A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
tace’ ina kikaje?
Sai da ta zauna
tace’ naje gidan uncle ne,shiyasa kuma wannan matar tashi tasani aiki wai sunyi Baki, takarashe tana ya tsine fuska, kallanta kawai Ummusalma keyi batayi magana ba, abinci ta kawo masu suna ci sahr na Mata Santi,duk sanda sahr tayi santin abincinta babu Wanda take tunawa kuma sai yusseer Allah sarki ko ya suke?
Haka rayuwa tayi ta tafiya cikin kwanciyar hankali ta jima da siyan simcard Amma bata ma sa numbern su mama ba bare ta kirasu,in fact bata da numbern ba kowa sai ta sahr ita kadai gareta.
Sahr kuwa a bangarenta tana mamakin umsalma tunda tazo bata nemi gida ba,abin na bata mamaki sosai,sai kuma abinda ta lura dashi duk dare tana karanta wata paper kafin tayi bacci haka idan tayi bacci ta tashi sai ta karanta ta,ko karatu zatayi tana karanta papern,ita kanta ta karanta papern ya kai sau ba adadi ita bataga amfanin karantawa ba,tunda indai haddacewa ne to ta tabbata ta haddace ta. Kuma tasan dole wata Rana zata bata labarin ta kamar yarda itama ta bata labarin ta ahaka.
????????????????????
~Nigeria~
Tunda suka dawo daga raka Ummusalma su yusseer suke kuka,sunki suci abinci,sunki cin komai, suna ma dakin ta Akan gadanta sun rungume juna sun tukuikuye wuri daya suna razgar kuka,mama tayi fadan tayi fadan ta gaji,Basu taba rabuwa da ita koda na kwana daya bane, da can ma dakin ta suke kwana daga baya ne da tayi rashin lafiya suka dena kwana,har dare suna dakin ko sallah basuyi ba bare su tashi suci abinci ,haka har bacci ya dauke su,idan sun farka suyi kukan su suyi bacci,ga yunwa na cinsu Amma inaaa baza su iya ci ba.
Bayan anyi Isha Mama ta fadawa Abba abinda ke faruwa,idan ransa yayi dubu to yabaci sosai ya fusata ya dau charger ya fita da ita sai dakin Ummusalma Yana zuwa lokacin bacci ya dauke su gashi daman sun galabaita,baiyi wata wata ba ya zula musu,wata rin zabura sukayi suka Kara rungeme juna maimakon su gudu inaaa sai suka Kara tukuikuyewa wuri guda takaici ya Kara kama Abba baisan sanda yayi ya tafakar suba suna ihu suna kuka,Mama na gefe don itakam daman abin nasu ya isheta,ahaka yayi ya gaji ya fita,mama ma ta bishi, dakyar Yusuf daman shine mai Dan wayo ya tashi ya tashi ya zauna ya janyo yaseer Yana rarrashinsa lemo ya tashi ya dauko masu da cake da Chocolate,yanaci yana bashi ahaka suka ci dayawa idan suncinye sai ya Kara masu har suka koshi,tashi yayi ya daura kan yaseer a cinyarsa
yace’ Yaya bazata taba dawowa ba,
Kallansa yaseer yayi
yace’ a,ah zata dawo dazu ta fada min cewar kar na fadawa kowa zata dawo ai,
A,ah bazata dawo ba ta fada maka zata dawo ne Amma ba dawowa zatayi ba,
Cike da tausayi yake maganar kana ji kasan Yana cikin kunci ne,
Taya kasan bazata dawo ba ita ta fada maka ne???
Ba ita bace mama naji tanan fada.
Yaushe?? Ya tambaya cike da zakuwa
Dazu ta shigo kana bacci lokacin ta shigo tace’ indai Ummusalma ce bazata taba dawowa garemu ba har abada kuma sai mun manta da ita a kwakwalwar mu,
Ya karashe da kwalla na zuba daga idonsa, yaseer ma kukan yake,
yace’ shikenan yanzu bazata dawo ba?? Kana ganin zamu manta da ita ne?
Zamu manta da ita idan ta mana wani abun.
Mezata mana to?
Kallanshi yayi yace’ ina abokin mu da ya manta da mamanshi? Ka tuna Shi?
Daga masa Kai yayi yaci gaba yace’ to da ya fada min abinda yasa ya manta da shima lokacin da ta tafi ta barshi kuka yayi tayi shine antyn Shi(matar babanshi) taba Shi wani abu yasha tace inji mamanshi tace a bashi yace tunda yasha shikenan be Kara tunawa da ita ba sai da ya gan maman tasa. To itama mama Shi zata bamu bazamu Kara tunawa da yaya ba,
Kuka yaseer yasa don ya tuna wahalar da abokin su yasha kafin yaga mamanshi kulluma idan suka biya islamiyya zasuga Yana aiki idan suka tambayeshi ina mamanshi sai yace’ Shi baida mama.kuka sosai suka Kara sakawa daga karshe, Yusuf
yace’ idan mama ta bamu Abu kar mu karba kuma kar musha,idan ta bamu muce munsha,kuma mudena Zan can Yaya a gabansu ko???
