A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????

Mama da Abba na zaune a daki kowa cikin damuwa yake,ta kalle Shi,

tace’ wai Alhaji baza ba mu fadawa jama’a rasuwar ‘ya’yan mu yau kwana daya fa,jibi kuma kwana uku dole ai za’ayi masu sadaka de,

Abba yace’ aga Nina kawai muyi musu sadaka bakin mu Alaikum idan anyi bakwai ma muyi musu har ayi arba’in,

Cikin mamaki tace’ Alhaji wannan wanne irin batune haka? Ka kwasan mekake cewa? Anya ba kasan me kakeyi kuwa?

Yace’ ehh sanin nasan abinda nakeyi ne yasa nace kar a gayyato mutane,

‘ to amma meyasa?

‘ saboda idan mutane suka san cewan ‘ya’yan mu sun rasu,za’a tambayi dalili ko mun boyewa na waje bazamu boyewa na ciki ba, kuma na cikinne zasu sanar wa ‘yan waje,shima Wanda aka sanar wa ba shiru zaiyi ba idan yayi gaba zai sanar,daga karshe kuma kiga an fara posting a social media,kuma dole labarin zai tashi daga ainahin labarinsa ya koma wani kalar labarin shiyasa nace muyi shiru bakin mu Alaikum,

Sosai ta gamsu kuma ta yarda da wannan shawara tasa,

tace’ mu kuma haka Allah ya kaddara mana rashin ‘ya’ya har biyu a lokaci guda.
Kallanta yayi kawai baice komai ba don yasan har yanzu batayi hankali ba,idan ma ya fada Mata cewa zatayi Wanda ya sace sune,shikuwa tun ranar da aka neme su aka rasa sai an turo masa da text har yau da yake kwana uku da dauke su,kuma Kala Kala wani ya gane me ya kusa wani kuma sai an mai bayani, Yana tunanin l bema San ta tafi ba. Kwanciya kawai yayi ya rufe ido,Yana tuba abinda ya aikata a shekarun baya.

Koda Mama ta sauko sai taga ummu a zaune a parlour gaidata ummu tayi, mama tace’ Ummu sai dai hakuri haka Allah ya kaddara mana fatan Allah ya bamu ikon cinyeta,
Daga Mata kawai ummu tayi tace’ Bari na Shiga dakin su zan dauki handout din a,
Daga Mata Kai kawai mama tayi,
Tashi tayi ta Shiga dakin datasan san anan suke ajjewa kayansu kuma ana suke karatu, table din karatu uku ne a dakin sai gado a tsakiya don wardrobe din dakin itace ta zuba littafi da tarkacen su, wurin table dinta ta duba taga babu ta duba ko nasu ma shima taga babu, wardrobe ta duba anan ta handout dinsu tasu ta kwasu ta ta ajjeta akasa tana dubawa, sai data zare ta ta ajje ta Kara da Wanda zata dauka, a Sama ta dauko kawai sai ta ajje a kasa,har zata rufe sai kuma tayi tunanin ta mayar inda ta dauka, taje daukowa ta hado da wani littafi sai da mayar ta zare littafin zata Maya dashi taga kamar diary “‘ Kona waye ? Ta furta sai kuma tace’ to ko su suke rubutawa? Dauka tayi ta hada da abinda ta dauka ta rufe wardrobe din ta fito, sallama tayiwa mama ta wuce gida,

 Tana shiga taga uncle Yana cin abinci wucewa tayi ta Shiga daki, sai da tayi sallah tukunna tazo ta kwanta, diary din ta dauko, 

tace’ yanzah haka yaseer ne uban hauka zai wani kafa rubuta diary kome zaice oho masa,
Page farko ta bude taga wani zane kamar jariri iri an wulgar a cikin towel, sai kuma daga kasan zanen wasu yara ne su biyu kamar su daya da uniform a jikinsu, daka kasa aka kuma zane wata yarinya ‘yar karama tayi tagumi, sai kuma can kasa aka zana gida ya kama da wuta, kuma kowanne Zane da rubutu a jiki amma ita bata wani gane komai ba tunda rubutun a wani style akayi Shi Wanda ya rubuta ne kawai yasan me ya rubuta a jiki, Kara bude page na biyu tayi shima zane ne bata tsaya kallon me aka zana ba ta bude wani shafin, ganin mai sunan a jikin yasata waro Ido Ummusalma Muhammad?
Ai tuni ta Kara bude wani page anan taga rubutu da yawa,daga nan tafara karantawa,daga farko labarin very interesting amma da taje tsakiyar Shi da karshe tuni ta fara kuka,har kawo sanda ta zata tafi London,kifa littafin tayi,tayi rufda ciki ta cigaba da rera kukanta,
Uncle da tazo Kiranta don taci abinci kuma ya fada Mata su Umma sunzo, ganin tana kuka yasa Shi zuwa ya daga ta Shi a tunanin sa kukan besties takeyi,ya Dura kanta cinyarsa ya fara rarrashinta besan dalilin dayasa bayasan kukan ‘yarshi ba,ko Shi yasa kuka to ana jimawa zai rarrasheta sai dai kuma ita Allah yayi da tsokana shikuma bayaso ga Dan Karen surutu, ganin taki tayi shiru yasa shima ya dakata Yana nazarin kukan nata, littafin da yagani shima yasashi dauka, page din karshe ne inda zata tafi London daga nan ba’a cigaba ba, farko ya karanta kadan sai kuma karshe karshe karshe da ya Karanta, dukda be Karanta complete amma ya fahimta abinda zai fahimta,bema iya magana ba ya sauke kanta a pillow ya tashi ya fice,

