A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ Baza mu Kara tambayar ki ba amma watakila idan kika ji namu kalar labarin ki tausayawa rayuwar mu ki bamu taki,hannunta ya rike gam cikin nasa

yace” Wasu yara ne Yan shekaru shida suka tashi daga bacci suka gansu a cikin wani kango,suna sanye cikin uniform na makaranta da lunch box a wurin da’alama ta yaran ce,suna tashi dayan

yace’ ya Muka gammu anan,dayan yace” bacci mukayi muka gammu anan mu tafi gida,
Sun fito don su tafi sai Kash sun kasa neman hanya,suka karasa karshe de suka fara tafiya har suka shigo cikin gari,kayan jikin yaren kawai za’a kalla asan yayi datti, kowa sai ya kalle su ida n suka wuce, haka suka Gama zaga gari Amma babu alamar ma garin da suka sani,duk Wanda suka hadu dashi suna tambayarsa ya kaisu gida,kowa kallan mahaukata ya fara yiwa yaran,a haka suka kare suna kuka suna tambayar mutane gidan su, har dare yayi gashi sun fara Jin yunwa, lunch box din hannunsu suka bude suka ga abinci,ci sukayi tas suka cinye Amma kuma babu ruwan sha,inda suka zauna gefen masallaci ne hakan yasa su zuwa suka sha ruwan, suka koshi,daga nan kuma sai bacci neman inda zasu kwanta suke Amma babu wurin kwanciya daga karshe de cikin masallacin suka kwana a takure sakamakon sanyin da ake yi, lokacin sallah akazo aka tashesu dole suka tashi sukayi sallah,Basu iya komawa saboda sanyin da ake yi duk da rigar sanyi a jikin su Amma ta makaranta ce,sai da gari ya waye suka fito suka tsare mai abin hawa suka ce ya kaisu makarantar su, tambayar sunan makarantar yayi sukace Basu sani ba,mai irin wannan uniform din, yace kaf garin nan babu mai irin uniform dinsu, a haka ya wuce ya barsu,ganin haka yasa su sukayi ta tafiya,suka ga sunzo wani wuri,Basu San ko ina bane,don Basu taba zuwa ba Ashe wai Tasha sukaje,ganin mai abinci tana bada abinci kowa yazo ta bashi yasa su zuwa wurin suka ce tabasu,sai tace’ na nawa zata Basu,anan suka San biya ake a bayar, ganin sun tsaya suna kallanta yasa tace’ idan baku da kudi,kuzo kumin wanke wanke sainna Baku sauran abincin, kallanta sukayi sannan dayan yace” taimaka mana zakiyi bamu iya ba,ca tace idan baza suyi ba Tou su tafi kar su tsaya bata Mata lokaci,dayan ne yace zasuyi,hakan kuwa akayi suna wanke kayan ma sunayi tana cewa sai sun sake ahaka suka Gama Mata wanke kayan,abincin kuwa dan kadan ta basu,sai daya ne ya hakura ya barwa daya,suna nan har Rana tayi tace suzo suyi Mata wanke wanke,suka kuma yi Mata shima de Saida suka sake, ta Basu abinci Wanda beci bane da safe ya yaci shikuma dayan ya hakura,har dare muna tare da mai abinci,itace ta bamu wurin kwana inda take sa kwanikanta,anan suka kwana,gari na wayewa ma hakan ce ta faru sai da suka Mata wanke wanke wannan Karon harda Shara sanan ta basu abinci,suna cin abincin take tambayar su,
Ku yaran nan ina de ku ba almajirai bane,kuma de naga kamar daga makaranta kuke ina iyayen ku,daya ne ya bata amsa yace” muma bamu sani ba,kuma mu bamu san kowa ba,
Tace’ to zaku ke kwana anan kuna min Shara da wanke wanke zanke Baku abinci,Tou suka ce,tunda ganan suke shara da wanke wanke,saidai dayan akwai tsokana duk Wanda ya gani indai bai fishi ba to sai ya tsokana shi,ahaka take daura mana talla kullum muna siyarwa wataran kuma ba ciniki, ahaka munkai wata uku a wurinta,Amma bata taba sai musu kayan sawa ba da wannan uniform din dashi suke zama saidai ta bamu sabulu tace suyi wanki,duk ranar da zasuyi wanki to da gajeren wando suke zama,Ashe tana da yarinya yar boarding tana zuwa kuwa komai ya fara canzawa don ta tsane mu sosai wanki ma muke Mata idan be fita ba Duka ne zasusha haka zasuyi tayi suna sakewa,
watarana aka daukewa mama mai abinci(sunan da suke kiranta) kudinta ,a gaban su yarinyar ta dauka kudin,amma yar sai tace’ sune suka dauka,haka ta kamasu tayi ta jibga kuma ta koresu, gashi dare ne Amma a hakan ta koresu, sunyi kuka sun gode Allah,suna cikin tafiya Basu lura ba zasu tsallaka titi daya ne ya fara tsallàkawa mota ta bigeshi,dagudu dayan yaje Yana Kiran sunan mus’ab,
Kallanta yayi yace kina ganewa ko? Kin kuma gane suwaye yaran?

