A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tace’ Baba kayi hakuri,wallahi ban lura bane,amma ga wannan Ka sai fruit ka sha kar Ka zauna haka Baba,
Kara damke hannunta yayi

yace’ Allah yayi maki albarka yata, Allah ya kareki, Allah ya biyaki duniya da lahira Allah kuma ya jikan magabatanmu,nagode sosai yata nagode nagode,
Sannan yasa Kai ya fice yabar ta a tsaye tana kallanshi, gani take kamar tasan mutumin Amma kuma a, INA????
Horn taji ana Mata tazo ta zanje motar ta,zuwa tayi ta Shiga,ta tafi,
Lokacin da taje gida an fito daga magriba, parking tayi tafito,so take takira drivern ta amma bazata iya daga murya takirashi ba kawai tadau waya ta kirashi,Yana ganin kiranta ya tashi Dan ma yaga zuwanta,durkusawa yayi

yace’ gani madam,
Mukullin motar ta Mika masa,
Karba yayi ganin zata wuce dasauri

yace’ madam amm daman naga gobe naji ance zaki tafi karatu kuma daman ke kadai nakewa tuki a gidannan,gashi kuma Alhaji ya sallameni,shine nace mezanyi da wannan din?
Tsaki taja a zuciyarta sannan

tace’ idan baka so Ka yar,
Tasa Kai ta wuce.
Ikon Allah ya furta Shida tunda yake beta tunanin zai samu motar nan ba shine ya bar sabuwar Ashe rabonsa ce Ikon Allah, Kenan cike da zumudi yadawo benchi sauran ma’aikatan ya fada masu,sun tayashi murna kam balaifi.

Sallah tayi sannan ta dauko Qurani ta karanta, taso ace tayi sauka kafin ta tafi,Amma kuma hakan ma ta godewa Allah da tasamu,kuma Insha Allah bazatayi sakaci ba,tana nan zaune har Akayi Isha tayi, sannan tayi Shirin bacci,ta kwanta Kenan mutumin dazu ya fado mata rai,babu abinda yafi mata dadi irin addu’ar Shi,batasan idan akayi kyauta haka akeji ba,to ita wama ta taba bawa Abu?Neenace kawai take sai mata chocolate kuma idan ta kaimata ma sai tace’ ban gode ba kuma bazan gode ba,amma hakan bayana nufin idan takuma bata takuma cewa hakan ba.ajiyar zuciya ta sauke tana Kara tuno inda tasan fuskar mutumin nan,ganin ba mafita yasata sauka a gadon ta kunna fitilan dakinta, dakin zanenta ta Shiga ta yaye abinda take rufe zanen dashi,zaninka kalakala duk abinda taga ni indai ya Mata kyau to sai ta zana shi,a da tana bawa zanen muhimmanci kusan shine yake cinye Mata lokutanta. Bin zanen take daya bayan daya don duk sunyi kura,Idonta ne ya tsaya kan zanen yaseer da ta masa daukowa ta kura masa ido,tabbas kamar su daya dashi,kayan drawing ta dauko ta zauna adakin tafara zane, mutumin ta zana sak sak Shi,sosai kamaninsu suk Yana tsaye cikin kayan data ganshi babbar riga ce a jikinshi Amma duk ta Kode,ta tsufa sai dai awanke take tas,kallan zanen takeyi wani iri Abu take ji mai kama da nishadi da nutsuwa,ganinta fara jin bacci yasa ta fito da zanen a hannunta ta daura akan mirror takashe fitila ta kwanta.
Da Asuba da ta tashi sai da tayi addu’ah sosai da sosai akan tafiyar ta,batakoma ba ta zauna tana harda har gari yayi haske sosai,komawa tayi ta kwanta,bacci ne ya kuma dauke ta batare data sani ba,jirgin 11 zatabi,bata sani ba tana bacci,mamace tazo ta tasheta tace ta tashi ta fara shiryawa,wanka tayi ta fito,zama tayi ta dau zanen ta kalla itakam har ga Allah wannan Baban ya birgeta kuma tana jinsa a ranta sosai,ajjewa tayi ta shirya,doguwar riga baka ta dauka tasa sai rolling ta fito lokacin har 10 tayi,ganinsu a dining yasata karasa parlourn zata zauna,ai da gudu Yaser

