A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

✨✨✨✨✨✨✨

Suna zaune a tsakar gidan bayan sun gama cin abincin su, sai hira ake da raha,

Mus’ab yace ”wai taya kika hadu da ita?”

“Kawai haduwa mukayi a asibiti shikenan muka kulla kawance shine kuma take fada min tayi zaman Abuja kaza da kaza waye da waye shine fa kawai na tambaye ka unguwar daka zauna shine Ka fada, Ka wani kwafsa”

“Dana yi me?”

“Mtsww tace kamar na sanka din nan ai sai kaja ta da hira ehh wallahi nima ganin sani nake maki waye waye amma sai kayi shiru”

“Banni kawai am speechless”

Mas’ud yace” wai daman wannan yarinyar ‘yar renin hankali wani ta kalle mu ta kallli wannan yarinyar tace kannai, ta ban haushi”

Amina tace ”ya Mas’ud tambaya fa tayi”

Binaif yace ” kaci sa’a da bata ce Kannan bane danine haka zance ehh kannai na ne sai me aciki”

Mas’ud yace ”tab da anyi ruwa da kankara kuwa, bawannan ba Fav yaushe zamu je mu Hira ne wai?”

” Twinny baza ni da Kai ba”

“Kar Allah yasa aje din, ya sunan ta?”

Ummusalma tace ”sunan Inni ne da ita fah”

Amina tace” tab akwai girmama wa Kenan ko, sunan uwa guda?”

Shiru mas’ud yayi Dan beza ci haka ba, Sam yaso ace ba haka bane da sai tayi kuka idan suka hadu,dukd hakan ma ba kyale ta ba zaiyi,

Ummusalma tace ”Zafa kaje dubiya Abban na beda lafiya”

“Abban ki kuma?”

“Haka take fada,Abba na, Abba na, komai Abba na, kaga Kenan ya dawo Abban ku”

Mus’ab yace ”yes of course Abban mu”

Tashi Binaif yayi yace ” ga me tafiya”

Kallan Ummusalma yayi Yama ta alamar ta same Shi a mota

Mas’ud yace” zaka tafi baka yiwa Baffa da Inni sallama ba”

Har ya kusa zuwa kofar fita yace” ina ruwan ka ne”

Bakin sa yayi yayi alamar zip, yace” babu water na a ciki”

Mus’ab yace” Kai Kam baza Ka taba dena magana a cikin hurumin da babu ruwan Ka”

Ummusalma tashi tayi ta fita,

” Sai lokacin daka dena munfirci Zan dena”

“Waye munafikin”

“Wanda ya tsargu Ida Ka tsargu kuma tou, amma ni bance munafiki ba”

Kwafa yayi yace” kama ce,wallahi yanzu nan nace a fasa bikin, daman ba zuwa wurin budurwa kake ba,naje na hada maka bomb din da zata ji Baya san Ka, sai anzo biki tace ta fasa”

“Zafa Ka iya ko”

“Sosai ma”

Ganin Shi a baya yasa itama Shiga bayan ta zauna, ganin tazarar dake tsakanin su yasa ya kalle ta ya kalli space din,

yace ”ni zan matso ko ke zaki matso”

Turo baki tayi gaba, sannan ta matso daf dashi, be ishe Shi ba sai ya kuma janyo ta jikin Shi,luf tayi a jikin sa Yana daga ta yayi ya cire mata hijabin ta ya kuka rungume ta yana shafa Mata baya, cikin irin muryan nan Mai kama data Yana Jin bacci

yace ”sai yaushe?”

Rufe idan ta Dan kwanciyar tayi Mata dadi sosai har wani bacci bacci take ji, bude idan ta tayi ya fara wasa bottle din rigar sa,
tace” duk sanda ka ga dama”

Rike hannun ta yayi yace” baza ba ki daga min hankali ba, kuma ki tafi ki bar ni yau zanyi missing”

Shiru tayi bata ce komai ba yace” mi amor”

Tace “yau meye fassaran Shi please”

” My love”

Kallan shi, tace” my love?”

“Ehh”

Tana kallan Shi shima kallan ta tace ”tun yaushe Kenan?”

“I don’t know,kawai ji nayi na kamu, kefa?”

Kwanciyar ta tayi tace” ba kamu wa mayi ba,harbu wa nayi”

“Really?”

“A’ina na harbe ki”

Shiru tayi ya matse ta, tace” baby na Yana kuka fa”

Sakin ta yayi yace ”kin ma fini san wannan babyn”

“To kar naso Kaya na?”

“A’a so abin ki,wata nawa ne”

“Uku”

“Laa tab kice wata ba’ita ba biki”

“Hmmm bari za’ayi sai an gama suna sannan ayi bikin”

“Wacce yarinya ce yake nema?”

