A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????

     _Akanji magana_


     10

Mus’ab ne ya share Mata hawayenta sannan yaci Gaba,
Shekarar mu daya da yin candy bamu ci gaba ba bama ma fita sakamakon Daddy yayi tafiya tsawon shekara daya,
Ana ya gobe bb zaidawo ina gyara masa dakinsa,shikuma twiny Yana waje kasancewar babu kowa a gidan daga Hajiya sai Saima yar Hajiya kenan Wanda take sa’ar muce ita,ina cikin gyarawa ya shigo dakin yana Mita,ban Kula shiba donni nazata da Yan unguwa yake fada, ganin mitar taki karewa nasa nace’ me ya faru zaka shigo kana yiwa mutane Mita haka,kana wani hade Rai,
Sai

yace’ Saima ce tazo ta sameni tace wai mu yafe mata,ta tuba meye da meye haukarta de,wai kasan me tace daga karshe?
Girgiza masa Kai nayi yace’ ca tace tana sanka,nazo na fada maka,

Kai kuma me Kace Mata,

Kasan de bazan ce mata a,a don ko kallanta ma banyi ba, bare kuma a samu matsla,to kawai nace Mata.

Ni Gaskiya Bana Santa,taya za’ayi ace yarinyar da ta wulakanta mu,tun muna yara kuma yanzu tazo tawani ce tana San dayan mu,Kai ina bazai yiwu ba,
Baka ganin tarko aka Dana mana?

Abinda bansani ba de,Amma tunda gobe BB zai dawo ai sai mu fada masa ko?
A haka muka yanke shawaran fadawa BB ,daddare muna zaune a part dimmu muna game,ta shigo cikin wasu arnan kaya, masu bayyana tsiraici,ko sallama babu bare kuma mu bada izinin Shiga,Bama mu lura da ita ba muna game dimmu, tazo kanmmu ta tsaya

tace’ mus’ab kaji abinda mas’ud ya fada maka ?
Sai da tayi magana sannan muka lura da ita ganin irin Shigar dake jikinta yasa muka kalli juna,bamu Kara kallanta ba Saida ta Kara maimaita wa, cikin wata jarumta

