A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ Nifa dan ki tsorata yasa nasaka maki kadangaren nan,

Lokacin guda abinda ya faru ya dawo Mata batasan lokacin da ta fashe da dariya ba, ashe shi yasa mata kadangaren kuma shi yake Jin tsoro, rigar dake hannunsa ya daura Mata a kanta, zaiyi magana yaga ta tashi ta tafi tana cigaba da dariya, murmushi kawai yayi shima ya tashi ya tafi.

      ♡♡♡♡♡♡♡♡♡

 Juyi kawai take,takasa bacci tarasa abinda yake damunta tasan de yanzu duk yanda akayi yana cikin damuwa, samun kanta tayi da tunanin halinda yake ciki,ko yayi bacci,taya ma zaiyi bacci bayan halinda yake ciki, ko tunanin me yake? Oh God, tashi tayi ta zauna,takwanta,ta kuma tashi,daga karshe dai kwantawa tayi ta janyo wayarta,wurin apps kawai ta Shiga badan tasan abun da zatayi ba,sai dan ta kasa bacci,kuma takasa nata tunanin sai wanda bai san tanayi ba, WhatsApp tagani ita har ga Allah tama manta da ta sauke Shi akan wayarta, data ta bude ta Shiga,ta Shiga contact ganin yusseer batasan numbern yusuf ba bare ta yaseer, dubawa tayi kuwa taga Dukan su online, 

“Hi” tace masu su duka,

” Hlo” suka amsa a kusan tare,

“Ya kake”

“Lfy”
“Waye”

“Please wake magana?”

Tasan Yusuf ne yace waye, yaseer kuma yace please wake magana, murmushin tayi tayi reply da,

“Macece”

“Wace”?

“Okk please wace”

“Please dawa nake magana Yusuf ko yaseer”?

“Ohhh daman baki san dawa kake magana ba Kenan”?

“Ai nazaci kin San dawa kike magana”
Murmushi takuma yi,

“tayi reply ai Bansan dawa nake magana ba”
Nade San ina magana ne da daya daga cikin ku,
Ta lura yusuf ke fara reply saboda amsar da yake bata,

” Sai ki Bari ki tantance dawa kike magana”
” A,a sai dai Ka fada min wane Yusuf ne ko yaseer?”

” Please don Allah wace?”
” Ga dukkan alamu da Yaseer nake magana ko?”

” Kin renawa kanki hankali waye zai fada maki dawa kike magana,go to hell”
” Ohhh sorry yusuf ana aasfi ya Yusuf”

” Ehh nine,amma to ya Akayi da kike tambaya?
” Dan na tantance daya daga cikin ku yanzu kuma na tantance”

” Da kinsani kike tambaya ?
” Yanzu nasani de”

“Kamar ya?”
“Eh Duka sunan daya nasaka”

“Ohhh tunda kin sani tou sai anjima”
“Baka san kasan dawa kake magana”?

“Ban fahimce ki ba, kina so tantance,idan na ganeki kinsan halinmu Kenan? Please ke wece?”

“Bansan nasan dawa nake magana ban bukatar hakan.
” Haba yusseer”

Ai batayi aune ba kawai taji Kira ya shigo wayarta, bakuwan number ce don haka ta daga, batayi magana ba sai dai jin muryan masu kirannata yasata lumeshe ido, yusseer ne,

“Yaya don Allah kiyi magana dagaske kece?

“Yaya kina ina Don Allah yanzu zamu zo ganinki please yaya,
Muryanta kasa kasa,

tace’ yusseer yanzu dare yayi ku bari sai zuwa gobe don Allah please yusseer,

Yusuf yace’ yaya kece kike magana haka? Yaya kindena yin shirun? Yaya talk mana,
Jin muryan sa na rawa alamar zaiyi kuka yasa ta yin shiru, cigaba da magana sukayi idan wannan ya yayi sai wannan yayi, dakyar ta fada masu inda take, idan sunzo su kirata.

????????????????????

