A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ummu kuwa suna zuwa ta nemi wuri ta zauna tana tunani, uncle ne ya zauna a kusa da ita ta daura kanta a kafadar sa ya rungume ta, idan ta taf kwalla.
tace, “Nima haka Zan sha wahala? Daman haihuwar da wuya?”
Sai hawaye ya zubo,
yace, “nata ne ya zo da haka kinji ko? Naki ai bazai zo da wuya ba ina tare da dake kuma ma ai tare zamu Shiga tare zamu haihu tunda daman tare muka yi…”
Be iya kara Sawa ba ganin yarda Binaif ya wani tashi bukut ya ban kada dakin ya shiga kafin ma ya tashi har ya shige shikuwa Binaif jin abinda Uncle yace tare zasu Shiga shine yasa Shi ya tashi ya shige.
Yana Shiga ya ganta ta hada zuba sharkaf amma babu ko digon hawaye sunayen Allah kawai take ambata gashi tazo six cm amma shiru bata haihu ba kawai ganin sa sukayi akan su ya shigo ko sauraran su ma beyi ba ya wuce ya wurin ta ya rike hannun ta gam Yana kallan fuskar ta dat tayi ja jijiyoyin kan nan sun tashi rada rada kana gani zaka sa tana cikin hali na wahala sai anan wata addu’a ta fado masa ya fara karanta mata tana maimaita wa be taba sanin haihuwa akwai wahala ba sai Daya zo kansu Ashe haka mutane suke ji be sani ba ya tausaya mata sosai. Wani ciwo taji Wanda yafi nada ya taso gadan gadan ya zo mata kokarin mike wa take zata tashi anata tunanin, taji nurses da doctor din suna cewa”Push” taji de suna magana Amma bata San me suke cewa ba kawai ita kokari take ta tashi ko zata ji dadin abin take ji Binaif kuma sai maida ta yake Jin abinda suke cewa yasa shi Kara kwantar da ita cikin sanyin muryan da ita kawai zata ji.
yace, “Ummusalma you have to push idan kayi shikenan fa zaki ba komai oya one,two,three push”.
Kara damke hannun sa tayi sannan tayi yarda ya umarce ta namma de shiru sai datayi wurin saura hudu ana biyar din ne Allah ya taimake ta ta haihu wani irin relief taji sanda taji ta sakayau tare da kukan yaran ko yarinyar. Binaif wata ajiyar zuciya ya sauke Kai kace shine ya haihun zama yayi ya Daura Kan ta a cinayar sa yana kallan ta Sai anan ta bude idan ta ganin sa da tayi kamar shine yayi haihuwar fuskar sa ta hade da gumi Sharkaf haka ma rigar jikin sa Kana ma ganin singlet din dake jikin sa tsabar yarda yayi horrible bata san sanda dariya ya so ya kubce mata ba tade maze tana cikin hawuya tayi murmushi, shima murmushin ya mayar mata yana shafa kanta suna kaiwa da juna murmushi har aka Shirya abinda suka Haifa basu sani ba Ashe ana ta masu magana ina kayan yake sai waje suka fita suka anso.
Nurse din ce ta katse ce tace, “kun samu baby girl fa”.
Dayake da Dan karfi tayi magana yasa suka ji ta sakin hannun ta yayi ya ansa yarinyar yana kallan ta, ita kuma tana kallan sa kallan ta yayi.
yace, “Bamu yi tunanin sunan da zamu sa ba wanne suna zamu saka?”
A hankali tace, “zulaihat”.
Nurse tace, “ya kamata Ka barsu haka su huta a shirya ta itama”.
“To shikenan idan kin huta kya Fadi sunan banji abinda kika ce ba Bari naje”.
Daga Masa Kai tayi sannan aka tura wani dakin acikin Labour room din, shikuma ya fita da yarinyar a hannun sa Yana kallan ta Yana fita Mas’ud yayi Kan sa sai Suma suka tashi.
Yace, “bb ya take? Ta haihu lafiya? Ba abinda ya same ta? bb please kayi magana mana sai wani kallan yaro kake ina tambayar ka”.
Dagowa yayi da murmushi a fuskar sa.
Yace, “Chatty all is well she’s fine”.
A tare suka sauke ajiyar zuciya sai kuma aka fara ‘yar rige rigen daukan yarinyar, Baya yayi Yana kallan su.
Yace, “Yusseer yaushe kuka zo kuma?”
Yaseer yace, “ai Baka San sanda mukazo ba? Lalle ma bb gaskiya Ka Shiga duhu”.
“To naji yanzu wa kuke so a bawa? Uncle? Chatty? Mus’ab? Yusuf? Yaseer? Ko ummu?”
Kallan yarinyar yake Yana magana sukuma suka tsayawa sororo suna kallan sa can ya dago yace, “yawwa tace a bawa Ummu”.