Daga masa Kai yaseer yayi ya rungume Shi,shima rungume Shi yayi
yace’ kanina yau bamuyi sallah ba,
Dago yayi ya kalle Shi kawai sai yayi dariya
yace’ Yayanah ehh haka nefah
Dariya suka tuntsire da ita, yaseer
yace’ taabbb wai Kaine yaya taaab ko a mafarki bazance ma ba,
Yusuf shima dariyan yake yace’ Ka tuna sanda Yaya tace kana cemun yaya ??
Ai naga baka girmen ba da zance maka wani yaya,tsayinmu daya dai,
Amma ai na girmeka a shekaru ko ?
Laaaaaa shekara dayan? Dayace fa kuma Zan biya Ka kadena cewa Ka girmen,daga haka suka tashi sukayi sallah tun Azahar har la’asar kayansu suka je suka cire sannan suka dawo suka kwanta sunayi auna hiran yayar su,
Washegari kamar ba abinda ya damesu suka tashi sukayi wanka,wai su yanzu andena masu wanka,suka sa Kaya iri daya abinsu sunyi kyau kallo suka kunna yaseer yaje ya karbo masu abinci sukaci suka koshi,suka fita wasa,koda mama tace masu abinci fa, sukace sun koshi,
Washegari Monday ma zuwa sukayi suka ci abincin su sukace sun wuce,
Haka rayuwar su tacigaba da tafiya ko mama ta tambayesu yaya cewa suke babu wata yaya agidan idan ba sameera ba a tunaninta abinta yaci saidai kuma ba haka bane Sam don Basu manta da yayar suba…….
By: Hijjart
Abdoul
Cwthrt????
???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
7
A bangaren Abba kuwa,yaji takaicin bada motar da tayi,Amma ba yarda zaiyi tunda ta Riga da ta bayar.
Yana dakinsa Yana zirga zirga yaje ya dawo ya yaje ya komo,ahaka mama ta shigo ta sameshi,tsabar tunaninsa ma yayi nisa baisan da zuwanta ba,sai da ta zauna
tace’ Alhaji lafiya kuwa?? Naga kana ta yawo a tsakar daki meke faruwa?
Kallanta ya yayi ya dawo kusa da ita ya zauna ya ja doguwar a jiyar zuciya
yace’ Bakomai ke damuna face rashin sanin menene acikin safe din dakin can,bansan ya zanyi ba,
Numfasawa tayi
tace’ Alhaji mezai hana mu chanza pin din,
Ba pin bane, password ne kuma ma password ba iya adadin letters din bane kullum sai na gwada Amma ina,kuma dole sai an bude za’a iya canzawa,yanzu ya zamuyi?
Yaci gaba,
Haka zamuyi ta kallanta muna adana Amma munkasa budewa? Bama wannan ba na tabbata duk wani takardu masu amfani Yana cikin su.
Shiru tayi don itama bata da mafita Akan haka,su bawani iya Abu sukayi ba,kuma ba Wanda zasu yarda dashi su fada masa damuwarsu. Lallaba Shi tayi Akan kar ya kadamu sunsan zasu bude duk Daren dadadewa kuwa. Daga haka suka dauko maganar Ummusalma, mama
tace’ Nifa Alhaji yarinyar ince de baka bata wani kudi da yawa ba?
Kallanta yayi irin bangane ba, tace ehh ina nufin baka bata kudi da yawa ba kasan de dole zata bukaci kudi ai,
Yace’ koma nawa na bata ina ruwanki a ciki, tunda de ko ta neme mu sauya layi zamuyi,bare kuma tunda taje bata neme mu ba,tunda kikaga haka watakil ma an sace ta.
Allah yasa ma ni an sace ta din,don kwata kwata banasan Kara ganinta.
Ameen yace kawai ya jawo system ya fara aiki ita kuma ta fita.
????????????????????
~_London_~
Ummusalma har tayi wata hudu da tafiya, a bangarenta kuwa bata wani tunawa da wasu Marika don marikanta zata kirasu ba iyaye ba, bazata kirasu da iyayenta ba, bata tunawa da su sai akai akai,karatun gaban tama ya ishe ta. Tana yawan tuna su yusseer,musamman idan ta tuna rayuwar ta tada.
Kamar kullum Karatu suke ita da sahr,sun kusa fara exams sosai suke karatun su,Bama kamar ita da bata so su kwace course dayan don Duka tana San abinta,sungama karatun suna Dan hira sama sama sahr ta kalli umsalma don yanzu kusan kowa a department din su yasan umsalma Indai kana tare da sahr to sai Ka santa,ta kalleta ganin wannan papern da take karantawa