A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hajiya da tuntuni tana parlour jin wannan batu na Umma yasata Jin wani dadi daman ko bata koreta ba tana da niyyar koranta don ta lura wannan yarinyar akwai sa ido baya ga haka kuma bata jin zata iya barinta saboda gudun tuna mata asiri, shiyasa take yawan koren yan aikinta cikin sauki abinta, wannan ma kuwa sao gashi Umma zata koreta, murmushi ne ya kubce mata,tayi Maza ta mayar Shi gudun magana, Anty ce ta fito da sauran yaran Jin hayaniya,

Anty tace’ Umma ina wuni,
Harda tsugunnawa irin biyayyar nan,

Umma da har yanzu bata zauna ba tana dagare da sandar ta ga glashinta,ta kalleta ta tabe Baki,

tace’ hmmm ai wuni ya ruga da gudu, tunda yanzu magariba zamu shiga, ai nazaci gaisuwar ma kun manta yarda akeyi tunda ba’a San hanyar gidana ba,
Ganin Saima da tayi yasata rabka uban salati,

tace’ yanzu daman wannan yarinyar batayi aure ba ?? Wannan ai banbanci na da ita kadan ne, kawai ita ras take tafiya nikuma ina dogara kafata kuma bana gani da kyau,Amma babu wani banbanci taab lalle akwai kallo, idan ban manta ba kinkai shekara dai dai dai har ashirin da takwas haka ne ko ba haka ba?

Hajiya tace’. Umma ashirin da bakwai ne ai,

” Kwana nawa ne za’a ce mana da takwas ji shashanci banza,daman kina nan kika barni a parlourn ko tayin Zama ba’a min ba??

Saima tace’ naji kina zancen korar mana mai aiki,gaskiya bazamu lamunta ato ke zakiyi mana aiki ne ko me?

Daddy ne ya daka Mata wata tsawa yace’ mahaifiyar tawa kike fadawa haka,
Ya tafi gadan gadan zai buge Umma,

tace’ a,a saurara bashi ya kawo ni nan ba, yanzu abin da za’ayi shine Zan Kori mai aiki idan na koreta kuma kune zaku keyin komai da komai idan kuma kai,ta kalli Daddy, Baka da ‘ya’yanka sunayi ba to kana nufin kace minne bana da martaba mana da kima Bana da daraja a wurinka,Zan kuma sa ake bincika min,Naga karshen rashin kunya,kuma kuna Kara fadar magana Zan bullo wani Abu,ko na dawo Zama a gidan nan fakat,
Dame magana? Shiru kake ji anyi babu Wanda yake ko tari,sai yaran da suke kumbura Baki suna Mita iya ka zuciyar su, Binaif ta kalla,

tace’ Kai kuma muje Ka nuna min dakin wancan kurmar na Gama aikina na fice,
Ja yayi ya tsaya ko kallanta beyi ba,

Tace’ laa shikenan shima ya koyi kurmanci wuce nace ko sai na maka maka wannan sandar ne,
Ganin tana Shirin maka masa yasa Shi yin gaba yana gunguni, itama tana digisa kafa da dogara sandarta ta bishi a baya, sai dai kafin tayi Rabin parlourn Shi yaje kitchen, aikuwa ta tsaya,

tace’. Kai,Kai audushakuru, badakai nake ba?
Dawowa yayi kawai beyi magana ba, ya tsaya,

tace’ a hankali zaka bini kasan da aka Gama gidan ma ba’a kawo ni nagani sai da aka zuba Matan gwal sannan nama San da zancen gidan,kaga babu inda nasani, saboda haka bini a sannu, sannu sannu bata hana zuwa yaro sai dai a Dade ba’a jeba,
Juyawa yayi kawai ya fara Jan kafa shi be taba wannan tafiyar bama,ahaka de suka karasa har kofar dakinnata, knocking yayi yaji shiru zai kuma yin wani,

tace’ matsa min ni na Shiga ai dakin Bana ubanta bane,
Matsa Mata yayi ta bude ta Shiga,tana Shiga ita kuma tana fitowa daga toilet niyyar daman tana fitowa ko bata zoba ta dauki kayanta ta fice, ganinta da tayi yasa sunkuyar da Kai kallo,ta fara wasa da hannunta,dukda gabanta Yana faduwa Amma babu wata alama a tattare da ita, ita kuwa Umma kallan tsab ta Kare mata cikin wata murya mai sanyi irin tasu ta tsoffi da tunda tazo gida batayi ba ,

tace’ Ki hada hada kayanki zamu tafi dake kinji ko?
Dagowa tayi ta kalli matar ji tayi matar ta tafi da ita, bakadan ba Ashe ba korarta zatayi ba ita zata dauketa, amma kuma a zahiri bata son ace bata dauke ta ba,
Shima kansa Gogan da yaji abinda tace wani dadi ne ya kamashi, zuwa tayi bakin kafita da ta ajje hijabinta ta dauka sannan zata dauki kayanta,Umma

tace’ ina ke ina daukan kaya haka ajje,.
Binaif ta kalla Wanda yake tsaye yanan kallanta komai nata a nutse takeyinsa, tabe Baki tayi,

tace’ zoka daukar mata,kasata a mota kuma kaima kasande zaman gidan nan ya kare maka bakai ba gidan nan tam,
haka kawai, tace tasa kai ta fice,tana gogarawa ta fito,sukuwa Yan gidan tunda ta tafi kowa ya fara fadar abinda zai fada,suna jin karar sandar ta kowa yayi tsit ya samu waje ya zaune,ko kallan su batayi ba,

