, duk da dai nasan yayi aiki da sihiri amma bansan ya yayi ba.”
Jinjina kai Salahadeen yayi yace “Yanzu fad’a min inda ya kaita, bana son b’ata lokaci dayawa, idan kuma kayi taurin kai zan saceka kaima a madadinta, watak’ila idan nayi haka ta bayyana gareni.”
Wata dariya ya shiga rerawa da k’arfi yana nuna Salahadeen, saida yayi niyya dan kanshi ya dakata yana ci gaba da nuna shi da hannu, a hankali ya dinga sunkuyar da kai yana layi kamar wanda yasha k’waya, kafin kace me kuma kawai saiya fad’a kan desk d’in.
Wani murmushin k’asaita ya saki shima ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana kallonshi, da sauri Richard dake gefe shima cikin kayan ma’aikatan ya k’araso yana fad’in “Me ka samu a wajenshi?”
Girgiza kai yayi yana mik’ewa yace “Baiyi magana ba, idan munje can zaiyi.”
Sunkuyawa yayi ya d’auki Daniel ya sab’a a kafad’a, dama kuma irin tsofaffin nan ne busashi marasa jiki, kamar bai d’auki komai ba haka ya bi ta k’ofar baya dashi suka saka shi a mota, Richard kuma dasu prince suka bi bayanshi suka bar masu tsaron Daniel bakin k’ofar shigowa baki bud’e suna zare ido.
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:21 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LABARI*
SAMIRA HAROUNA
*SADAUKARWA GA*
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
5锔忊儯3锔忊儯
Ko da suka je d’auke da Daniel ya aje shi gefe yana gyara rigarshi, Leo ne ya shiga dariya yana fad’in “Wai Salah mutane nawa zaka k’wamuso ne? Ina tsoron fa gidan nan ya mana kad’an mu da wanda kake d’aukowa.”
Richard ma dariya yayi yace “Ai kasan nan yafi k’warewa, ita kanta wacce ake ta kwaso mutanen saboda ita fa ya tab’a k’wamusheta.”
Juyawa yayi ya harari Richard hakan yasa shi rufe baki da hannu yace “Nayi shiru.”
Ko da yayanta ya d’aukota daga gidan bus ta shigo gidan da gudu tana kwad’a sallama, sauran yan uwanta ne suka tarbeta da kuma mahaifinsu, tun basu gama gaisawa ba ta jefi mahaifinta da tambayar “Aba ina Sarah?”
D’an hararenta yayi yace “Tare kuka zo ne da zaki tambayeta? Ke baki san ina kika barota bane?”
D’an b’atar da dariyar fuskarta tayi tace “Aba ai ta rigani zuwa ita, ina take ne? Idan ma fa gidan Hajia ta sauka Allah nima can zan koma, dan ba zan zauna nesa da ita ba.”
Yanda ta k’arashe maganar da shagwab’a ne yasa babban yayanta Salim cewa “To sarauniyar shagwab’a, saiki bari har mu ganta sannan ki turo mana bakin.”
Dakawata tayi ta kallesu irin da gasken nan sosai tace “Wai me kuke nufi? Sarah fa tun jiya munyi magana cewa zata zo nan, kuma sanda mukayi magana tana kan hanya ne.”
Aba ne ya gyara tsayuwa yana gyara zaman babbar rigarsa yace “Kamar ya? To ina take? Mu dai bamu ganta ba, tasan wurin ne dama?”
D’an girgiza kai tayi tace “Muna cikin magana da ita ne kuma sai komai ya tsaya bata sake amsa min ba, kuma nayi ta kiranta bana samu saina d’auka ko ta shigo nan ne shiyasa, to amma ina taje?”
Yayanta da take bin bayanshi ne yace “To ko fasawa tayi?”
Kallonshi tayi cikin damuwa tace “Bana tunanin haka, sai dai ko in wani abu ne ya sameta.”
A d’an firgice Aba yace “Kamar me kenan? Kinsan wani abu ne a kanta da baki fad’a mana ba?”
Girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace “A’a aba, kawai dai ina ji kamar ba lafiya ba, Sarah babbr yarinya ce ba zata sab’a maganarta ba, na tabbata bata da matsalar kud’i ko abun hawa, kuma tunda tace tana kan hanyar zuwa shiga jirginta to me zai hanata zuwa d’in.”
Wayarshi ya ciro yana fad’in “Bari a sake kira aji to.” Kura ya dinga yi amma shiru ba’a samu, faruwar al’amarin nan ya jefa zuk’atansu cikin tsananin damuwa da rashin walwala, haka suka wuni suna buga kira wa lambarta, ganin har dare babu wani labari sai suka duk’ufa tunani da jimamin halin da take ciki, amma sam basu yarda Hajia tasan me ke faruwa ba, har Sajida da taje gaisheta k’ok’ari tayi ta danne damuwar hakan a ranta har ta baro gidan, duk da Hajia na fad’an yanzu ba zata kwana ba? Haka tace mata zata dawo ta mata kwanaki har sai ta gaji da ita.
Da safe ma ko da suka tashi suka ci gaba da doka kira, a yanzu kam sai Sajida ta fara hawaye da ikrarin ba lafiya ba kawai, hakan ya sake tashin hankalin Aba. A ranar a madadin sau d’aya da ake dafa abinci ana kaiwa makarantar almajirai sai aka kai sau biyu, sannan da kanshi ya nemi alfarmar malamin da ya saka yarshi addu’a Allah yasa ta kasance cikin k’oshin lafiya a duk inda take, a ranar haka ya tilasta yaran dula suka zarce da azumi da k’ara k’aimin ayyukan alkairi akan na da.
Ta galabaita sosai saboda k’ishin ruwa ga kuma bacci da takura, hakan ya haddasa mata ciwon kai da matsanancin jiri, ga yunwa da cikinta har ya gaji da kuka ya daina, tun yana ambaton sunan Allah a bakinta har kai sai cikin zuciyarta kawai take iya fad’a, idonta banda duhu babu abinda suke gani, da k’yar ma tale samun numfashin da take saukewa, ga d’aurin da aka mata da masifar zafi tana so ta motsa ta gyara hannayenta amma ba dama, har jikinta yayi sanyi tare da tsami, tun tana rik’e fitsarin daya cika mata mara har taji tana neman salwantar da abinda ke cikinta ta ziraroshi daga nan zaune, yawunta sun k’ame ta yanda bakinta ya bushe sosai ko yawu bata had’awa, lumshe idonya suke tana ci gaba da ambaton Allah tana fatan ya tseratar da ita.
Yanzu ma kamar jiya taji k’arar bud’e k’ofa amma bata ga ta ina ya shigo ba, bata iya kallon inda yake ba bare ta fahimci ma asalin wanene bare tufafin jikinshi, tana jin motsinshi har ya zauna kusa da ita kamar yanda yayi jiya yana fuskantarta, wata yar dariya taji yayi tare da fad’in “Princess, princess, yarinyar da bata gaji mulki ba amma tsabar iko yasa ake kiranta da sunan gimbiya.”
K’ala ba tace mishi ba sai sake mishi-mishi da take da ido, d’orawa yayi da “Kinsan wani abu Saratu? Mahaifinki baisan dad’in duniya ba? Na kuma ji dad’i da ban zama sakarai kamar shi ba.”