SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Tab’e baki yayi yace “Ina zan sani? Ki tambayi mata.”
Juyawa tayi wajen mai shagon har tayi zaune tace “Wannan fa?”
Mik’ewa tayi tsaye ta ciro d’auri mai yawa ta kamo ta dan ta lura ba bahausa bace, ita kuma bazarba mace tafiyarsu ba zatayi ba.
D’aga hijabinta tayi ta mata alama ta rik’e, rik’ewa tayi a hankali ta d’an d’aga rigarta, yana ganin haka ya dawo da baya ya tsaya k’ik’am yana kallonsu, jigidar nan ta d’aura mata, sakinta tayi ta kalleta tace “Ya kika gani?”
Sake d’aga rigar tayi wanda hakan yasa har cibiyarta ta bayyana, wata sanyayyar fad’uwar gaba yaji ta ziyarce shi, lumshe ido yayi sakamakon wani abu da yaji ya tsarga masa tun daga kan k’afarshi har zuwa kai.
Washe baki tayi tana kallon yanda jigidar ta mata, abun ya birgeta sosai shiyasa ma ta kasa sakin hijabin sai kallo take, juyowa tayi da niyyar mishi magana amma sai taga yanda ya k’urawa cikinta ido yana kallo, da sauri ta saki rigarta da hijabinta, ruf ya rufe ido saboda wata irin kunya had’e da takaicin kanshi sun kama shi, cikin dubara ya d’an juyar da kanshi kafin ya bud’e idonshi kan wani shagon.
Cikin taushin murya tace “Mr. zaka siya min wannan? Kaga ta min kyau ko?”
Kasa magana yayi har saida ta matso kusanshi tana kallonshi tace “Please mr.”
Da k’yar ya d’aga labb’enshi dan baya so ta gane komai a tare dashi yace “No.”
Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace “Pleaaaaase.”
Wani lumsassen kallo ya mata kamar mai jin bacci yace “A said no.”
Saida ta lab’e baki irin zatayi kuka ta shiga kiciniyar cire jigidar, da k’yar ta samu ta cireta ta taka a hankali ta aje kan wani tebur, cikin sanyin jiki ta juyo ta d’auki ledar kayan daya siya mata ta wuce. Da kallo ya bita ganin duk bata ji dad’i ba, jaka biyar ya ciro ya aje kan teburin ya d’auki jigidar da sauri ya bi bayanta.
Ba tare daya mata magana ba ya mik’o mata, motsinta da taji tasa ta juyowa da sauri, tana ganinta ta karb’a da sauri tare da washe baki, saida ta dubata da kyau ta kalleshi, bata tsaya komai ba ta fad’a jikinshi ta rumgume shi tana fad’in “Merci mr., merci beaucoup, que Dieus vous b茅nisse.”
A hankali ya shiga k’ok’arin jaye jikinshi, yasan ita a wurinta ba komai bane hakan, d’abi’a ce garesu idan abu ya birgesu suyi haka, yana nasarar raba jikinsu ya kalleta tare da wucewa bai ce mata komai ba, murmushi tayi ta bi bayanshi suka shiga kwana.
Suna tafiya a hankali wayarshi tayi k’ara alamar ya samu sak’o, cirota yayi a aljihu ya duba, da mamaki sosai ya sake k’urawa sak’on ido, sanarwa ce daga gidan bus na mota wai ya samu sak’on kaya ya zo ya d’auka, babban abinda yafi bashi mamaki shine sak’on daga Tha茂lande ne, shi dai baiyi magana da Richard kan wani abu da za’a aiko masa ba, tab’e baki yayi kawai ya mayar da wayar da biyyar idan suka koma gida saiya tafi dan ya k’agu yaga daga ina sak’on ya zo masa.
A hankali ta kalleshi tace “Mr., me yasa k’anwarka da matarka basa so na?”
Kallonta yayi amma bai ce komai ba ya sake kallon gabanshi, cikin rashin damuwa tace “Ina ganin fa kamar tana jin haushi na ne saboda ina zaune gidansu.”
Ko kallonta baiyi ba dan ya fahimci akan Iffa take magana, ba tare data kula da k’yaletan da yayi ba ta sake cewa “Ka fad’a mata tayi hak’uri na d’an lokaci ne zan zauna gidansu, nima ba’a son raina nake zaune ba.”
Ci gaba tayi da cewa “Sannan matarka nasan tana jin haushi na ne dan na aureka.”
Wani murmushi tayi mai kama da dariya kafin tace “Ka fad’a mata ni ba mai zama bace, ba jimawa zan koma inda na fito na bar mata mijinta, kuma ka fad’a mata babu komai tsakaninmu, amma ni gaskiya ina jin tsoronta saboda bata da kirki.”
Kallonta yayi, Farha take nufi fa, yaushe Farha ta zama haka to? Marar kirki? Shi dai k’ala bai sake ce mata ba saida yaji tace “Amma mr. kana ganin Abhi yana so na kuwa?”
Da sauri ya kalleta da mamaki, da k’yar ya iya cewa “Me yasa kika fad’i haka?”
