A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yusuf yace’ wai ca aka ce maku mun mutune ko yaya?

Yaseer yace’ mundawo baza’a yi welcoming namu ba,

Mama tace’ kune? Baku mutuba? ‘ya’yanah kun dawo gareni?

Sameera tace’ kamar ya? Baku mutuba wai daman?

Yusuf yace’ Wanda ya mutu idan Yana dawowa to mun dawo,

Yafada tare da zuwa ya zauna shima yaseer zuwa yayi ya zauma,

Mama tace’ ku fada mana ya akayi haka?

Yaseer ne ya Basu labarin komai,

Sunyi jimami bakadan ba,
Mama tace’ dakunje gidan su Ummu yarinyar nan ta damu,Tama fini Shiga damuwa,

Yusuf yace’ munje ai,Basu jima da dawowa ba daga Adamawa uncle dinta ne yayi accident ya Shiga ana zaton ko ya Shiga comma ne ba’a sani ba shine aka tafi dashi London shine yau suka dawo,

Mama tace’ subhanallahi dole naje gaskiya Nayi musu jajaje wannan Abu har ina haka? Allah ya kiyaye Amma ni bamma San shi ba gaskiya,

Yaseer yace’ mama idan kika ganshi kamar su daya da ya……

Yusuf yace’ yaya sameera, yarda kuka ganta haka take,sai dai Shi Baki ne ita kuma fara ce,
Yusuf ya aikawa da Yaseer wata uwar hararan Baka da hankali shima ganewan da yayi me yasa Shi wayem cewa ( yaseer akwai gane Abu ????)

Yace’ wallahi Mama Nima da ganshi fa nashiga comfuse sosai,

Yusuf yace’ dalla yimin shiru babu wani kama suke ba,ni karya ce Bana so,

Sameera tace’kuma kace muna kama? Shi baki,nikuma fara,

Yusuf yace’ a cewar yaseer ba? Haka yake cewa kuma nasan hakan zaice,

Mama sai nan nan take da su haka itama Sameera dukda babu shakuwa a tsakanin su Amma a kwai respect da fahimtar juna, koda Abba ya dawo shima yayi mamaki wannan lamarin.

????????????????????????????????????????????

Da gudu ya fito daga dakinsu Yana
cewa’ bb bb fav kuna ina, basa Parlour hakan yasa ya wuce daki namma basa nan sai kawai ya fito waje suna wurin Shan iska da gudu ya karasa

yace’ bros yayi accident wallahi yayi accident Allah shiyasa Bama samun sa, shikenan,
Sai kuka ya rungume bb da suka tashi tsaye tun kafin ma ya karaso Jin Kiran su da yake, shima Binaif din rungume shi yayi

yace’ cool dawn, fada min taya kasani,

Yana shashshekar kuka
yace’ muna waya da Sameera sai suka dawo kuma bankashe wayar ba lokacin ina typing Abu a system to a speaker nasata shiyasa ban kashe ba, naci gaba dajin zancenta, har na fara Jin zancen su anan naji abinda yake faruwa,

Sai ya Kara fashewa da kuka, shima Mus’ab kukan ya farayi ya rungume bb shima bbn rungume su yayi,Suma sunyi kika ina ga Ummusalma kuma? Ajiyar zuciya ya sauke yaja su ya Kai lilon ya zaunar su shikuma ya tsaya,

Yace’ baza ku iya Kula da ita bakena ko?
Shiru yayi sannan yaci Gaba,
yace’ kunsan me kukeyi kuwa? Kuka fa kuke? Ko Baku sani ba? Ehh?
Iska ya furzar yace’ kun fita shekaru ina ganin zaku fita hankali da tawakkali Ashe nayi kuskuran fahimta, yanzu idan nace kuje ku fada Mata mezatayin tunanin ya faru idan kukaje kuna kuka? Tunani zatayi mutuwa akayi, shine abu na farko da zata kawo aranta,kuka beda amfani, na farko zakuyi asarar lokacin,na biyu zaku sa kanku a damuwa na uku zakusa zuciyar ku ta cunkushe, na hudu da kukan da kuke inama zaikiri kuke? Kuka ma Kala Kala ne, bako ina akeyiwa kuka ba, akwai abin kuka a lokacin baza ku iya kukan ba Alhali kuna so kuyi Amma ba halin yi,ku tana da kukan ku, zaiyi maki amfani, kuyi masa addu’a Allah ya bashi lafiya itace kawai addu’ar,