Ko kaya basu sauya ba tsabar murna da zumudi,basu lura da cewan goma ta gota ba,yusuf ya zuri key din mota suka fito, wayar yusuf kawai suka tafi da ita saboda Kiran Yaya,wani irin farin ciki suke ciki koba komai zasu ganta kuma zasuji dadi, koda suka fito bakowa a parlourn sai Sameera da shigowar ta kenan,bama su lura da ita ba,suna rigayen fita, mai gadi ma bacci yake yaseer ne ya bude get din. Suka fita abinsu,gudu kawai suke shararawa kasancewar dare ne motocin sunyi karanci sai dai dai ku da ba’a Rasa ba, sun kusa zuwa dab da unguwar wata mota tazo tasha gaban su saura Kiris su bugi motar, Allah yasa yayi saurin taka burki, Basu Ankaraba suka ga anzo an bude motar tasu an fito da su,an shaka masu wani Abu,tun suna magana suna tambayar suwaye har suka dena magana.

Basu tashi tashi ba sai shida da rabi na safe yaseer ne yafara bude ido, ganinsa a saban wuri yasa Shi bude ido da kyau, daki ne dan madaidai ci,da gado shima gadan bawani babba bane ba sai kuma mirrorn da bakomai akai, dakinde yayi kyau daidai misali Amma idan aka hada da nasu to ko rabin kwatar nasu beyi ba,ga Shi komai na cikin sa sabo ne,kamar de dakin amarya, dakyar ya tashi ya jingina da gadan da yake Kai, ya kuma lumshe ido ya bude a hankali kuma ya fara tuno abinda ya faru har zuwa lokacin da aka Shaka masu abu, yusuf ya kalla yaga yarda yake motsi, alamar Yana son ya tashi, yajima Yana motsi daga bisani ya tashi zaune ganin ba dakinsu ba yasashi kallan yaseer kamar yarda shima yaseer din kallansa yake,daganan kuma ya karewa dakin kallan tsab, har ya tuno abinda ya faru dasu, kofar da yagani yasa Shi ya nufa, toilet ne sai dai dan karami ne toilet din compare to nasu, babu bathtub sai rariya kawai, sai toilet sit, saidai dukda kasancewar sa karami toilet din ya masa kyau Jin wani kamshi Yana tashi, Ahaka yayi abinda zaiyi ya fito, shima yaseer Saida yagama karewa komai kallo Sannan ya fito, carpet din dakin akai sukayi sallah,

Yaseer yace’ ko me muka musu da zasu sato mu? Ko yanka mu za’ayi ne?

Wani irin kallan baka da hankali yusuf ya masa yace’ da yanka mu za’ayi akace maka za’a barmu muyi sallah ne? Ko akace maka zamuyi magana?
Kawai Sato mu akayi,kamar yarda ake satar mutane,

Yaseer yace’ ina wayar ka? Mu Kira Abba yazo da police a fitar da mu,

Sai a sannan ya tuna yana da waya, aljihunsa ya duba amma babu daman three quarter ne a jikinsu da shirt,to a aljihun yasaka kuma babu,alama Kenan sun dauke ta, yusuf

yace’ yanzu ya zamuyi?
Nima bansani ba, yaseer ya fada,

Zama sukayi sukayi su kayi shiru kowa da abinda yake sakawa,su mamaki ma suke wai su aka sato sai kace wasu kananan yara, abin mamaki, suna nan har karfe 10 basu motsa ba, Rasa ma abin yi sukayi gashi windown ba irin casu bane wannan harda wani karfe ajikin sa, dakin kuma ba komai bare su samu su banbare karfen su gudu,to Idan ma sun fita daga dakin sun san yanda wajan yake ne?

Knocking din da akayi yasa su tashi a zabure suna kallan kofa, wani ne yazo hannunsa rike da kaya niki-niki, ya ajje Yana kallansu,Zama yayi a bakin gadan sannan,

yace’ da kunyi hakuri kun zauna,ba abinda zamu muku kawai de abinda muke so daku shine hadin kai zaku bamu, idan mun samu abinda muke so zaku tafi cikin sauki, idan kuma kukayi mana gardama kuma kuke kokarin guduwa to kusan cewa daukar rai bakomai bane a wurin mu, kashe mutum har lahira bamu dauke Shi komai ba, kuma ba mutuwar sauki muke ba,Idan mun muku mutuwar sauki ai kunji dadi bamu muku azabar Wanda yake kokarin guduwa ba, abinda nake nufi shine,idan zamu kashe mutum to yau zamu yanka masa kafa an jima mu yanki fatar sa anjima mu yanka Shi,tsantsar azaba ce zata sa mutum mutuwa, kuma bamu da imani,
Ya karashe Yana zaro wata zarbebiyar wuka sai kyalli take don sun gano fuskar su ta jikin wukar, tunda ya fara kuma suke zare ido tashin hankalin su basu San wanne irin hadin Kai yake nufi ba, ga kuma zancen mutuwa da suka ji ana ambata, da irin azaba idan sukeyi laifi su kashe mutum, Basu Kara Shiga tashin hankali ba sai da ya zaro wannan wukar,da kana gani kasan yanka daya ne naman ka ya fita, Basu ankaraba suka ji yana,

