A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Bata juyo ba, tace’ taabb kujimin da mutum Shi Bemin wanka ba daya wahalar dani sai nice karama Dani Zan masa wanka, cib,
Sarai yaji abinda tace, yace’ magana kike?
Juyowa tayi ita tazaci a zuciyar ta,tayi maganar da yake a fuskarta,
tace’ a,a kawai fah,
Sai kuma tayi shiru, takowa ya fara yi tana ja da baya Yana takowa tana ja Baya, haka sukayi tayi, bayan da zata ja kawai tajita tsudum a cikin ruwa, me zaiyi idan ba dariya ba,
Tsayawa tayi sororo acikin ruwan tana kallan shi, yau ta taba ganin sa yayi dariya haka, sai da taga yana murmushi, sai da ya tsagaita dariyan Amma still da murmushi a fuskarsa, ya zauna a bakin bath tub,
yace’ tsuntsun daga Sama gashashe,
Daure fuskayia bata yarda ba, babu wasa a fuskarta,
yace’ yarinya duk wani cikar ki da batsewa sai dai an…
Ruwa ta watsa masa hakan yasa Shi yin shiru shima ya watsa mata haka sukayi tayi be Masan sanda ya Shiga ruwan ba shima sai dakyar ta yarda yasata a ruwan zafi kuma taji sauki laifi sannan ta fito shikuma yayi wankan sa, kin Zama tayi a dakin ta koma dakin ta, ta shirya atampa tasa bata daura Dankwali ba ta fito, ta zauna a dayan parlourn, tana Danna waya,wani lokacin kuma ta kira, ta jima sannan ya fito cikin kanan kaya sai kamshi ke tashi, sannan sukayi breakfast, sai da suka Gama,
yace’ muje na rakaki kiga gidan ki,
Batayi musuba suka fito suna zagaya gidan har part din su Mas’ud suka je, three bedroom ne a ciki sai parlour sai kuma kofar baya, yayi kyau shima, suka zo Garden,
tace’ meyasa ba’a Kula dashi?
Yace’ Nima bansani ba,haka kawai,
Girgiza Kai tayi kawai, yace’ Allah ya shirya ni ko?
Tace’ ohh daman idan Ka girgiza Kai abinda kake nufi Kenan?
Yace’ kusan haka?
Amma ba haka bane,
Yace’ Kai kekam ko?
Menayi?
Babu komai,
Suna tafiya sun zo wurin field dinsu,
tace’ idan umma tazo gidan nan ca zatace gida ba rahama, babu iska, babu sanyi sai sanyin nasara,
Murmushi yayi yace’ Umma ai, jarabar ta tafi karfinta,har addu’a nake Kar Allah yabani Dan ko ya masu halinta,
Tace’ ba ruwana idan tajika kaida ita ne,
To na nawa kuma, sai dai Kar a kuma,
Tace’ wai tsaya kaga wata kofa a can karama, kuma kaga wata ma anan suna kallan juna,ina ne?
Murmushi yayi ya rungume ta, yace’ nazaci bazaki gani ba, shiyasa ban fada maki ba,
Tace’ko bangani yau ba,wataran zangani nida gidana?
Yace’ haka fah masu gida,
Fadi Ka Kara,
Ina ne?
Yace’ muje mu gani ko ina ne?
Zuwa sukayi ya bude da key din hannunsa suka Shiga gida taga ni irinna su komai da komai iri daya tunkafin ta Shiga tasan hakan,
Yace’ laaaa ai gidane,
Tace’ gidan waye?
Yace’ muje muga wancan shima,
Shima zuwa sukayi suka ganshi yarda nasu yake shima haka yake,
Tace’ gidan Glip da Chatty ko?
Murmushi yayi ya yaja kumatun ta yace’ haka yake, Sweet Mi Amor,
Tace’ idan ba’a fada min mi amor din nan ba Kar a Kara fada min,
Yace’ angama Madam,
Tace’ Mai gida,
Daure fuska yayi ya matse hannunta dake cikin nasa,
tace’ ouch da zafi Mai gida, Haba Malam zafi fah,
Yace’ karki Kara fada min kinji ai?
Angama mai…aww angama Malam,
Harara ya dalla mata,
tace’ laaaa daman Malam Ka iya harara haka? Kaga yarda kayi kyau kuwa, Bari na ma hoto kamin kyau sosai Dan Kara muga?
Banza yayi da ita suka karaso gaban parlourn,
Tace’ mu yaba asa mana kujeru ana ba?
Yace’ za’a sa,
Bari naje na dauko mana,
Zuwa yayi ya dauko masu, suka zuna suka daura kafa akan table,
Tace’ nagaji dayawa,
Yace’ ayyyaahhhh sorry Madam,
Tace’ idan kace madam din nan irin masu sai da abinci nan yarbawa ko iyya murai haka nake ji, kawai haskoni nake acan,
Dariya yayi yace’ ni kuma fah?
