A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????
A parlour kuwa da suka sauka yan gidan na dining har sun fara cin abinci su Abba da mama sai Sameera(yarinyar dazu) suka karaso kowa fuskar nan a murtuke take wai su a dole fushi sukaja kujera suka zauna suna kowa yaja plate ya fara cin kasancewar an zuba masu.mamace ta kalle su

Tace’ yanzu haka fada kukayi ko??
Ta tambayesu tana kallan daya bayan daya.
Kamar daman jira suke a tare suka dago sukace

To bashi ne ba?
Yusuf ne a ya aikawa Yaseer da harara

yace’ ai mama Shine yace min wai dalla

Nima ai ka fada min,kuma kai ka fara cakumoni ai nagani.

Ya isa haka Abba ya tsawatar masu,shiru sukayi sai hare hare itama mama bata Kara cewa komai ba.

Sameera ce tace’yanzu akan Dan wannan abin shine kukayi fada, kukam bansan sai yaushe zakuyi hankali ba wallahi,
Ba Wanda ya tanka Mata haka suka Gama cin abinsu suka wuce sallah.

Yusuf yau bacci nake ji bazan tsaya kallo pi mask ba,kaji ko,
Ko kallan ba beyi ba yacigaba da kallansa,

Kaji ko,gobe Ka ban labari, na tafi?? Ya fada cike da zakuwa,
Namma shiru

Magana fa nake maka na tafi naje na kwanta zaka ban labarin na yau, kaga nima ina baka ehh na tafi?
A fusace ya juyo

Yace’nifah ka dameni,na hanaka tafiya ne? Tafi mana
Wata dariya yayi yace yesss kayi magana yau daman nace sai kayi magana ai indai munyi fada sai kayi tajin haushi ni banga abin Jin haushin ba tunda de ya wuce ai ko?
Besan sanda yayi dariya ba yace’ naji kasani magana sai me kuma?

Nifa yanzu kwata kwata kallan ma ba dadi daman yaya ce take sawa gidan ma Yana dadi Amma gashi yanzu ta koma wata shiru shiru da ita,

Nima fa kawai kallan nake amma badan dadi ba, da gidan ma nikam yafi min dadi,
Basuyi kallan ba har goma suka tashi suka tafi dakin su don kwanciya.
Mama ta kalli Abba

tace’ me kake gani game da tura Ummusalma karatu kasar waje?
Dakatawa yayi da abinda yake

yace’ sabida me kikayi wannan tunanin? Kina nufin can zamu koma da zama har sai ta kammala karatunta ko kuwa ya kike nufi?

Tace’ba haka nake nufi ba kawai mu turata can don nikam gaskiya na gaji da zama da ita gaskiya wallahi kana gani de ta canja cikin shekara daya da kusan rabi,duk wani Abu da muka daurata akai ta ajje shi gefe,
Numfasawa yayi sannan
yace’ tou daman me mukeso ne dangane da ita komai ai abinda muke cewa tayi Shi takeyi walau mekyau walau marar kyau,to kin gani,

Ummmm Alhaji Kenan a gani na idan har taje can kaga ba ita ba karatu, kaga fa bata San kowa ba kuma ita kadai cezatayi rayuwar ta daga nan sai ta samu gurbataccin kawaye su daurata a hanyar su kaga shikenan mu rabu da ita,zuwa gidama sai taga dama,Amma idan tana nan kawayenta gabadayan su suna San karatu kuma makarantar da suke ita ma cewa zatayi nàn take so kaga daga nan sai sharawa da Shiga tsakanin har su ja ra’ayinta,
Tunda da tafara yake kallanta burinshi be wuce kar tayi karatu mai zurfi ba sannan tazo tace zata zama CEO na company dukka ba company daya bane Amma Shi kam gaskiya bazai iya bata koda guda daya bane balle kuma duka,duk dakanta take cewa ita Business zata karanta kuma ta zama CEO,Amma yanzu Jin wannan Idean na matar sà ya yarda dari bisa dari kuma daman yarinyar bata da wani kokari tunda daman performance dinta tunda ta fara double number take dauka a tayi kokari tazo ta ashirin asu talatin.
Mamace ta katse Shi ganin shirun yayi yawa

Tace’Alhaji ya dai naji shirun yayi yawa ko baka amince bane?
Ajiyar zuciya ya sauke sannan

Yace’wato saratu bansan mezan ce bane ai tunda kika yanke shawarar nan to tayi kawai Allah ya shige mana gaba.Da ameen ta amsa


