NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Da k’arfi ta dantse hak’oranta dan su daina kakkarwa, mik’ewa tayi ta tunkari mai maganar amma ta kasa cewa komai, mayar da kallonta tayi kan Salahadeen wanda ya gama fahimtar abinda ake nufi ya shiga jinjina kai kawai yana d’an ciccije leb’e, cikin fitar da wani marayan kuka tace “Me yasa kayi haka? Saboda ni kawai zaka nakkasashi haka?”

Sunkuyar da kanshi yayi dan zuciyarshi tafasa take sosai, ba lallai ya juri iya rik’e kanshi ba har da ita d’in ma, cike da gatsali Kabeer yace “Wannan da kike gani ba mutumin kirki bane, shine ya karya min hannu yaro Malik ya karya mishi hak’ori saboda kawai kunyi musayar yawu dashi.”

A hassale Salahadeen ya cakumi wuyan rigarshi cikin d’aga murya yace “Ya isa haka, ya isheka Kabeer, ka daina mata wannan k’aryar banzan.”

Matsowa tayi kusanshi ta nunashi da hannu tace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:20 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 5锔忊儯0锔忊儯

“Sake shi malam, akan me zaka shak’e shi haka? Saboda ya fad’i gaskiya.”

Da k’arfi ya tura shi har yayi baya baya sosai kamar zai fad’i, kallonta yayi sosai ya fuskanceta cikin son k’watar kanshi yana sauke wani numfashi kamar wanda yayi gudu yace “Sarah ki saurare ni, wannan mutumin k’arya yake min, sam ban aikata laifin nan ba, wallahi ba ni..”

Da k’arfi ta d’aga murya tace “Ya isa.”

Kallon juna sukayi sozai shi yana mamakin yanda ta d’aga mishi murya, ita kuma kallon mamakin zai raina mata hankali, cikin kukan tausayin kanta tace “Me kake so ka fad’a min Slahadeen? Kana so ka ce min ba kai bane ko me? So kake ka nuna min kai mutumin kirki ne?”

Dafe kanta tayi da hannu tana rintse ido cikin k’arfin hali ta sake bud’ewa a kanshi tace “Tun a waccen ranar ya kamata na tabbatarwa kaina kai ba mutumin kirki bane, tun ranar daka mari Amit saboda kawai ya tab’a jikina ya kamata na fahimci had’arinka, sakamakon abinda ya faru a waccen ranar ya kamata nasan cewa komai zaka iya aikata saboda zuciyarka a bushe take.”

Marairaicewa tayi cikin sanyi sosai muryarta na fita da k’yar tace “Me yasa Slahadeen? Me ya maka da zaka mishi wannan hukuncin? Dubi yanda ka kassarashi haka wanda ba lallai ya rabu ba, saboda kawai ya mareni a fuska ya d’aga min murya, me yasa zakayi dan Allah? Ina imani da tausayinka suke? Ina suffarka ta zama d’an adam ta shiga ne…?”

Duk da ta kai k’arshen kalmar amma yanda ya kalleta saida yasa gabanta fad’uwa, nunata yayi da yatsa yana ci gaba da sauke wahalallen numfashin nan da yake jin kamar zai tafi da rayuwarshi yace “Sarah ki daina, karki kaini bango, na fad’a miki bani na aikata ba, sharri ya min yana so ya shafa min bak’in panti a wajenki.”

Girgiza kai tayi tace “Akan me? Ya zaka ce ba kai kayi ba bayan nasan waye kai, yanzu tambaya d’aya kawai nake so ka amsa min dan Allah.”

Saida ta gyara tsayuwa sosai tana kallonshi tana lumshe ido tace “Me yasa kayi haka? Saboda so na ne? Ko kuma saboda baka son ganin farin ciki na ne?”

Cike da damuwa kamar zaiyi kuka yace ” Sarah ki fahimta mana, mutumin nan yana so ya…”

Da sauri ta had’e hannayenta alamar rok’o, idonta a rufe saboda sarawar da kan ke mata yana mata nauyi, cikin jigata sosai tace “Dan Allah na rok’eka ka fita a rayuwata, bana so ka sake shigowa rayuwata har abada, ni ba yarinya bace zan kula da kaina, sannan shima zan kula dashi fiye da rayuwata, saboda a mahaifata yake zaune.” Ta k’arashe maganar da d’ora hannu akan mararta, tana fad’a ta juya kan Daniel ta sake durk’usawa gabanshi, kallonshi tayi cike da tausayi tace “Nan asibitin kud’i nasan zasu kula da kai, i am sorry.”