Saida ta tab’e baki tace “Saboda yana so ya kashe ni mana.”
Kallon gabanshi yayi tare da cewa “Ko tamtama bana yi akan soyayyar da mahaifinki ke miki, yana sonki sosai kuma ba zai iya kashe ki ba.”
Matsowa tayi kusanshi tana gyara ledar hannunta tace “To amma me yasa ya so kashe ni?”
Ba tare daya kalleta ba yace “Ba zai iya ba na fad’a miki, ko da ya d’ora bakin bindiga akan ki zai d’auke ba tare daya cutar dake ba.”
Cikin rashin yarda tace “In kasan ba zai iya kashe ni ba me yasa ka taho dani?”
Kallonta yayi hankali kwance yace “Indai har abinda nake tunani akan shi gaskiya ne, to nasan dole akwai wanda zasu kashe ki idan shi ya kasa.”
Da sauri ta kalleshi tace “Su wa?”
D’aga mata kafad’a yayi alamar bai sani ba, hakan yasa tace “Hakan na nufin kenan Abhi na zai iya shiga cikin matsala?”
Jim yayi alamar tambayarta ta gindayar dashi ko tunasar dashi wani abu, tunani ya shiga kan abubuwan da suka faru da kuma tambayarta, akwai fa yiwuwar hakan ta iya faruwa, to idan ma ya faru me ya naka a ciki? A hankali ya kalleta kamar wanda baya son magana yace “Ban sani ba nima.”
Sake matsowa tayi kusanshi sosai ta mik’a mishi ledar hannunta tace “Taimaka min da wannan na gaji sosai.”
Kallonta yayi yana k’ank’ance idonshi yace “Wai ke bakinki baya ciwo ne? Kiyi shiru ko na minti biyu ne mana.”
Da sauri ta mishi alamar da yatsunta biyu alamar tayi shiru, tafiya suka ci gaba da yi sai dai yana hankalce da lura da yanda take tafiyar, alamu sun nuna ta gaji sosai kamar ba zata iya kai kanta gida ba, amma haka yayi banza da ita suka ci gaba da tafiya har suka kusa gida.
Kallonta yayi yace “Kinsha iska sosai ko?”
Cikin hammar jin bacci ta jinjina masa kai alamar eh, da sauri yasa bayan hannunshi na hagu ya rufe mata baki, zafin iskan bakinta ne ya daki hannunshi, yana kallonta tana kallonshi saida ta gama ya janye hannunshi tare da fad’in “Ki dinga rufe baki idan kinyi hamma saboda shaid’an zai iya cutar dake.”
K’ala ba tace mishi ba dan idonta ne suka fara lumshewa alamar bacci, shi kanshi ya sani da gida suke da yanzu kwance kawai zatayi daga hamma d’ayan nan, basa yarda suyi ta biyu indai har bacci suke ji.
Suna shiga gida a k’ofar d’akin ta jefar da hijabin da ledar hannunta ta shige ciki, saman kujerar ta kwanta ido rufe bata sake bud’ewa ba. Mama ce ta d’auke kayan tana shiga dasu ciki tana fad’in “Kin gaji ko?”
Jin bata amsa ba yasa ta aje kayan kusanta ta fito, ko d’aki bai shiga ba ya sake fita dan d’auko sak’on nan.
Yana dawowa ya wuce d’aki ya bud’e kwalin, enveloppe ce sama sai wani carton a cikin, bud’eshi yayi sai yaga tarin takardu ne sai kuma kud’i na dala America wanda suka kusa firgita tunaninshi, da sauri ya d’auki enveloppe d’in ya bud’a dan ganin abinda ta k’umsa a ciki. Dogon rubutu ne a farar takarda kamar haka.
“Salahadeen, ba alfarmarka zan nema ba dan ka ci gaba da zama da Sarah a matsayin mata, dan ‘yata mai matuk’ar tsada ce da kai kasan tafi k’arfin ajinka, amma duk da haka saboda jin dad’inta zan rok’eka da Allah ka rik’eta cikin kyautatawa da kulawa. Na sani ba zasu barni ba kamar yanda nima ba zan juri rayuwar tsangwama ba, Sarah zata zama marainiya gaba da baya, amma ba matalauciya ko matsiyaciya ba. dan ba zan yarda ta had’u da ahalina ba, sun guje ni saboda dukiyata ta tsoratar dasu, babu wanda zai rumgumeta a yanzun da bata da kowa, kai, kai kad’ai gareta. Duk wata dukiya da Sarah ta mallaka a wurin mahaifiyarta ta halak ce, sannan nima na k’iyasta dukiyata ta halak, wanda sune kake gani anan gabanka, kadorori ne na gidaje filaye shaguna k’ananan masana’antu da kuma campagni guda biyu, wannan halak d’inta ne wanda na dinga juya mata. Ka sadata da dukiyar nan ka kuma shige mata gaba a duka al’amuranta, na yarda da kai na kuma yarda da k’wazonka d’ari bisa d’ari. Salahadeen ka fad’a ma Sarah ina sonta kuma ba zan iya yarda a cutar da ita ba.”