A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’ me yake so kuma?

Murmushi Anty safiya tayi,
tace’ a bangaren abinci Yana san dambun cuscus,tuwo, yadai fi san abincin gargajiya, Zan iya fada maki sauran kya gane da kanki na Baki hint,
Hannunta ta kuma kamawa tace’ taso muje parlour,
Parlourn suka koma Anty safiya ta je dakin Umma sai gata da yar jaka ta fito tana Kiran mai aikin Umma zama tayi tace’ sauko kasa na maki kitso, babu yarda ta iya haka ta sauko ta zauna badan taso ba sai don bazata iya musu ba, mai aikin kuwa da lalle ta fito a hannun ta,

Umma tace’ ki mikar da kafar a miki kunshi,
Shima mikewa tayi aka fara Mata, ummi da tun dadewa ta fito daga daki tana kan kujera tayi nan tayi nan bata zama wuri daya sai kace rainan Maza.

????????????????????

Ji yayi ma zuwa gidan ya masa nisa gabadaya wani tashin hankali yake ciki wani irin zufa ce ta jika masa kayansa babu abinda yake furtawa sai Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, har ahaka yazo gida ko jira agama parking beyi ba ya fito ya Shiga gida,bakowa a parlour sai TV dakin Mama ya wuce fitowar ta kenan daga wanka ganin yanayinsa

tace’ Alhaji lafiya kuwa?

Yace’ wanne lafiya? Mutane ashe daman kawai kiwon mutane suke haka? Yau kinji tambayar da aka min ne? Bazan iya tantance maki tashin hankalin da na Shiga ba,daman da ace ba a gaban su nake ba wallahi sai na shako su sun fada min uban wa ya fada masu wannan maganar, wannan ai tozarci ne,
Fada yake bilhakki da gaskiya,

Mama tace’ haba Alhaji Ka fada min me ke faru mana ba wai ka daureni ba da jijiyata ba, yi min bayani meke faruwa,
Banza yayi da ita ya fara zirga zirga sai da ya lafa sannan ya fada Mata abinda ke faruwa,

tace’ Alhaji baka ganin kawai ‘yan adawa ne da basa son ci gaban mu?
Tace’ kuma beyasa Ka sai da company bacin bamu da takardu a hannu,

yace’ dalilin shine,zamu sami riba biyu kinga ga kudi sannan kuma ga companyn mu zai dawo gare mu, kinga idan na bashi takardun karya da shi zai dogara kuma kinga bayan kwana biyu sai naje da shaidu na kinga daga nan zai dauko waccan takardar a matsayin shaida kuma ta karyace shikenan zai dawo hannuna idan ma ba’a ci tarar sa ba,

Tace’ to da kasan da wannan wannan zancen banza zai daga maka hankali kyalesu kawai sai mu dauko ‘yar gidan Yaya hajjaty dake Cyprus kaga shikenan kuma ita Salma ba Ummusalma ba,

Jin wannan batu nata yasa Shi cikin farin ciki tuni yama manta da batun ‘yan jarida kuma zaiyi maganin su amma ta yaya?

✨✨✨✨✨✨✨

Bashi ya dawo ba sai karfe uku na rana kasancewar yau juma’a akwai cunkoso shiyasa ya jima be dawo ba har uku, gaba daya ya gaji rigar bayan ya cire ya riko a hannu ya daura a kan kafadar shi dayan kuma ya riko Leda ya shigo gidan,a Kan kujera ya zube ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya rufe Ido yayi ya bude dakyar ya tashi ya Shiga daki tana kwance kamar me bacci sai dai ba bacci take ba tunanin sa kawai take har yanzu bai dawo ba kuma ta kasa kiranshi kawai sunansa ta zubawa ido wayar a hannun ta take Idan ta a rufe kanta a bude kitson ya zubo har kafadar ta ta sha riga da wando sun Mata kyau sosai kallanta kawai yake baima San ya karaso ba sai ganinsa yayi a Kan gado gefen ta yasa hannu ya fara shafa gashinta kanta, a hankali ta bude ido suka hada Ido kasa dauke nata tayi sai ma kara zuba masa su da tayi samun kanta tayi da,

cewa’ ina kaje? Baka tashe ni ba?
Bai dena shafa kannata ba cikin muryan nuna alamar gajiya kuma a hankali,
yace’ Baki min sannu da zuwa ba zaki fara tambaya ta?