cewa'” idan baku yarda ba da hadin Kan da zaku bayar yanzu nan zan kashe ku,kisa mafi sauki a wuri na,
Yafada yana tashi tare da matsowa inda suke,ai kuwa suma suka fara matsawa yana matsowa suna matsawa,ganin ya daga wuka zai fille masu Kai a tare,yasa su cewa,mun yarda fa mun yarda wallahi, Allah mun yarda wallahi, acikin lokaci kankani suka hada uwar zufa sunga mutuwa yaseer harda guntun fitsarinsa a wando, Yana ganin kuwa ya ajje wukar ya arta a guje a don Shiga bayi,

Yace’ yawwa good boys Ashe kuna San ranku haka, yanzu kuke kirana da Oga kunji ai,
Kamar kadangare yusuf yake daga masa Kai yana hadiyar yawu,dakyar gashi ya makure ajikin lungun bango, ya durkusa,

Yace’ kuma inaso ku kwantar da hankalin ku kamar kuna gida, ga Kaya nan na kawo maku idan kuna bukatar wani abu kuyi knocking kofa zanji zan zo,ga abinci na kawo maku kuci ku koshi kunji ko?
Bai jira amsar suba ya maida wukarsa yayi gaba, yaseer yana Jin ya fita shima ya fito, ya zube a gado,vl basu da wata mafita face su bashi hadin kai dari bisa dari yaseer ya fada Yana suke ajiyar zuciyar a akai akai, shi kuwa yusuf baima iya bashi amsa ba saboda yanda yaji kansa wani iri kawai haskowa yake an fille masa Kan nan da yanzu ya farka ido yaji ana cewa man rabbuka, taaab lalle ne abinda yake gani a film ashe anayi a gaske,wuyansa ya shafo ya ji,ya sannan ya sauke wata ajiyar zuciyar da baitaba yi ba tunda uwarshi ta kawo Shi duniya, daga bisani ya zame ya kwanta, basu san iya adadin da suka kwashe ahaka ba,Amma Jin ana kiran sallah yasa ya tabbatar musu da Azahar ce tayi, yaseer ne ya fara tashi ya bude ledan Kaya ne sosai dayawa sai ledan abinci, kayan ya fitar ya gani sosai kayane masu kyau kusan Duka iri daya ne har colour.

Sai dai wasu ban bancin colour din, kwashe kayan yayi ya zuba su a cikin wardrobe din dakin duka kayan kanana ne, sai singlet da boxers Suma duka wayanci iri daya ne, bai wani shirya su ba kawai, sai wata leda da gani itama,zazzage ta yi ganin su brush Maclean ne da kayan amfani yasa yakai toilet cikin karamin cupboard din da yagani yasa Shi zubawa,daga nan yayi wankan sa tare da alwala da brush ya fito, shima Yusuf ganin yaseer ya dan kwantar da hankalinsa yasa Shi kwantar da nashi hankalin
Sai da sukayi sallah sannan suka ci abinci gudun kar suje yunwa ta masu illa. Daga nan kuma aka fada tunanin gida, babu wacce suke ji irin ummu, yau zata shiga makaranta ko a,a.
Bama sajin mama akan yanda suke jin ummu daga nan kuma suka gangara tunanin yaya, sun san ta zuba ido ta gansu amma shiru. Suna nan har la’asar suka tashi sukayi wanka,aka kawo masu abinci suka ci, har dare yayi, oga ne yace su fito su zauna a parlourn zasu tattauna, suna fitowa kuwa sukayi arba da kattai manya manya, a daddare suka samu wuri suka zauna,ganin haka yasa ogan sake masu sosai yayi wasa dasu yayi ta jansu da hira saida yaga sun sake amma ba can ba sannan ya fada masu abinda yake so, su duk a tunanin su wani mugun aikin ne,amma dukda haka basu ji dadi ba sai dai tunda zasu iya abarsu sukoma da ransu kuma a sake su to yafi komai dadi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page