Wata irin tsanar Mama da Abba yakeji lokaci tsanar da besan ta Shiga zuciyar sa ba lokaci guda,Yana daf da Shiga parlour yaji Anty na,

cewa’ har yanzu ba’a Sami labarin yarinyar ba, ina tsoron a fada masa wani ciwon ya same Shi,don Allah Baba kumu Bari sai mun tabbatar hoto kawai nagani,
Baba yace’ wato zainab Bana ki ta taki bane inasan na kawo karshen wannan abun ne ina son na Gama da Iyaye na lafiya kulluma Baba da Inna da ciwo suke kwana suke tashi, banje ba Amma kulluma ana bani labari,

Umma tace’ ya kamata ace a wannan shekarar munje Bana iya bacci sai nayi mafarkin su,kuma kinga Adda itama an nemeta an rasa kosama ko kasa an bincika ko ina babu ita har sun fitar ma da ran Kara ganinta a duniya sun hakura sannan kuma muda muke ran suka San inda muke sun haramta mana zuwa inda suke wannan Karon kome zai faru sai dai faru,iyaye ba abin wasa bane,

Anty tace’ naji zakuje kuma Nima zanje Amma don Allah ku taimaka kar ku fada masa har sai idan munje don Allah ku min wannan alfarmar Baba Umma please,
Numfashi taja yace’ shikenan zainab bakomai, Fatana Allah yasa kar su koremu kamar koda yaushe idan munje,
Babu Wanda ya amsa sabida zuciyar kowa da irin tunanin da suke,

Uncle dake corridorn da zai sada Shi da parlour Yana tsaye Yana jinsu,kowaye suke zancen sa kuma oho,fitowa yayi yaje wurin Baba ya zauna kusa dashi ya kalleshi kawai sai ya rungume shi,Yana sauke ajiyar zuciya, idan da sabo ya Saba da irin wannan abun nasa,anacewa Da yafi saboda Uwarsa to shide yafi saboda dansa,
Yace’ Babana mai sunan ,jika na, ya akayi ne?
Uncle da Baya iya boye damuwar Shi ,

yace’ Dad wani abun al’ajabi na karanta,
Tashi yayi zaune yace’ Anty ina wannan yarinyar nan? Bejira cewar taba ya Dura yace’ labarin ta na Karan ta,a wurin Ummu gashi can ma tana kuka, daga nan ya Basu iya abinda yasani,
Babu Wanda ya iya magana don kowa yaji labarin ta dole a tausaya mata,kuma ma mace fa da tausayi.

????????????????????????

Suna zaune suna buga game,an kawo masu komai duk wani da suke so ana yi musu matsalar kawai wayace babu,kuma ko akwai ma bazasu Kiraba suna San rayuwar su,suna so kafin su mutu su Hadi da Yaya.

Yusuf yace’ kasan lokacin da muke game da Yaya?

Yaseer yace’ lalle ma nasani mana, wayace ma,wai meka mayar ni ne?

Yusuf yace’ ahh yaro mana mekuwa na mayarka,

Yaseer banza yamasa idan Yana game Baya iya magana yanzu sai a cinye Shi gashi daman mutul combat ne aikuwa de ba Ankara ba yaga yusuf yamasa penalty .
Haushi ne yakama Shi yace’ na fasa idan ba tsoro ba a koma ball kasan sai na maka 10-0,

Nikuma gani Wawa sai na tsaya kamin,akoma mana aga Wanda zai cinye,

Ball suka koma suna bugawa babu Wanda ya cinye har lokacin sallah yayi suka dawo suka cigaba abinsu.

✨✨✨✨✨✨

Umma na zaune a parlour taga sun fito,

yace’ Umma zamu fita,

Kallansu ta da kyau tace’ idan Banda de yaran zamani ina kaga an fita daga daura aure ? Jiya fa aka daura auren ko kun manta ne?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page