Tace’ Baka fada min ba,kuma sannan Ka tafi kana fushi dani,

Hawayefa yake hangowa kwance a idanta yana daf da zubowa. ji yayi bai kyauta mata ba ya fada laifinta atleast yasan zata gyara, ganin idan tasake magana hawayene zai zubo mata yasa ya sunkuya daidai fuskarta ya furta am sorry,
Ya fada yana lumshe ido,
Tashi tayi zaune tana goge Dan hawayen da zai zubo mata,ta tashi ta shiga toilet bata jima ba ta fito,

tace’ na hada maka ruwan Ka kaje kayi,
Ware ido yayi irin really……

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

INA MIKA GODIYATA GAREKU MY FANS,IRIN YARDA KUKE SON LITTAFINA, BAZAN IYA CEWA KOMAI BA,SAI GODIYA ALLAH YA BARMU TARE INA MUGUN YINKU IRIN OVER DIN NAN SOSAI,
GAISUWA TA MUSAMMAN ZUWA GA AMSIE(cwthrt????)
MUJA(yallabiyata????)
UMMIE MUKHTAR
WALEEDA
DA KUMA SAURAN INA ALFAHARI DA KU DUKA
love you all ????.

22

Yana Jan Jan Dan ya taje, ta rike hannunsa,sabida wata irin masiffan zafine daya ratsata,

tace’ a hankali fa ake bi,

Yace’ Madam a hankali fa nayi,

Wanne hankali kasa duka karfin Ka kaja,sai kace Ka damu gashin doki,

Yace’ to naji sake min hannu, zanbi ki a hankali bazan yi da zafi,

Promise?

Promise,

Sake masa hannun tayi,tana kallansa yarda ake kunshe dariya,aikuwa ta Kara hawa gashi yace Mata Madam, ahankali yake bin Kain yarda bazata ji zafi har ya taje Shi tsab,ya kawo mai ya shafa Mata,ya kuma tajewa,ya dauko ribbon,

yace’ to ki juyo mana a kulle kinsan bazai dauro ta haka ba,
Batayi musu ba ta juyo shikuma ya daure Mata kai,

yace’ kinma fi kyau haka,kyanta kitso aka min,a yarda suke haka sai sun fi kyau,

Tace’ ban taba kitso ba.

Yace’ to juya kiga yarda na iya gyaran gashi na tabbatar ko ke bazaki iya ba,
Juyawa tayi ta kalli kanta a jikin madubin ta kalle Shi yarda yake murmushi irin nayi abin arziki nan,

Tace’ sai kace wata yarinya zaka min three babies?
Ashe shiyasa yace da kitso ne sai yafi kyau, kallon Shi tayi,

tace’ wannan ai damuna zasuyi,

Shidai Yana tsaye Yana kallanta ta jikin mudubin, yarda take cuno baki tana kumbura Baki,shifa abin arziki yayi a ganinsa Ashe na yara ne, kuma fa tasan tayi kyau amma take kushewa shikam Allah ya hada Shi da Mata, a Dan zaman da sukayi da ita ya gane 70% a halayarta.
Sunkuyowa Yayi daidai fuskarta suna kallan juna ta cikin madubi,

yace’ kinyi kyau mi precioso,
Ya kaimata peck a kumatu ya fice, murmushi kwance a fuskar Shi,
Kallanta ta dawo dashi wurinsa har ya fice,ta dawo da kallanta ga madubin murmushi tagani a fuskar ta har dimple dinta duka biyu ya lotsa, shafa inda yayi mata peck din tayi tana mai kallan kanta a madubi, Idan aka ce Mata zatayi murmushi nan gaba to zata karya ta mutum,bare kuma ace tayi dariya? Ada tana tunanin yaushe zatayi Kara Jin farin ciki a tattare da ita, sabida damuwar da take ciki kuncin da bakin cikin da take ciki, shekara bakwai ta ta wuce,a tunaninta ma tayi bankwana da dashi, sai kuma yanzu rana daya kwatsam wani daban yasata dariya alokacin da bata shirya a lokacin da batayi zato ba, dukda shima Yana cikin damuwa ahaka yake danne damuwarsa don yaga annashwarta to ita Akan me bazata danne ta ta damuwar ba itama ta dawo kamar kowanne mutum??
Ajiyar zuciya ta sauke,ta cire hijabin da yafawa jikinta ta karasa shafa mai,tana shafawa tana tunano ranar da suka a London har yanzu ta manta inda suka fara haduwa amma Shi kamar ya tuna hakan,
Sai da tagama tsaf ta feshe jikinta da turare, har ta Kai hannu zata cire three babies din da ya mata ko me ta tuna kuma oho ta barshi, wurin trolley dinta ta nufa ta dauko kayan bacci masu laushi Riga da Wanda tasaka ta kuma fesa tureranta, sannan ta jera kayanta a dayan side din, ta jera komai da komai,ta zuke jakar ta sata a kasan wardrobe, kayan bakko ta dauko shima ta dau muhimman abubuwan ta, ta rufe ta ajje, ta fita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page