NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Shakoor Aghali

Da sauri ya sake komawa baya ya sake nanata kalmar kai kad’ai gareta, wuk’il wuk’il ya shiga yi da ido da tunanin me ke shirin faruwa dashi? Takardun ya d’auka d’aya bayan d’aya yana dubasu, ya jinjina sosai ganin girman tarin dukiyar data mallaka, a hakan ma wai iya halak d’in ce ne aka ware, ko dalolin nan kad’ai zasu isheta rayuwa daga yanzu har ta gama rayuwarta amma a haka ga masana’antu dake gudana suna tato mata kud’i a koda yaushe.

Mayarwa yayi ya rufe a daidai Farha ta shigo d’akin daga wanka, yanda ya ga har yanzu fuskarta a had’e yasa shi sauta murya yace “Wai har yanzu hushi kike dani?”

Ba tare data kalleshi ba tace “Akan me zanyi hushi da kai?”

Wani murmushi yayi yace “Akan abinda ya faru d’azu mana.”

Murya k’asa k’asa tace “Hum! Ya zanyi to tunda tsintaciyar mage ta fini, alamu ya nuna kai da Mama duk kun fi damuwa da ita akai na.”

Girgiza kai kawai yayi bai ce mata komai ba ya mik’e shima ya fito.

Tayi nisa a baccinta sosai taji wata masifaffiyar razana, a firgice ta farka amma ba’a hayyacinta, dan bala’in tsafin da aka mata ake son zare jininta yasa ta fita a hayyacinta, ba zata iya misalta yanayin da take ji a jikinta ba, baiyi kama da sanyi ba kuma ba zafi ba, k’amk’amewa tayi wuri d’aya tana karkarwa idonta rufe gam ta datse hak’oranta sai gab gab suke.

Da sauri mama dake tsaye tana sallah ta ga tashinta a razane, daga tsayen ta sallame tayi sauri ta je kusanta, zaune tayi kan kujerar ta rik’ota tana fad’in “Saratu lafiya? Sarah ke kalle ni.”

Sam kamar bata san tana yi ba, sai dai ita data tab’a jikinta sai taji wani mugun zafi ga uban gumi dake ta tsatsafo mata, kallon fuskarta tayi ta ga idonta a kulle suke, kallon Mamuh tayi dake karatu tace “D’aga sautin muryarki.”

K’ara jawota tayi jikinta ta daidaita bakinta a kunnenta ta fara mata karatu a cikin suratul Baqara. Sun jima haka kafin taji ta fara wata zabura kamar tana son k’wacewa daga gareta, Iffa ta kalla da suma duk suke kallonsu tace “Ki taso min Salahadeen.”

Da sauri ta fita dan kira shi, kasancewar ba bacci yake ba yasa ko da ta bubbuga k’ofar sau d’aya yayi tafi alamar yana cikin sallah, bata sake bubbugawa ba har saida ya bud’e k’ofar yana kallonta, da sauri tace “Mama ce tace ka zo.”

A hankali cike da rashin son magana a lokacin yace “Lafiya?”

Saida ta yatsina fuska tace “Yarinyar nan ce.”

Juyawa tayi kawai ya biyo bayanta da sauri, suna shigo ya ga abinda ke faruwa, da sauri ya zauna kan kujerar yana k’ara kallonta ya kalli Mama yace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:04 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               1锔忊儯6锔忊儯

“Mama me ya same ta ne?”

Yatsarta ta d’ora kan labb’enta alamar yayi shiru, sake matse Sarah tayi a jikinta ta ci gaba da mata karatu a kunne, a hankali taji ta fara d’an sassauta rik’on da Sarah ta mata, yanayin gumurzun da take ne ya canza alamar ta samu nutsuwa, sannu sannu ta sulale kan k’afafunta ta kwanta tana sauke numfashi, ta d’an d’auki sakonni a haka kafin ta d’ago a hankali, Mama ta kalla tare da kallon duk wanda ke d’akin, da mamaki tace “Lafiya ba kuyi bacci ba?”

Cikin taushin murya Mama tace “Ba muyi ba.”

D’an juyawa tayi ta kalleshi tace “Me kake anan kai kuma?”

Kallon Mama yayi ya mik’e tsaye yace “Saida safenku.”