tace’ idan anga dama azo a mayarni gida,
Da Daddy take hakan yasan Shi tashi shima be ko kalli inda suke ba,yaga alamr kansu na rawa to dole zai seta sukuwa don bazai iyuba ya biye san zuciya ya Saba wa mahaifiyar sa,
A hankali yake tafiya har suka iso wurin motar bude mata kofar yayi ta Shiga ta z zauna Binaif ne yace’ Daddy kawo a kaisu,Mika masa key din yayi shikuma Daddy ya zagaya gaba ya Shiga sukuma suna baya,babu wanda yayi magana har suka iso gidan Umma.
A parlour suka zauna Binaif da Ummusalma a kasa sai kuma su Daddy a kujera,
Daddy ne yayi gyaran murya

yace’ Ummusalma,
Sai ta dago ta kalle Shi sannan ta maida kanta kasa,haka nan taji gabanta ya tsananta gudu, yacigaba,

yace’ Nayi maki wani laifi, laifi Zan kirashi amma kiyi hakuri ki yafe min, don Bana Jin wannan laifin zaki iya yafe min Shi, nayi abinda Iyaye ne kawai zasu a yafe masu a matsayin su na iyaye, sai dai kuma ni ba Mahaifin ki bane asali ba, ban taba ganinki ba sai dai mai kamarki,kiyi hakuri Ummusalma Ina me Baki hakuri,
Numfashi taja sannan yace’ na daura maki aure da ‘dana Abdulshakur Binaif.

Wani irin zillo taji zuciyar ta tayi sai dai kuma bata iya dagowa ta kalle shiba Jin wani nauyi da takeji,babba dashi Yana tacewa tayi hakuri, gashi kuma Yana cewa bashi ne Mahaifin taba,
Cigaba yayi yace’ wannan shine kuskuren dana aikata a gareki ina mai Kara Baki hakuri da kiyi hakuri, bakomai yasani aurar dake ba ga Binaif sai irin abubuwan da ake fada min game da ke ku biyun, sannan kuma bana San ace shine yayi sanadiyar wargaza maki farin ciki,ki gafarce ni,nasan bazan cancanci yafiya ba daga gareki amma dole na nema wannan alfarmar,

Ganin idan ta barshi zaici gaba da neman yafiyar ta,koba komai shima Mahaifine a gareta tunda ya rike Mata ‘yan uwa ya Gama Mata komai, ganin zai Kara yin wata maganar don har yace ki ya, da sauri

tace’ Daddy kayi kowanne irin Abu da zakayi ganin Ka Kare martabar ‘yarka,kadena Bani hakuri don kaima Mahaifine a gareni, Bani da wani Abu da San saka maka dashi sai addu’ah ita kadai Zan iya saka maka dashi,Daddy kadena rokata gafara don min kawai umarni zaka Bani na bi, Daddy Ka ubane kuma mahaifi, Wanda ba Mahaifin kwarai bane zai iya ganin za’a bata ‘yar wani beyi magana ba,Amma Kai tunda har Ka iya yanke wannan hukunci Ka aurar dani ga danka,hakan yayi min dadi, dukde abinda ake zargin muna aikatawa ko kusa ba haka bane, Amma Daddy ba komai a nawa ganin gata Ka min, gatan da ko Wanda ya rike ni bemun ba,kuma Ka nuna min ina da mutunci a Idanka, haka kuma Ka nuna min cewan baza’a cuce ni ba kayi shiru,gashi kuma Kaidin shugaba ne adali,
hawayene ya zubo a idanta sharewa tayi taci gaba dacewa Baka San wacece ni ba Ka hada zuri’a da ni,Baka da kome nawa ba Ka hada aure na da ‘danka. Shiru tayi tana share hawayenta dukda kokarin da take na kar su zubo amma inaa abin yaci tura, cigaba tayi ,

Mahaifin da yake amsa sunansa na Mahaifi a gareni yaso ace na bi duniya,duniya ta wulakanta ni,yaso ace na lalace, lalacewar da bazan muru ba, yaso yace ya lalata min tarbiya, tarbiyar da Zan ruguza tarbiyar wasu, be nemi yafiya taba sai Kai da kamin gata? Bedamu Dani ba sai Kai da Ka damu Dani? Be kiyaye inganci na ba sai Kai da ka kiyaye? Be martabani ba sai Kai da Ka martabani?? Akan me zaka kake ta neman gafarata,Alhali kuma mu yakamata mu nemi gafarar Allah, Daddy Baka min komai ba, Baya ga haka Kai ne mutumin da Ka rike ‘yan uwa da amana Ka Rene su Ka ciyar dasu Ka tufafar dasu,dukda neman keya haddin ‘yarka da sukayi amma baka koresu ba a gidan ka,Ka tura su karatu,babu irin sharrin da ba’a masu ba Amma haka kake kade kunnanka, wannan Abu da kamin Basu kadai kayiwa ba hardani ‘yan uwa nane kamar yarda basu bakin yimaka godiya haka nima, hakan be isa nayi maka biyayya ba?
Kawo yanzu kuka yaci karfinta,shiysa tayi shiru ta kifa kanta a kujeran dake kusa da ita,tana cigaba da kuka,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page