yace’ don Allah kizo muci abinci,kinga daga yau shikenan baza mukara ganinki ba inji mama wai har abada haka ne?
Maganar yaron tabbas ta daki zuciyar ta duk da tasan hakanne amma gudun wani Abu yasa ta ta girgiza masa Kai

tace’ zandawo,
Amma kar Ka fadawa kowa kaji ko?
Tsalle yayi

yace’ ehh bazan fada ba, Yusuf kawai Zan fadawa ko?
Daman tasan sai ya fada masa kuma kamar yarda ya fada bazai fada dinba,
Daga masa Kai tayi,yaja hannunta suka nufi dining,kujera ta ja kusa da yaseer ta zauna tea kawai Tasha shima bata shanyeba,
Masu aiki tasa suka fito mata da kayanta akasa a mota,gaba dayansu suka fita Mota biyu sukayi,daya Abba da Mama daya kuma su,kallan gidan take tana kassimawa a ranta ko zata dawo? Ko bazata dawo ba?wama yasani.sune suka fara fita sannan su Abba,idanta ne ya sauka Akan bracelet din hannunta bata san lokacin da tace’ tsaya,
Dakarfi ta fada sabida haka cikin sauri ya tsaya Allah yasa ma Basu fita daga layin ba ko nisa ma basuyi ba, ko gama tsayuwa baiyi ba ta fito a guje,tafara gudu har taje gidan, fara bugawa tayi mai gadi ta zo ya bude mata yayi mamakin ganinta su da suka fita yanzu me kuma ya kawo ta,saura kadan ta bangaje Shi yabata hanya Amma ya tsaya Yana kallanta,da gudu ta shiga,dakinta ta wuce ta Shiga toilet cupboard ta bude ta dauko zobe da papern nan sannan ta fito kallan mirrorn tayi da sauri ta dauko zanen sannan ta fito gudun kar ta bata lokaci,koda ta fito ma a kofar gida ta samesu,kawai Shiga tayi suka tafi.Ajiyar zuciyar tayi Allah ya taimake ta bata manta ba,har sukaje babu mai magana acikin su ,har su yusseer don yau ba kanta,suma bajin dadin suke ba,isowa sukayi kowa ya fito aka fitar mata da kayanta, suna nan aka fara Kiran su ganin su yusseer na kuka ne yasata itama Jin hawayen na zuba mata, amma Itakam ko fargaba bataji ba bare kuma taji faduwar zuciya,gainin irin kukan da suke, yasa Abba yazo kusa da ita

yace’ ya’isa haka,yi hakuri,ban tambayeki ba na manta ina motocin ki suke ne ban ga ko daya ba daga ciki?
Ko kallan Shi batayi ba

tace’ na bayar,haka kawai tace tasa Kai zata wuce ya riki hannunta, dawowa tayi da baya Amma bata kalleshiba ba envelop ya Ciro a aljihunsa ya damka mata sannan ya saki hannun.wucewa tayi ta tafi.sunanan har jirginsu ya daga sannan suka tafi cike da damuwa don hajiya mama ji tayi kamar an cire Mata wani gagarumin dutse akanta,bata da wata damuwa acikin zuciya amma a fuska kam akwaita,haka bangaren Abba shima hakanne.

Ummusalma kuwa a jirginma kuka tayi mai isarta kafin tayi shiru,bacci ya dauke ta….

     Saidai  muce _safe_ _trip_  Ummusalma ????????????

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
????A BAKIN WAWA????