Zai fita Farha kuma zata shigo wacce ta zo ganin abinda ya fito dashi a daren nan, da hannu ya mata alama su koma, gaba ta shige yana bayanta suka koma d’akinsu.

Cikin jin haushi ta kalleshi tace “Wai me yarinyar nan take nufi dani ne?”

Dakatawa yayi daga kabbara sallah daya so yi ya kalleta yace “Kamar ya me take nufi dake?”

Cikin d’aga murya tace “Naga bata barinka ka huta, duk sanda ya dace ace kana hutawa ko samu nutsuwa saita fito da wani salon tsirfa, me hakan ke nufi to?”

Kasancewar baya son yawan magana kuma baiga abin magana a abinda ta fad’a ba kawai ya sake daidaita gabanshi ya kabbara sallah, kallonshi tayi ta jinjina kai tace “Yayi, kayi banza dani mana tunda tare kuke.”

Da safe ma tana baccin da bata samu tayi mai kyau ba mama ta tafi makaranta. Ko da ta tashi ba tayi mamakin ganinta ita kad’ai ba, wanka tayi ta shirya amma da ta zo karyawa sai taga soyayyen k’wai ne, bata cin k’wai ko hasalima bata tab’a cin shi ba, bata sani ba ko da tana yarinya an bata amma da wayonta kam a’a, waje ta zauna kan kujera tana hammar yunwa.

Tayi jiran shigowarshi amma shiru, sai matarshi dake kai kawo wani lokacin a tsakar gidan, duk in ta wuce sai dai ta ja mata tsaki ko harara, ita kuma ko a jikinta bare ta damu, yunwar data dameta ma kawai ta isheta riga da wando.

11:20 Mama ta shigo da sallama, a yanda Sarah ke ganin mama kamar uwa sai kawai ta ruga kamar yarinyar goye ta rumgumeta, ita kanta mama sai taji abun wani iri, dariya tayi tana fad’in “Saratu ke kad’ai ko?”

Saida ta d’ago daga jikinta tace “Mamie sannu da zuwa, kin tafi kin barni ni kad’ai duk yunwa ta dame ni.”

Da mamaki ta kama hannunta suka nufi ciki tana fad’in “Yunwa kuma? Baki ga abun karinki bane?”

Saida ta zauna kan katifa ta yamutsa fuska tace “Mamie na gani, bana cin k’wai ne.”

Cire hijabi tayi tace “Ah bari to na samo miki wani abu ki ci, ai ba kya zauna da yunwa ba.”

Da kallo dai ta bita dan bata gama fahimtar wani abun ba data fad’a, tana fitowa shigowar Salahadeen kenan, gaisawa sukayi tare da mik’o mata ledar hannunshi yace “Dama na siyo muku ne, ni zan fita tare da Kasim muke.”

Cikin tuhuma tace “Shine kuma bai shigo ba? Lafiya?”

“Lafiya lau Mama, kinsan halinshi ai.”

Har ya juya tace “Baka ji ba.”

Tsayawa yayi yace “Na’am.”

Cikin nuna shi da hannu tace “Yar amanata bata ci komai ba, me zai hana ka samo mata wani abu ta ci?”

Saida ya kalli cikin d’akin kafin yace “Shikenan, bari na samo mata.”

Juyawa tayi ta nufi d’akin tana fad’in “Yawwa kayi sauri dan Allah.”

Ko da ta bud’a ledar ta ga gasashen nama ne saita aje ta k’wala kiran Farha, tana zuwa ta gaishe da maman kafin tace “Kinga naman nan Salahadeen ya kawo, ki samu wuri ki juye saiki fitar ma da kowa, su Iffa da basu dawo ba sai a aje musu.”

Kallonta tayi tace “Mama ni kuma? Gaku zaune zanyi rabo?”

Murmushi ta mata tace “Kiyi Farha, karki manta yanzu ko bana nan a gidan nan ke ce babba, saboda ke ce matan d’an na farko.”

Cike da jin kunya da kuma dad’i da izza ta sunkuyar da kai, har cikin rai ta ji dad’in abinda mama ta fad’a musamman daya zama a gaban Sarah ne, ko ba komai zata san bata da gurbi a gidan nan. A wajen Sarah kuma rarraba musu ido ta shiga yi dan bata san ma me Mama tace ba bare ta damu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button