Washegari kamar yarda ta saba tashi haka tashi,bayan tayi sallah tayi wanka tasa uniform dinta lokacin har 7 yayi sabida akwai ta da nawa komai yanzu a hankali take yinsa sabanin da,
Time table ta duba ta dauko books dinta tasa ajaka,zama tayi ta sa socks dinta sannan ta jawo wayarta ta duba time gani tayi 7:25 yau har ta dan makara dukka ko Akan yarda take fita kullum,fitowa tayi ta shiga dakin baban su ta bude cikin safe ta dauki kudi kusan rabin rapern yan dari biyar tasa a jaka ta fito ta wuce.
Kamar yarda tayi tsammani hakan tagani su duka suna dining suna cin abincin su, dauke Kai tayi ta wuce taje kofa kenan Yusuf ya taso da gudu ya rungumeta ta baya shima yaseer zuwa yayi ya rungumeta,juyowa tayi ya hada su ta rungumesu yaseer

Yace’idan kin dawo zaki min zane na ko??
Da sauri Yusuf ma

yace’nima zaki min ko?
Kamar yarda suka sani nodding Kai kawai ta masu ta sunkuyo tayi pecking nasu tare da breaking hug din ta juya ta fice, suna tsaye suna kallon motar ta sun fita kasancewar bata rufe kofar ba,kallan juna sukayi sannan suka juya suka koma suka ci gaba da cin abincin su,
Hajiya mama tunda suka tashi take fama zabga masu harara ta tsani wannan shakuwar tasu, wani takaici ne yakamata,tayi ta antaya masu harara har suka gama,bama su San tana yiba,su surutun Suma sukeyi. Suka gama kowa ya watse suka fito aka kaisu makaranta,kowa ya kama gabansa.

????????????????????
Ummusalma zaune a class a second seat littafi a gabanta tana karatu Amma a zahiri ba karatun take ba tunani take Neena har yanzu Bata zoba Anya kuwa lafiya?kodai batada lafiya? Ko kuma sunyi tafiya?
Bata ankaraba taji ana gaida teacher wato har ya shigo da sauri ta tashi itama.bayan sun zauna taji yan bayanta suna cewa waifa oral test zaiyi mana
Dayar tace’ haka yace,ehh mana haka yace idan mun Kara haduwa zai mana test kuma oral, taaabbb.
Ita duk ba wannan bane damuwar ta damuwarta Neena bata zoba kuma tasan muddin bakayi test dinba bazaai maka make-up ba yazatayi?
Malamin beyi wani bayani ba ya fara daga farko

Yace’ you Stand up,
ya nuna ta farkon seat din ahankali ta tashi,
Yace’ explain Imagery or figure of speech, don’t waste my time if u don’t know,
In ina tafara tana fada tana in ina alamar be zauna ba ko kuma bata gane ba don dama ba meaning ya masu ba explanation ne kuma daman sai Wanda ya gane,

Is okay, your name yafada
Fada masa tayi ta zauna nan yayiwa ta gaba itama,akazo kan Ummusalma tun kafin ace ta tashi ta tashi ba ta kalle Shiba sabanin Shi daya kalleta,

Yace’ give me 6 Non African poetry and 6 African poetry,
Batare da ta kalleshiba ta fara fada masa tunda ta fara yan class din suka zuba Mata ido musamman new comers don wasu a tunanin su ma bebeyace bata magana Ashe tayi tanayi,shikuma direction din da take kalla ya kalla yaga idan ta a kofa kamar me jiran wani ya shigo,har ta gama sannan

yace’ your name

Amina Muhammad suraj tafada tare da zama ya kalleta yaga ita kaidai ce

yace’ your seatmate name,
Ummusalma Mahmud tafada,
Yan class da gulma nan kowa yafara kuskus da seatmate dinsa haka de Akayi har period din ta fita wani ya shigo ba Neena ba labarinta sai taji duk makarantar ta isheta daman ita kadai ce me debe Mata kewa a class din duk sauran ba kulata suke ba wai kurma wasu kuma suce Mata bebeya bata damu ba,amma Neena haka zata sata agaba tayi tayi kuma bata gajiya duk da bata taba tanka Mata ba,har Akayi break nan wasu daga cikin yan class din suka zo zasu Mata cikat karya akan rashin maganar ta tunda suka fara ko kallo Basu ishetaba balle ta daga ta kallesu gani take idan ta takelle Suma ai sun Sami wani matsayi ne babba makuwa,haka suka Gama suka tafi,yunwa take ji dole ta tashi ta fito taje cafeteria ta siya abin da zata siya ta dawo ta zauna tana ci a class,a takure de tajita duk ba Neena,har aka tashi tanan zaune kowa ya fice sai ita,tashi tayi taje tayi alwala tazo tayi sallah ta fito lokacin har an watse tana cikin tafiyar ta mekama data hawainiya ta hango wata tana watering flowers,
Kamar Neena ta fada a zuciyarta
cigaba tayi ta tafiya taga de itadince,Kenan tazo takuma fada,
Neenan ce ta hangota ta gudu ta zo wurinta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button