“Sameera ce”

“Mas’ud”

“Please Baby idan kaje gida kaje gidan su ummu idan kaje please Ka neme wa Yaya auren ta nasan Baban ta zai ba shi”

“Meyasa kika ce haka, ummu she’s just 17”

“Amma zata iya zaman aure ba”

“Please kidena it can’t be possible”

“Ummu na san uncle din ta,shima uncle din ta nasan ta, yusuf ada Yana San ummu but lokacin da yaji komai lokacin ya yanke shawarar bazai bar ummu tayi saurayi ta ba kodan uncle, kaji yarda abin yake, Shi Yusuf ya Riga su Jin komai daga wurin Antyn Ummu”

“Shikenan yarda kika ce”

“Yawwa fa yarda akayi bikin mu Suma haka za’ayi nasu,a daura aure take Kula da mijin ta that’s all”

“Mus’ab fa”

“Wannan rabu dashi zan San yarda akayi”

“Baby please Ka bar wannan shafa bayan babu dadi”

“Bari to na zuke zip din sai nayi dakyau”

Fara wa zugewa yayi kafin ta farga har zuge mata zip din, a sukwane ta tashi tace” haba Dan Allah baby na tace bata so fa kabari nikam”

Janyota yace” idan to zo muga babyn, wannan babyn tafi ye cin”

“Yanzu ma yunwa nake ji”

Ware ido yayi yace” yaushe yaushe muka gama cin abinci”

Turo baki tayi tace”Sake ni nikam, tafiya zanyi”

Hade bakin nasu yayi,tuni itama tafara kawo charge sai da ya kashe Mata jiki bata da ko digon karfi,
yace” mu tafi gida?”

Shiru tayi tana sauke numfashi,bata da muryan ma da zata bashi amsa sai girgiza masa Kai da tayi alamar a’a,

Ajiyar zuciya ya sauke Yana cigaba da shafa ta, shine harda su balle bra, kasa Hana Shi tayi,don bata da karfi ko digo a jikin ta,

Sunkuya wa yayi yace” nayi?”

Ganin idan ta a rufe yasa yayi wani munafikin murmushi, ya cigaba da abinda yake,

Mas’ud ne ya kwankwasa glass din motar, tsaki yaja,ya Dan yi kasa da Shi glass din kadan ,

yace ”meye?”

Mas’ud yace “bakomai kawai de naga lokaci yana tafiya”

Tsaki yaja ya mayar da glass din ya zuge, yasa mata hijabin ta, sannan suka fito, ko kallan Mas’ud beyi ba ya wuce Shi, suka shi,

Mas’ud kuwa yace” oho de koma meye”

Shima ya Shiga, a waje ta tsaya shikuma ya wuce ciki ya masu sallama zasu wuce,

Baffa yace ”ka dauki matar ka Ku wuce”

Murmushi yayi yace” a’a Baffa zata zauna anan ko zuwa gobe ne ma”

Baffa yace” ai muma goben zamu wuce Gumel daman rashin lafiya Innin kuce shiyasa muka zo nan din Amma Insha Allah gobe zamu wuce”

Binaif yace” to goben idan Allah ya yarda sai nazo na dauke ta,amma zamu wuce da su Mus’ab”

Baffa yace” to shikenan hakan ma yayi daidai”

????????????????????????????

Suna zaune harabar gidan, suna Shan iska, Dan babu batun nepa jiya aka zo aka tsige ta, Sameera dasu Yusuf suna zaune kowa da abinda yake,

Mama tace” kudin masu aiki”

Numfashi yaja ya ajje, yace” zan bayar ko zuwa gobe ne”

“Ina kudin da ka Ka Ciro jiya Mai uban yawan nan”

“Ya ilahi! Kin manta da Shi na biya masu nepa?”

“Duka uban kudin nan ka basu? Zaiyi kusan dari biyu”

” Na bawa su Yusuf Arba’in, na bawa Sameera goma, na basu dari da talatin,ashrin din na bawa mai gadi”

“Gaskiya Kam”

Jinjina kai,kawa tayi,

Yace” idan an sallame su, shikenan sai su tafi, dan bazan iya ba duk wata ana basu kudi”

“Suna tafiya ina tafiya ta, wallahi bazan iya ba, me kake nufi? Cab! Nifa Kenan zanyi aikin gidan nan”

Be kula ta ba, ya kalli Sameera da take rubuta project,
yace ”Kina da Wanda kike so?”

Gaban taji ya fadi, tazaci zai nemeta Ashe ba zuwa zai yi ba, a hankali ta girgiza kanta hawaye na nema zubo mata,

yace” wani zaizo yayi maganar zuwa gobe, kira na de yayi a waya daman idan kina so wani ne tunda bakya San wani kuma to falillahil hamd”

Wani siririn hawaye ne ya zubo mata, haka nan taji gaban ta ya Shiga faduwa, ambatan Allah kawai ta fara yi, daga karshe ma tashi tayi ta koma daki,suna su yusuf kwashe kayan ta sukayi suka Shiga dakin, babu Wanda ya iya ce Mata uffan kawai tagumi sukayi suka zuba Mata Ido.

Har akayi magariba akayi isha suna nan Basu tafi sai dai idan lokaci yayi suyi sallah su dawo basa ce mata komai sai kallo, sun dawo daga sallahn Isha Kenan sun koma dakin Sameera sai ga ummu nan,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button