A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi Sameera tayi kawai, tace’ to shikenan Amma kinga yanzu Zan fita,

Naje to na rakaki mana, banan kofar gida ba?

Shiru Sameera tayi tana kallan ummu, tana wani tunanin ta daban, Ganin haka yasa ummu matsawa kusa da ita,
tace’ Yaya Sameera akwai abinda ke damunki ko? Dan Allah ki fada min, komeye idan za iya taimaka maki Zan taimaka,ko da Addu’ah ce ai na rage maki sosai, Dan t fada min meke damunki? Jinyar Abba?

Hawayene ya zubo a idanta ummu tasa hannu ta share Mata, sannan tace’ Ummu bazaki gane ba, ummu wannan shine abinda nake tsoro gashi kuma yana daf da faru ko kuma nace ya faru,

Sai hawaye, zuciyar ummu ce ta karye batasan taga ana kuka gashi yarda take Mata maganar ma kadai ya isa ya karyar da zuciyar Mai sauraro, Kara damke hannunta tayi,
tace’ ki fada min ko mene, Insha Allah zamu Sami mafita,

Murmushin takaici tayi tace’……..

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

44

Tace’ Ummu na fada cikin tarkon San mutumin da besan inayi ba, be dauke ni komai ba sai kawa,

Ban fahimce ki ba, yaya Sameera me kike so ki fada min?

Ummu, nafada cikin soyayyar wani, watakila ma Shi Yana can Yana San wata, Shi ake kira so maso wani, bantaba San wani da namiji Sama dashi ba watakila ma Alhakin wasu ne ke Bina, bansan yarda zanyi ba,

Kiyi hakuri, Insha Allah komai zaiyi daidai, Amma bakya tunanin Baya San wata dabi’arki ? Shiyasa ma ya dauki a matsayin kawa?

Bansani ba,

Ya sunansa?

Mas’ud,

To mezai Hana kawai ki fada masa?

Ko sansa zaiyi ajali na,bazan taba fada masa ba, nasan mena keyi,

Shikenan to ya Sameera ina da shawara,

Tame Kenan?

Baki da Dan biscuit haka? Alawa de haka na Dan sha, so nake kawai naji ina Dan cin wani Abu,

Tashi tayi tace’ Bari na dauko maki cookies,

Tana ganin ta fita tayi sauri ta dauki wayarta tasa a silent tasaka a kasan pillown ta karma taga haske,

Bata jima sosai ba,ta dawo dauke da cookies din, ta bata ita kuma ta koma ta zauna, ci fara yi kadan kadan,

tace’ ko mu Bari sai gobe yanzu kinga Mama ta kirani wai na koma gida dare yayi,

Tace’ to shikenan sai da safe,

Fita tayi daga dakin ta koma dakin su yusuf knocking tayi a bakin kofar,
yaseer yace’ waye?

Nice nan,

Me zaki mana,

Ba ruwanka nazo ba,

Bude kofar tayi ta Shiga suna kwance kowa ya danne kan waya Yana fama,
tace’ Dan Allah ina San kumin abu,

Yusuf yace’ me Kenan? Harda su hada mu da Allah yau,

So nake yau Daya kawai Ku zauna da ya Sameera kuyi hira da ita irin ta ‘yan uwan taka Dan Allah,

Meyasa to?

Kawai inasan hakan,

Yusuf yace’ Kunyi magana da yaya salama ne?

Idan kaje Ka tambayeta,nidai ga abinda nace,sai da safen Ku,

Ya fice ta bar su anan,

Tashi sukayi suka Shiga dakin ta, ganin ta a kwance tana tunani yasa,
Yusuf yace’ ya Sameera lafiya?

Tace’ yusuf yau kuma?

Yaseer yace’ Baki da lafiya ne?

Kara sawa ciki sukayi suka zauna a bakin gadan,

Yusuf yace’ mama ta Damu da rashin zuwanki, me zai Hana gobe kije?

Yaseer yace’ kullum sai tayi kuka,

Tace’ shikenan? Abinda ya kawoku? Naji tou zanje, Ku tashi Ku tafi,

Yaseer yace’ a,a mun kawo maki wani saban labari ne fah,
Daga nan kuma suka fara wannan yayi wannan yayi wannan ya Hado nashi wannan ya kawo nashi, tuni taji zuciyar ta wasai babu wanj damuwa kuma itama ta warware sosai suna zuba zancen.

Bata taba tunanin younger brothers will make you laugh even when you are sad. And make your life more charming and Happyyyy,

Having a Brothers is blessing…..

????????????????????????????

Yaushe za’a sallame mu doctor?