  • Akanji magna 6 Sai 8pm suka isa, Ummusalma tayi bacci har tagaji ,gawata azababbiyar yunwa da takeji, babu abun da taci tun tea din da tahada ta sha bata Kara cin komai ba,a jirgin ma ba abinda taci kasa ci tayi,ita ba juriyar yunwa ba,ahaka de suka sauko daga jirgin ta kwasa kayan ta,sannan ta tsaida taxi ta Shiga bayan ta fada masa inda zai kaita, suna tafiya tana kallon garin,ga mutanen kamar yanzu ne gari ya waye a haka suka iso har bakin campus din ya kaita,Bayan ya fitar Mata da kayanta,ta Ciro kudi ta bashi(envelope din da Abba ya bata) canji taga ya miko mata,karba tayi tasa ajaka,tana nan tsaye tana kullawa tana kwancewa yanda zata fara daukan kayanta Allah ma yasa trolley guda biyu ne kawai, sai kuma yar luggage sai hand bag dinta shikenan,shahada tayi ta dauka luggage din sai ta afara Jan trolley din tana tafiya a hankali,kana ganinta kasan ta gaji,kawai tafiya take bama tasan room dinnasu ba bare yanda yake ,kawai de tafiya take abinta,wata baturiyar ce ta ganta, tasan ta gaji duba da irim tafiyar da take ga kuma Kaya,Jan trolley din ma kadai aiki ne, wurin ta taje tace” can I help??
    Nodding Kai tamata alamar ehh, trolley din ta karba,suka cigaba da tafiya tambayar ta room din tayi tafada Mata room number din a sama yake don haka sama suka nufa, har suka iso,tare suka Shiga ta ajje mata kayan sannan ta wuce,dakin take kallo ya burgeta komai biyu ne a dakin gado biyu,da bedside drawer sai wurin karatu shima biyu, wardruppe ma haka sai kofa biyu da tagani,ajje kayan hannunta tayi taje ta bude kafa daya balcony dayan kuma toilet ne jakarta ta bude ta dauko abinda zatayi amfani dashi ta Shiga toilet,shima ba laifi ya Mata kyau kamar toilet din gida,kuma gashi a wanke tsab bako kura,wanka tayi da ruwa mai zafi don garin ba laifi akwai sanyi,kuma ga gajiya ta debo, alwala tayi sannan tayi brush ta fito mai kawai ta shafa ta saka wata doguwar Riga,ta shimfida dadduma tafara jera ramuwar sallah,har Isha tayi sannan tayi addu’ah daga nan ta ciro kayan da Mama ta hada mata taci ta koshi.
    Kayan ta fara jerawa a cikin wardruppe tana cikin jerawa sai ga wannan dayan tazo taimaka Mata tayi suka gama gabadaya komai da komai,Zama tayi a bakin gadon itama dayar Zama tayi tare da Mika Mata hannu

tace’ I am Sahr
Mika Mata hannu tayi itama

tace’ Ummusalma,
Wani irin kwalalo ido tayi

tace’ umselm?

Not umselma Ummu then salma,

Ohhhh Salma?
Daga Mata Kai tayi sannan Sahr
Tace’ can I say umsalma?
Daga Mata Kai tayi kawai

Sahr tace’ am from Paris, am studying psychology, o level,and you?

From Nigeria study gynecologist,but I will change the course,I want business and psychology ,I don’t know what to do,
Takarashe cike da tausayi, kallanta Sahr tayi ,amma bata tambaye ta ba tunda ba tasan gynecology amma dai tasan is a good course,
Hannunta ta kamo tace’ kada ki damu uncle Dina Yana aiki a school din za’a San yarda za’ayi idan zaka iya studying Duka biyun to idan kuma bazaka iya dole sai kiyi guda dayan.
Kallanta kawai Ummusalma keyi daga haduwa yau yau din nan Amma shine harda temako?
Sahr cigaba tayi kinga kar ki damu bakomai.
Nodding kai tamata, tace’su zo su kwana anan, tunda ita kadai ce,kafin dayar tazo,daman itama ita kadai take kwana dakin su satin ta guda da zuwa Amma dayar bata zo ba.
Haka suka kwanta tayi addu’ah sannan ta lula tunanin gida,bata taba barin gidansu daidai da na kwana daya ba,amma yau ta tafi tayi nesa dashi tasan ita da gida nan kuma sai a mafarki kuma don a lahira bata zatan Tama hadu da su Abba da Mama kuma,wani sashe na zuciyar ta kuma su Yusseer take tunani ko ya zasuji idan lokacin dawowar ta tayi basu ga ta dawo ba? Tasan tunda tace wa yaseer zata dawo to ya kudurta zata dawo din kuma sai yayi ta kirgen kwanaki,indai itace har yayi ya gama.Sahr kuwa video call takeyi da yan gidan su tana yi tana narka shagwaba,yayindda Ummusalma take kallanta don kuwa ta burgeta mutuka,tunuwa tayi lokacin da take ganiyar mulkinta itama, hawaye ne ya zubo mata tayi saurin gogewa,ahaka bacci yayi awan gaba da ita,daman kuma ta gaji saidai baccin da ta sha a jirgi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button