Shiru yayi yace’ yanzu kuma itama taje tayi Mata kukan, hmmm,

Yasa Kai ya fice Jin ana kiraye kirayen sallah, sun jima a wurin don sai da aka kusa idarwa sannan suka tashi suka tafi, a masallacin sukayi alwala Dan kar ma su Kara makara.
Saida sukayi Isha sannan suka dawo ‘yan gidan sun handeme a parlour damma yanzu sun warke Amma Aneesa har yanzu kugunta ciwo yake, darurarta daya Allah yasa ba illa ya jawo Mata ba, suka shigo suka wuce kowa yayi dakinsa, a kusan tare suka fito,yau bejin San Jan mota shiyasa yabawa Mus’ab key din yaja shikuma ya Shiga Baya, ya lumshe Ido so yake kawai yajita a jikinsa wata kasala yakeji da kewanta yarasa wanne daga ciki ya rinjayi daya, idan sa a rufe sukuma sunyi shiru ko radio babu balle waka damman Shi ba kunnawa yake na kar gwara radio Yana saurara, har suka isa yayi parking sannan suka fito parlourn Baban su Nafisa suka Shiga na bangaren ta ganin parlourn ta da Baki shiyasa suka wuce suka Shiga,Anty safiya ta gansu kuma sai taga kamar wani Abu nadamun su,ta taso Dan taje taga kiranshi, tashi tayi ta Shiga parlour gaisawa sukayi,

tace’ lafiya?

Binaif da ya kwanta yace’ lafiya qalau yunwa mukeji kawai ASA akawo min abinci su inaga sun koshi,

Mas’ud yace’ haka muka ce ma?

Yace’ haka nagani de,

Anty safiya tace’ to Bari masa Nafisa ta hada maku ni nayi Baki,

Tashi zaune yayi yace’ Nafisa kuma? Ina take ita?

Sarai tasan wayake nufi tace’ kaga ni Bani da wata gidannan kowa Yana da sunan shi Bari naje,

Tatashi tafita, mas’ud da Mus’ab kuwa hada Ido sukayi suka basar Sarai ya gansu ya koma ya kwanta ji yayi ma Shi ba dadi wallahi, Shi kadai yaka fa Jan tsaki,ya jima beja tsaki ba daman,aikuwa ya fara Mita shikadai a ransa,

Nafisa kuma bata nan tana wurin Hajja Dan yanzu wayancj suna can har itama Ummusalman tana zuwa Amma ba sosai ba,sai dai yanzu suna can su Duka, don haka tayi hanyar part dinta, da sallama ta Shiga, Hajja ta amsa, suka Dan gaisa,

tace’ Nafisa tashi kije ki hadaw su Binaif abinci su uku ne Maza ki Kai masa,

Hajja tace’ a,a zancen me nakeji? Ina kince min wannan ce matar tashi salamatu?

Tace’ ehh itace,

Hajja tace’ to iya zata Kai masa,Maza tashi kije ma ki hada masu anan, Nima nayi tuwom ai,

Nafisa tace’ kinyi tuwo ko kuma kinda anyi tuwo?

Hajja tace’ kome kika dauka duk haka ne,ja’ira kawai,

Badan Ummusalma taso ba itama tashiga kitchen din Hajja Nafisa ta taimaka Mata, ta jera komai a tire sannan ta fito ta kofar baya ta shigo sabida mutune dake parlour, ciki ciki tayi sallama idan sa a rufe har tazo ta dire a gabansa besani ba,sai dai yasan anzo Dan wani kamshin turaren wuta yaji mai sanyin dadi Yana tashi, sai ya Kara lafewa a jikin kujerar, ajjewa tayi zata fita har taje bakin kofa,

Mas’ud yace’ ya zaki tafi Baki zubawa mijinnaki abinci ba? Kinsan fa ajebo ne,

Ai bashiri ya tashi zaune Jin ance miji aikuwa itace da Shigar ta ta kulluma bata da Kaya sai doguwar Riga sai kace mai ciki(????) a yarda yace, dawowa tayi tana gallawa mas’ud harara, ta tsugunna ta zuba masa ta Mika masa,Yana kallanta it’s komai nata da sanyi takeyi Amma ta iya fada da sauri har tana kamar ta sarke Dan bala’i, ganin ta miko masa bata ko kalleshi ba yasa Shi kin karba, ganin be karba ba yasata karawa ta mikawa su mus’ab mas’ud ne ya karba tare da daukan spoon,

yace’ fav zomuyi nan,
A tare suka fita, Kara zubawa tayi ta Mika masa bata kalle Shi ba, namma kin ansa yayi dagowa tayi suka hada Ido ya kauda kansa gefe,

tace’ Ka ansa,

Yace’ nagani ai, Amma gani nayi ba’asan naci abincin shiyasa,

Tace’ ni banceba,

Nima bance kince ba ai

Gashi kuwa Ka fada?

A,ah nace gani Nayi,Alana nagani ai shiyasa na fada hakan,

Tace’ Wacce alama Kenan?

Kinga na farko kinzo ba sannu da zuwa ba gaisuwa ba ya aiki ba ya gajiya ba komai, sannan sai da aka fada maki aikinki tukun kika dawo kika yi sannan kuma the worse ko kallo na ma babu,

Tace’ to naji, na gyara ina yini,ya aiki,ina gajiya,kazo lafiya?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page