Doctor yace’ ehh zamu gani zuwa gobe lahadi sai mu sallamake, Amma fah bed rest na kwana uku zuwa sati,

Yace’ to shikenan, Allah ya kaimu,

Mama da ta shigo yanzu shikuma likita na fita, ta samu waje ta zauna,

tace’ Alhaji dazu kana bacci lawyern Ka yazo yace za’a daga ne tunda Baka da lafiya ko a za’ayi wannan Monday din,

Yace’ naji sauki, ai babu abinda za’a fasa, sai nadawo da Duka kadarata ta dawo halalina,

Tace’ Allah de ya bamu sa’a,

Yace’ idan Allah yasa na dawo da kadarata kasar nan zamu Bari, gaba ki dayan mu kuwa,

Amma Alhaji hakan shine daidai,muje muyi rayuwar mu cikin kwanciyar hankali,

Bari kawai, nasan kudin da Zan samu a wannan shari’ar ai dayawa, ga sata ga karya,ga cin amana duk Shi daya,

Tace’ Allah ma zai bamu sa’a Insha Allahu Rabbi,

Shiru sukayi na wani lokaci kafin yace’ Ina Sameera bata Zuwa ta dubani,

Mama tace’ tun sanda tazo din nan bata Kara zuwa ba, har yau kuwa,

Shiru yayi na wani lokaci kafin yace’ idan komai ya kammala kawai ta fito da miji ayi Mata aure,

Komai dai yayi daidai Alhaji wannan duk Mai sauki ne,

Mai sauki ? Shiyasa Naga kullum kina kukan rashinta ai.

✨✨✨✨✨✨✨

Tunda ta tashi daga bacci ta gyara ko ina tasa turare da freshener da kullum sai tasa ko tayi Shara ko batayi sai kaga kamar an share duk bayan kwana biyu take gyara gidan ta,ba Yara ba, ba Baki ba, ta kuma saki labulaye ta kunna ac, tuni zakaji wani sihirtaccan Kasala Yana sauka a jikinka da dadi jiza kayi bacci kawai kake bukatar yi da hutawa,
Bayan ta gama ta Shiga kitchen shima ta gyara sannan ta daura breakfast dayake tasan za’ayi Bako tana Gama breakfast tayi lunch bata ita ta Gama ba sai shadaya, ta jera breakfast din a dining sannan taje tayi wanka, riga wando tasa masu kyau rigar fara da ja ja a wuri bottle din shikuma Wandan ja ne, sai tasa jan Vail tayi kyau sosai gashi yau har da su goga pink lip bakinta shape din love sai ya Kara fitowa gashi ta tsuke Shi, tasa takalim ta fito.
Dakinsa ta nufa har lokacin bacci yake, ajiyar zuciya tayi tazo kusa dashi ya zauna tana kallan fuskar Shi, yarda yake bacci, murmushi tayi ta kai hannunta ta shafa shi, ya kifta ido, ta rufe Mai hanci da baki tuni ya bude Ido ganin ta tana murmushi yasa Shi cire hannunta,

yace’ wannan muguntar fah?

Murmushi tayi Mai kyau Wanda dimple dinta ya Loma,
tace’ Ka dameni da munshari,tun dazu nake tashinka kaki Ka tashi,

Mika yayi Akan gadan ya tashi zaune,
yace’ nine ma ke, karewa.

Aikuwa ni banayi,

To da kika tasheni mezaki Bani,

Bakomai kawai Ka tashi kayi Wanka, nake ganinka,

Hmmm ke gashi ba..mstw,
Wai ma yaushe ne wai?

Yaune mana, zuwan bakon Ka,

Mtsww ke kin damu da zuwan sa,

Kaima Ka damu,

Naji tou, tashi ki hada min ruwan ka,

Ai na hada,

Yanzu na huce ai,

Be huce ba,

Kince fah kin dade kina tashi na kinga ai ya huce, kuma daman yau kinyi lefi,

Nashiga Dakin kakata menayi? Kuma ni sarkin laifi,

Yace’ Baki gaida Dani ba,

Matsowa tayi kusa dashi sosai tace’ baby ina kwana? Ka tashi lafiya?

Lumshe Ido yayi ya bude yace’ Baby? Ni? Woww,Kara fada muji?

Kafe bakinta yayi da Ido, ta bude Baki zatayi magana Kenan taji nashi ya ciki, sun jima suna aikawa da juna sako, Vai din kanta ya jima da fita,sai kuma ya saketa ya rungume ta zuciyar Shi Yana bugawa da sauri sauri, sai da ya daidaita kanshi

yace’ ya naji lema a kanki,be karasa bushewa ba,

Turo Baki tayi tace’ to tunna jiya ne,

Yace’ ohh haka ne fah, Amma Zan duba da kaina sai na tabbatar,

Saida ya sankan ce, tace’
Haka Yana da kyau Mr lizard,

Ta zari Vail dinta tayi waje da gudu, murmushi yayi tare da girgiza Kai ya Shiga toilet ashe ko ruwan ma bata hada ba, kafin ya fito ta gyara dakin ta fece.

Tana zaune a parlour ya fito yace’ ke Daya ina suke?

Tace’ ba key ban ganshi ba, kuma Basu zoba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page