Tace’me ?
Dakike cemin mai gida,
Aww Kai ai haka naji ana fada maku,
Naji wannan.
????????????????????????????
Hajiya ki fito ki Sha iska muma yau zamu bar gidan nan, sabida haka gashi nan an tanadar maki komai, da komai na bukata idan kina neman Abu ki Kira wannan wayar ki fada komai duk abinda da kike so,an mallaka maki wannan gidan halal malak, ga takar dun, sai dai bake ba fita kinsan Idan aka ganki da matsala, idan zaki fita kisa nikaf,
Tace’ yaro Ka fada min mana, waye ya maido ni nan,
Yace’ Hajiya Kenan, gaskiya bazaki jiba, abinda aka ce kawai kiyi, sannan zanke kula dake ga kudi ance na Baki,
Tace’ ni yanzu mezanyi da su?
Yace’ ance na baki ne,
Yace’ banda wayo Banda wayo Amma kije ko ina,
Tace’ Banda yawo Amma naje ko ina? Idan Zan fita kuma masa nikaf mekenan?
Yace’ abin nufi daga Layin nan sai Layin nan,zaki ke ganin mu ai, muna Sami Ido, mude mun fada maki mun fita,
Shiru tayi tana tunani to mene ma amfanin yawo? Ina zataje? Wa tasani? Daman ta Saba rayuwar ta a daki shekara talatin babu fita,
Bayan ya fita ta tashi ta dafa abincin ta a gas ita kadai ta gyara gidan ta tayi komai, ta zauna tana jiran lokacin sallah tayi, Zama tayi tunanin rayuwar ta,
Numfashi taja tace’ Allah yagani gareka ni ZULAIHAT ina ganin rayuwa Allah Ka kawo min sauki ya Allah.
????????????????????????
Kwana biyu yana yau be ganta jiya da yau kullum Yana ganin ta Amma yau Sam be ganta ya neme ta kuma a Layin babu ita babu labarinta gashi yanzu ana neman Ayi magriba yayi neman shiru tun ranar Friday rabon Shi daya ganta, ya zaiyi? Besan gidan suba, besan sunanta ba, kawai kamarta yasani a shekaru bazata wuce Ummusalma ba koma bata kaita ba, yarinyar nan kana ganin ta kasan wani Abu na damun ta,kullum bata cikin walwala, gashi besan ta.
Numfashi yaja ya samu wuri ya zauna Yana tunanin yarda zaiyi meyasa ma be tambayeta ba?
Wata zuciyar tace kana shegen tsoron zaka iya? Wama yasani ko matar aure ce,
Zuciyar Shi yaji tayi wani irin bugawa Mai kama da tsoro shine Karo na farko hakan ya faru dashi, yanzu meye mafita?
Tofah ????
????????????????????????
A asibiti kuwa an ansa Abba cikin gaggawa sai dai duk abinda ya kamata suyi,sunyi ba har yanzu be farfado ba, gashi yamma tayi, koda su Yusuf sukazo babu dison damuwa a tare dasu bare su nuna, Sunde hi shiru kawai, sun Kira Binaif sun sanar da Shi, ya fadawa Ummusalma batasan zancen da aka fada masa zaiyi jawo wannan abun ba, hakan yayi Mata kyau fatan ta Allah Kar ya karbi ransa a cikin halinda yake ciki tana so yanemi gafar su, tana masa wannan fatan. Tana kuma so taji dalilin dayasa yaci amanar mahaifin su, shine abinda take so.
✨✨✨✨✨✨✨
Baffa Dan Allah ku barni na nemi Salma Dan Allah Baffa,
Baffa yace’ wacce yarinyar? Ba wacce ta Baki kudi ba? Daman ita kike bamu labari ko? So kike ta bata ki? Kamar yarda aka bata ta? Yarinyar da sam bata da tarbiya?
Tace’ Inni Dan Allah kisa Baki, Inni, Salma na sona,sosai ta dauke ni tamkar yar uwa, da kunnne na naji tace bazata Kara nema na ba, watakila ma ta cireni daga rayuwar ta ina San ta,inaji kamar ‘yar uwa tace ita din, Dan Allah,
Kuka take sosai tana masu magiya,
Tace’ Baffa meyasa to tunda danake Baku labarin ta,da take Bani chocolate Baku taba yimin fada ba? Baffa Ka fada min dalilin raba mu da ita, dalilin yin nesa da ita Dan Allah Baffa, bacin Kaine Ka fada min nazama kawarta Baffa ba wannan bane hujja bashi bane ba,dole akwai dole akwai Baffa Dan Allah Ka fada min yau de, ko naji abinda nake ji ya ragu,
Yace’ Amina, bansan mezan fada maki ba, Amma tabbas anzo min da maganar ki fita daga harkar ta, idan ba haka ba,zamuyi biyun babu,babu ke babu ita,