A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yake tayi tace’bakomai kawai ina tuna wani Abu ne shiyasa,

Murmushi kawai tayi tace’
Anty me aka kawo daman kwadayi kwadayi nakeji, tafada kawai don ta kawar da tunanin da takeyi tasan daman a
hakan zata faru ga mutumin da Baya Sanka kuma yanzu yake kyautata maka,
Budewa tayi suka ci ita de antu kadan taci ta tashi,itamannawani dayawa taci ba dan daga ji na sayar wane.

Bayan sunyi sallahn la’asar ta Shirya tsab cikin shigarta ta kullum doguwar Riga tayi rolling ita kanta Anty taga tunda tazo sune kayanta batasa antamfa, sallama tayi Mata ta fita,

Anty tace’ kibari driver ya dawo sai ya kaiki,
Tace’ a,a Anty Zan tafi kawai,
Allah ya kiyaye Anty tace,

Allah ya taimaketa tana fita taga mai napep ta hau tafada masa inda zai kaita,
Yana ajjeta ta bashi kudin Shi ta Shiga gidan, bakowa a parlourn sai TV gidan de gashi nan yayi wani kaca kaca da shi duk an bata an zurzubar da abinci, a fili tace’ ohh sai kace marar hannu idan ya zubar da abinci bazai share ba, tsaki taja ta wuce dakin su, gadan ba’a gyare ba dakin ya danyi kura gashi nan ga kuma takardu daya barbaza a wurin kujera da kasan carpet rolling din ta cire ta cire doguwar rigar ta tasa wata yar Riga marar nauyi iya Ka gwiwa armless mai laushi da ita, ta fita ta dauko kayan aiki ta fara gyarawa sai da gyara tsab ta goge na gogewa ta tattare komai ta adana, toilet ma ta Shiga ta wanke Shi tass danma de taga kamar Yana wanke toilet din amma de wanki ta yafi nashi sau dubu ma kuwa, ta hada kayan shi kanana ta wanke su tas ta shanya a toilet din, fitowa tayi daga dakin ta dawo parlourn har zata wuce sai kuma tace bari ta gyara shima tas ta gyara ta goge komai tayi mopping kitchen taje ta zubar da ruwan ta kofar baya ta kitchen gayayi tagani tare da kasko a wurin,dauka tayi ta ta kunna gas ta daura Shi akai ta barshi ta dawo tayi arranging Abubuwan da wargaza tana aiki, sannan ta koma ta duba dayake ta sa wuta kuma a bushe yake tuni ya kama ta zuba a cikin kasko windows ta firo parlour wurin turen wuta ta nufa tasa Wanda zata sa tashiga daki har toilet tayiwa turaren wutar ta dawo parlour shima tayi Yana karewa tana sa wani a haka har ta gaji taje ta ajje a lungun dining tare da kunna ac, dawowa daki tayi ta kunna ac sannan ta Shiga wanka bata jima bata batasan ya dawo ya tarar da ita shiyasa ma ta fito da wuri gashi yanzu biyar tayi, body spray kawai ta fesa ko mai bata fesa ba, sai dai kuma tunda ta fito takejin hayaniya tana tashi a parlour ita Tama zata tv ce sai dai kuma tunawa da tayi ta kashe kuma muryan mace takeji tana fada, wardrobe ta bude don sa Kaya taga hijabinta kawai tasa ta fita turus taja ta tsaya a bakin kofa ganin mutanen, ita kuwa Saima cigaba tayi da fada,

tace’ wato don kun rena ni ina magana kunyi min shiru ko?
Sannan ba’a samu Wanda zai dauka kayan nawa ba ya wanke kome?

Ameera tace’ Wallahi sun mugun Rana mana hankali banzaye ‘ya’yan shegu kawai, daman fa kinsan halin ‘yan Dan kauye idan yayi klin bada sunan wani abu ba,

Tace’ bedamena ba nidai kawai adau kayana a wanke mun kuma wallahi duk sanda kuka Kara kunnawa mutene wannan hayakin sai ranku ya baci,an koreku kunki korowa a Karo na ba adadi shegu dagin matsiyata, Mus’ab yace’ kiyi hakuri zamu wanke,
Wani wawan Mari ta saukar masa,

tace’ hakuri? Kana da bakin bada hakuri Amma Baka da abakin amsa? To ni Saima sai naci uwar mai ……

Jikake tas, an wanke ta wani azabban mari,bata Gama Jin azaba aka kuma sauke Mata wani,ko bata tambaya ba tasan Binaif ne sai dai dagowar da zatayi sukayi four eyes da wata yarinya fuskarta a dauke tamau tana Mata wani irin kallo,kallon da bazata ta iya cewa na menene ba,

Fuska a dafe tace’ Wacece ke?