nace’ Gaskiya Bana sanki,Baki min ba kuma…..
Kafin ma nagama fadar abinda Zan fada ta wanka min Mari,daman nasan za’a rina shiyasa ko kallanta banyi ba,a tare muka tashi zamu fita,ta rike rigar mu ta baya,bamu Ankara ba ta saki wani ihu,kamar a mafarki muka ga ta fara yaga kayanta, sannan kuma tana gunjin kuka,tsabar mamaki tsayawa mukayi muna kallanta,bamu Kara tsinkewa da lamarin ba sai ji mukayi ana bubugga kofa,Ashe ta kulle kofar bayan ta shigo,dakyar mas’ud yaje ya bude kofar,Yana budewa kuwa ta fara zabga masa Mari ta ko ina,tana duka Shima Daddy ni ya kama yake zabga Ashe ya dawo bamu sani ba, Saida sukayi Dan kansu suka gaji sannan taja hannun yarta suka fita.
A ranar gani mukayi Ashe da ba kunci muke ciki ba yanzu ne muke cikin kunci Rana daya?tunda muna yara ake kulla mana sharri kuma mace amma gani ma mukayi Ashe ba sharri ake mana ba, yanzu ne aka yi mana shi.
Allah yayi mu da tsoron Mata sai tsoronnasu kuma ya Karo sanna tsana ta biyo baya. A parlour muka kwana ranar bamu rintsa ba, aranar muka fara tunanin iyayen mu.
Daddy kuwa ko a masallaci da muka hadu gaisawa mukayi dashi sosai kamar ba abinda ya faru,amma muna zuwa gida ya daure fuska,
Gari na Gama wayewa aka Kira mu aikin gida,kamar kullum aikin gidan muke gaba dayansa,sannan muka bi dakunan yammatan muka gyara dayake su basa nan,Anty ma bata nan amma haka muka gyara ko ina Banda dakin Saima,
Kamar jira take kuwa takai Karan mu wurin Hajiya, Hajiya kuma tazo ta tasamu a gaba sai mun gyara Mata daki idan bamu gyara ba wazai gyara? Dayake Daddy Yana yace ta gyara da kanta, muna nan zaune kuwa sai ga BB nan yazo. Tashi mukayi muka fita,bamu San me aka fada masa ba sai ganin sa mukayi idan shi yayi jajur tare da tambayar me ya faru,bamu boye masa komai ba muka fada masa abinda ya faru.
Bayan kwana biyu kuwa Daddy yace mu hada kayan mu zamu tafi da BB Spain acan zamuyi karatu,hakan yayi mana dadi bakadan ba.
A wurin kanwar Daddy BB yake acan,Wacce ake Kira da Anty ummi, Anty ummi bata taba haihuwa ba,sai yayan mijinta guda biyu Maza da take rikewa,bata da fara’a sosai sannan kuma tana da taka tsantsan a tarbiyar yara, sannan tana da bin kwakwafi akan yaranta. Rayuwar mu ce sosai ta sauya dukda de baza’ace muna cikin soyyayar uwa ba amma idan mukayi Abu ba daidai ba to zamusha fada sanann kuma daga baya tayi mana nasiha,idan taga dayanmu cikin damuwa to dole sai ya fada Mata mene silar damuwar sa, yaran da take rikewa Duka shekara goma sai kuma shekara takwas,
Mijinta beda matsalar komai don yana Kula da mu daidai iyawarsa. Kasancewar Fulani ce yasa bata mana Hausa sosai,daga mu har yaran,daman Shi BB basa Hausa dashi sai jefi jefi, tunda a wurinta ya taso,sai ya zamana muma mun fara iyawa,
Sannu a hankali muka fara zuwa makaranta physics muke karanta muduka,sosai wata shakuwa ta Shiga tsakaninta damu,bata fiye Zama ayi hira ba kullum tana daki,Amma zuwan mu yasa mas’ud zuwa dakinta ya jawo ta mu zauna ayi hira da ita, a hankali kuma ta fara sakin fuska,idan muna gida kuwa Bama barinta tayi aiki mu mukeyi har dakinta mu gyara komai. Sosai muke Karatun mu hankali kwance bamu da damuwar komai. A school kuwa mas’ud Yana ganin mutum zai fara zagin sa ba gaira ba dalili ko da Hausa ko kuma yayi da fulatanci,nasha hanashi yaki hanuwa, ga shegen fada,ko Dan bige Shi kayi to sai ya rama,dama can Ashe wuri ne baisamu ba.
Shekarar mu hudu cib muka kammala karatunmmu lokacin BB ya samu aiki a Nigeria tare da wani company, Shi architect ya karanta.
Dawowar mu Nigeria munzaci Abu zai lafa Amma babu lafawar da yayi, dukda de yanzu mun rage aiki amma kuma mu muke yiwa kowa wanki a gidan, Duka yanzu saura su hudu a gidan,Saima ce yanzu babba sai Ameera da Aneesa kusan sa’anni sai kuma Fatima wacce ake cemata auta,
Alokacin ne kuma aka tashi daga wanan gidan aka dawo zoo road kasancewar Daddy ya Shiga cikin siyasa sakamakon da dayake aikin governmenti,gidan upstairs ne,kowa na ciki, Amma mu muna boys qrts, sai na masu aiki,
Bayan mundawo daga camp aka tura mu service, kudu amma ba gari daya ba ,mukam mungi son haka dukda bamu taba rabuwa ba ,Amma hakan ya mana dadi,Amma kuma muna fadawa Daddy yasa aka mana transfer muka dawo Kano,bahaka muka soba Amma daddy yafi karfin komai wurin mu,shekarar mu daya munayin service muka Gama,sai zaman gida kuma, lokacin shekarar mu 22,Amma babu abinda ya sauya game da tsanar da Yan gidan suke mana,
Yanzu Daddy kulluma beda lokacin mu tun muna masa uzurin siyasa ce har muka gane Ashe kullaliya ce aka mana, yayin da BB shikuma ya koma Spain Yana yin masters dinshi,mu kuma muna gida,koda mun fita munyi yar buga bugar mu munsami kudi,muna dawo wa za’a kwace yan kudin da mukasa mu,daga baya mu kuma sai muke boyewa abinmu, a lokacin Anty ummi ta fara rashin lafiya ashe tana da ciwon zuciya,kuma taki yarda Amata aiki tace a dawo da ita Nigeria ana dawo da ita kuwa kwana daya ta rasu, wannan mutuwa bakaramin girgiza mu tayiba don mu Bama musan meke damunta ba Saida ta rasu. Zan iya cewa ma BB yafi kowa jin mutuwarta sabida a hannunta ya taso,itace mahaifiyar sa,da zai iya kiranta da shi. Ahaka komai ya wuce mutane aka fara mantawa da ita,saidai mukam har yau mutuwar ta sabuwa ce a garemu,itace mutum na biyu da ta taimake mu,taimakon da zai sa mu taimaki wani muma. Bayan bb ya kammala masters dinshi ya dawo yacigaba da aiki, yasamu aiki a Spain Amma be zauna acan ba ya dawo yacigaba da aikinsa daga nan shima ya fara kokarin ganin ya bude nasa company yasai fili kuma ya bukaci Daddy da ya taimaka masa tunda bazai iya Shi kaidai ba amma haka Daddy ya watsa wa idan sa toka yace bazai yiba daga karshe ma sashi yayi ya saida filin da yasaya kuma maimakon ma a bashi kudin ba’a bashi ba,dukda munsan ya damu amma ko a fuska bema nuna ba,ganin muna fuskantar matsala idan baya nan yasa Shi turo mu masters.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page