Ya fada yana takawa wurin ta ya mika mata karba tayi a Hankali tana kallan yarinyar ta kalli Mas’ud ta kalli yarinyar ta kuma kallan Mas’ud ta kuma kallan yarinyar ta kalli Binaif.
tace, “bata maka kama da chatty?”
Kafin Binaif yayi magana Mas’ud yayi wut yazo wurin su yace, “Allah ma ya sauwake ‘yar aljana tayi kama dani to ‘ya ta ce? Da zata yi kama dani ko Babar ta Bama kama bare kuma ‘yar ta?”
Fito da ita akayi hakan sa yasa su Duka suka tafi suka bi bayan ta har dakin da aka Kai ta tana kwance tana bacci an gyara da’alama kuma alluran bacci aka Mata Dan ta huta, samun wurin sukayi suka zauna sannan Ummu take bin su Daya bayan Daya tana baso batafin Minti Daya a hannun Ka zata Karba Binaif na tsaye a bakin kofa Yana kallan su sai da taje wurin uncle ta zauna a kusa dashi.
Tace, “bazan baka ‘yar mutane ba ka yarda ita ba ka leka ka ganta”.
Yace, “to ai Naga itama ‘ya tace”.
Mas’ud yace, “cabb baza Ka dau kaba gaskiya yaya haka kawai kawai Ka leka ta Ka ganta yawwa hakan yafi ko kuma kawai Ka dauka tunda ba ‘ya ta bace nifa na kusa haihuwa hahahaha har na hasko ni da ‘ya babu Wanda zai dauka a to Gwara ma aji tun yanzu ba dauka zakuyi ba”.
Mus’ab yace, “wai fav meye haka? Kai sam baka Jin kunya ko? Yaushe akayi auren har da Zaka fara zancen haihuwa? Akace maka a ruwa zaya sha kawai ta haihu ? Allah Ka dena taam”.
Yusuf yace, “ni yanzu a Bani yarinyar ma anbi an rike ko second bata yi ba”.
“Ba kuwa Baku zanyi ba ehe”.
Uncle yace, “nidai abani na koya rike ta kafin nawa yazo”.
Binaif ta kalla tace, “bb na Bashi?”
Murmushi bb yayi ya taho ya zauna a kan gadan yace, “ki bashi Shi ya kamata ma ya fara rike wa ba kowa ba”.
Dakyar ta bashi ya rike shima sai da ya sha gyara wai be iya ba, Yana rikewa kuma ta ansa ta rike ta.
Binaif yace, “wai yarinyar Bata kuka ne? Bata ci komai bafa”.
Mas’ud yace, “taab shaukin love ya dauke Ka taya zaka San me aka bata kaidai kawai kayi shiru”.
Girgiza Kai kawai yayi Yana kallan ta yarda take baccin ta hankali kwance,
Yace, “ba Wanda ya sani fa ya kamata a kira a fada”.
Uncle yace, “wanne fada kuma? Salan kawai mutane suzo su cika ta da surutu kuna ana so ta huta? Ya kamata fa mu koma gida ma abar Ka daga Kai sai ita tana tashi nasan za’a duba idan ba matsala a sallame mu”.
Mas’ud yace, “ni daman Bana San Zama ma kawai muyi ta zama muna jiran gawa waya sani ma ko…”
Binaif ne ya wurgo masa takalmin sa yace, “Ku tashi Ku tafi daman ba gayya muke oya Ku tashi”.
Tura Baki yayi ya tashi ya fara tafiya har yaje kofa ya juyo yace, “Kai wai Ku tsaya da wacce ma aka kawo ta ne?”
Mus’ab dariya yasa yace da motar da ba’a hawa wai ta Amarya ce sai gashi an dauki aljana a cikin ta”.
Dariya suka sa su Dukan su yaseer harda rike ciki Dan dariya babu abinda ya tuna sai sanda suka ce ya Basu aro suje makaranta it’s urgent yaki suka kada suka raya daga karshe sai Mus’ab ne ya basu tashi lokacin dawowar sa kenan kuma harda ummu zasu tafi a lokacin amma yaki sai ca yace motar Amarya ce Amarya ce zata fara hawa sai gashi aljana ce ta fara hawa.
Daure fuska yayi Yana kallan su ya kalli ummu yace, “ke fada wa mijin ki da besties dinki su fita harka ta Bani basu kinji ai”.
Ya kalli Binaif dake murmushi Yana kallan ta, yace, “bb Ka nemi motar da Zaka dawo da aljanar matar Ka ni nayi nan”.
Uncle yace, “relax da wanne key din zaka tafi? Sanda Ka kawo ta da Ka Ciro key din ma? Allah yasa ma ba’a dauke motar ba dan Naga yau kamar weekend security basa zama sosai”.