Ummusalma ta Kara daure fuska gashi daman fuska a daure an Kara tamketa tamau, ta hada gira idan nan ya Kara fitowa tayi folding hannayenta a kirji,
tace’ mace ce kamarki,sai dai ba ballagaza ba,marar hankali, shashan ba kamar ki.

Daga hannu tayi zata mareta taja Baya,
tace’ wanne zunubi nayi da zaki mareni?
Hahaha ba’a marina,ba’a dukana,ba’a fada min magana ko anyi bashi ne, bakisan Wacece niba kamar yarda basan Wacece keba sai dai yanzu nasan ke Wacece,

Ameera dake gefe tana kallan ikon Allah ta matso tace’ Wallahi tunda kika mareta sai kinhi dakin sani banza karuwar su mai kawo Ka…….

Bata karasa ba itama aka sauke Mata nata raban, ita har sau hudu,
Ummusalma taja ta tsaya a tsakiyar su,

tace’ idan naji wani ya Kara magana kuma ban Gama magana ba hmmm bansan mezanyi ba,

Saima tace’ uwarki zakice kina magana sai kace kin haifemu shegiya karuwa mai kama da…

Murmushi tayi ta matso daf da ita tace’ Naji ni karuwance a gidan aka ganni Wanda za’a iya cewa ni matar gidan ce,ke kuma fa?
Ehhh?
Ai batayi aune ba taji ta a kasa Ummusalma ta korfeta ta fada,gashi unexpected ne,ga titles har kanta da hannunta sai da suka bugu kasa daga hannun tayi,

Ummusalma tace’ waya fada maki ana karya doka ta? Ehh?

Murmushi tayi Wanda idan ba kallanta kayi ba bazakace tayi ba, idan ma kallan nata kake to sai Ka lura don ko second daya beyi ba ya bace a bakin ta, kayan dake kasa ta kalla inner wears ne ma Dan tsabar tambada Namiji zai wanke sai kace Dan daudu, mus’ab da mas’ud ta kalla Wanda suke kallanta tun fitowar ta suna mamakin ta inda ta fito sude basuga zuwanta ba kawai Marin suka gani, wata uwar harara ta maka masu ba shiru suka dukar da Kai kasa,

tace’ kwasu min Kaya,

Mas’ud ne ya kwasu ya Mika Mata shima Mus’ab ya kwashi sauran duk suka Mika mata,wata harara ta maka masu

tace’ bata,

Kallanta sukayi irin taya zamu bata Abu a kwance,

Tsaki taja tace’ ku watsa Mata mana,ita din uwar kuce?
A tsawace ta fada ranta yakai koluuwar baci ta tsani abun haushi,

Da sauri mas’ud ya watsa mata shima haka mus’ab din, tsaki taja dawo da kallanta ga Saima wacce take kwance ta kasa tashi daman ga aba raguwa ita kuwa Ameera tunda taji Marin da bata taba jiba tasawa kanta salama ta bar wurin Aneesa ce ta fito itama data ta rashin kunyar,

tace’ Waccs tsinanniyar ce take tada mana hankali ne ? Ina bacci ana min tsawa zanci uwar yarinyar fah ba ruwana,

Idan ba saita su tayi ba bazata bar gidan nan ba wato itace tsinanniya,hmmm shiru tayi sai da ta Kara so,

tace’ karuwa ce da dukan ‘ya’yan masu gida?
Mas’ud ta kalla ta gallawa harara cikin fillancin,

tace’ mareta?
Zaro ido sukayi alamar bawanda zai iya,

tace’ Ka mareta nace ko? Sai na mareka ni tukunna kaji zafi sai Ka mareta?
Ganin shuru yana bata Mata lokaci zatayi magana taji saukar Mari a fuskarta,ai batsan sanda ta dauki hannu ta zabgawa mas’ud wani lafiyyan Mari ba, zafin da yaji yasa Shi Marin Aneesa tare da korfeta ta fada, faduwar ta ma tafi ta Saima tsabar rudewa kasa ihu tayi sai dai hannuna yenata gaba daya data kasa kasagawa, ( taji Maza ???? )

Ameera data fito daukan ruwa ganin abinda ya faru a gaban idanta ba karamin mamaki taji ba,Ashe de kowa Dan iskan kansa sane samu ne kawai basuyi ba,

Ummusalma tace’ barganin ya maki wannan abun danawa Yana zuwa a gaba daga ke har yayar ki,ga kayan nan inaga ko ba kutafe bane, juyowa tayi takara maka masu wata hararan tare da masu kallan uku saura kwata ta wuce su da kallo suka bita har ta Shiga daki kallan kallo sukayi ganin inda ta Shiga,Saima dakyar ta iya tashi ta shiga daki ita kuwa Aneesa sai rarrafe tashiga, dariya sukaji a bayan su hakan yasa suka jiyo wurin kofa ganin bb Yana dariya sosai yasa suka karasa wurin sa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page