Tana fad’a ta mik’e da sauri ta nufi hanyar barin d’akin, saida ta kalleshi ido cikin ido suka kalli juna kafin ta fice daga d’akin, da k’yar da taimakon Allah ta kai kanta waje ta samu driver suka d’aga. Tana fita ya bi bayanta da sauri a matuk’ar kid’ime, shima a sukwane ya bar d’akin tare da wanda suka shigo, ganin Sarah ta shiga motarta shima ya shiga motarshi yasa ya kalli wanda suka fito yace “A fusace yake, ka bi bayansu kaima kaga me zai faru.”

Da sauri ya nufi wata k’aramar mota yana fad’in “To yallab’ai.”

Sala sala yake binsu sai dai kuma Sarah hanyar gida sukayi shi kuma saiya d’auki wata hanyar daban, hakan yasa ya kira Kabeer ya sanar masa, a take yace masa “A cikin gidan da waje Sarah na kan idona ne, ka bishi kaga ina zaije me kuma zaiyi.”

Nan ma kashe wayar yayi ya sake bin umarninshi, bai zame ko ina ba sai gidan Richard, a firgice ya shiga d’akin a gigice a kuma matuk’ar tafashe, yanda yake kam da akwai bindiga daf dashi zai iya harbin bango ko mai tsautsayi, cikin jin haushi da takaici ya ture tangaren d’in dake kan wata k’aramar drower da flowers a ciki, k’arar ce tasa Richard fitowa da sauri daga toilet yana gyara d’aurin towel d’inshi, ganin Salahadeen ne yasa bai tambayi me ya faru ba ko me akayi saboda sakin daya masa, abunda ya tambaya kawai shine “Wane mai tsautsayin ne kuma ya tab’oka yanzu da safe?”

Cikin karajin murya ya juya yana fad’in “Kabeer Kabeer Kabeer Kabeer…”

Da sauri ya dakatar dashi da fad’in “Me ya mata?” Kallonshi yayi kai tsaye ya jefawa kanshi tambayar ” Haka ya bari ta masa illa dama?

Girgiza kai yayi yana gumtse bakinshi yana safa da marwa, cikin rarrashi yace “Come on man, teld me what happened?”

Bakin gado ya zauna ya dafe kanshi da hannu biyu cikin rawar murya yace “Yayi nasara, ni na so nisanta ta dashi amma shi ya nesanta ni da ita, ban san me zai faru da ita ba yanzu, ban sani ba Richard, amma tana cikin had’ari sosai.”

Da sauri ya d’ago ya kalleshi yace “Tabbas a kewaye da ita ma akwai munafukai da basa zaune da ita dan Allah, to amma su waye? Ban sani ba nima.”

Zaune yayi akan kujera yace “Yanzu miye abun yi?”

Girgiza yayi ba tare daya d’ago ba yace “Ban sani ba Richard, yaushe ne? A ina? Me suka shirya mata? Duk ban sani ba, ban san girman had’arin da take ciki.”

Cike da taisayinshi yace “Ya akayi haka ta faru to?”

A hankali ya d’ago kanshi yace “Da safe ne wani mahaukacin tsoho ya zo gidan…” Duk abinda ya farun ya fad’a mishi, d’orawa yayi da “Idan na sa kaina tabbas zan gano gaskiyar komai, amma yanzu bana da wannan lokacin, bibiyarta da saka mata ido kamar yanda nake tun kafin ta san waye ni shine abinda zan fara yi yanzu, dan ba zan yarda su sake cin mani ba har su kassara ni.”

Mik’ewa yayi yana fad’in “Zan tafi yanzu, amma ka min wani k’ok’ari d’aya.”

Da fuska ya mishi alamar uhum! D’orawa yayi da cewa “Ka bincika min kamarorin tsaro daga titin gidanta zuwa titin sunshine hospital, ina so naga sanda had’arin nan ya faru ya akayi tsohon can mai kama da zallar matsala ya b’ata.”

Dariya Richard yayi yace “Baka da kyau fa.” Wucewa kawai yayi bai ce dashi komai ba, saida ya bar erea baki d’aya Kabeer da wasu su uku suka shigo d’akin da k’arfi, dan tunda wannan ya fad’a mishi inda suka tsaya ya d’auko hanya suka taho, mik’ewa yayi yana fad’in “Malamai ya dai zaku shigo min d’aki haka babu neman izini?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button