Kai ta daga masa, mas’ud ne ya cigaba,

yace” bayan an Kai mus’ab asibiti anyi mai treatment mutumin yace mu fada masa inda iyayen mu suke, fada masa komai nayi yarda muka tsinci kanmu da kuma yarda matar nan tayi masa sharrin sata,baice komai ba, yayi shiru yace’ Yana zuwa, baidawo ba sai washegari har lokacin kuma mus’ab bai far fado ba, sai kusan Azahar sannan ya farfado mutumin ne ya siyo mana abinci muka ci muka koshi sannan aka sallamemu, mutumin ne ya dauke mukaje hotel din da ya sauka shine yamana wanka yasama sabbin kayan sannan yace’ mujira Shi zai je ya dawo zamu tafi gidan Shi,muna zaune kuwa yaje ya dawo,
Tambayar sunan mu yayi muka fada masa,Amma duk yarda Akayi mu tuna sunan babanmu mun kasa,daga karshe ma kusan haukace masa mukayi ganin haka yasa Shi yin shiru,har mukayi bacci, bamusan mun iso ba ji mukayi ana tsashin mu,dare lokacin yayi,gida babba, part uku ne a gidan sai kuma wani Katon parlour, parlourn muka Shiga,ganin mukayi kowa Yana zaune yana kallo,ga kuma yara da manya,tasowa sukayi suka masa sannu da zuwa zuwa yayi ya zauna,mudai munja mun tsaya ganin babu Wanda ma ya Kula damu,sai da suka natsu sannan ya kalle mu yace’ mus’ab da mas’ud ku karaso ciki mana,karasowa mukayi muka gaida wasu Mata guda biyu,Amma ko amsawa Basu yi ba,dayar ce ma ta amsa dakyar,a haka ya gabatar damu a wurin yayansa manya daga nan kuma ya bayar da labarin mu, sannan kuma yace’zamu zauna a wurin Hajiya itace babba ba yarda ta iya ta amsa da tou.
Tundaga nan rayuwar mu ta kuma sauyawa don wata irin ukuba ake mana a gidan bamu da gata sai idan Daddy yana nan Wanda ya dauko mu Kenan,ko wanne irin aiki da kika sani munayi yaran gidan ma sun tsane mu har ta Kai ta kawo duk wani abun laifi Akayi a gidan mu ake cewa munayishi, dukda muna makaranta amma a kafa muke zuwa mu dawo a kafa gashi gidan Duka Matane yaran da manya ba maza, Mata shida yayan Hajiya babba sai kuma guda hudu yayan Anty, yayan Hajiya guda uku sun girmemu biyu kuma kusan sa’anin ne sai guda daya shekara hudu, yayan Anty kuma daya shekara hudu dayar kuma yar karama ce shekara daya,sai biyun kuma sa’annin ne da sa’ar mu dayar kuma ta Dan girme mu,Amma kaf cikinsu babu wacce bata Rena mu ba,da zaran mundawo a makaranta to mune komai na gidan kafin mu tafi islamiyya sai mun wanke uniform kaf,idan mundawo kuma mi goge,idan akace weekend yayi Bama Zama sai munyi wankin gida
gidan babba ne sosai Amma sai mun wanke Shi tas,kuma babu Wanda ke raga mana,abinci wataran sai magen su taci ta rage zamu ci,a haka mukayi shekara daya cib a gidan.
Watarana muna aikin wanke gida mun zuba klin dayawa a tsakar gidan muna wankewa babbar yar tazo wuce wa santsin ya debeta ta fadi, aikuwa mezanyi Banda dariya nayi ta dariya abina, aikuwa tana tashi ta wanke ni da mari,zata Kara taji an rike hannun,a fusace ta juyo wani yaro ta gani befi shekara 11 ba amma Yana da tsayi don zai kusa kamota,kallanshi takeyi

tace’ yaushe kazo ko kallanta beyi ya zo ya daga ni ya kama hannun mus’ab muka tafi,Ashe shima Dan gidan ne ba anan yake da Zama ba a Spain yake, tunda yazo ko ansamu aiki bamayi,sai dai masu aiki suyi, ahaka yagama hutun Shi ya koma, yana barin gidan shikenan kuma komai ya dawo ma,bautar tafi ma ta baya kullum ana kakaro mana aikin yi,sharri kam mun sha Shi ba laifi.
Ahaka muka gama secondary school lokacin muna da shekara 16 a lokacin anyi auran wasu daga cikin matan duk manya basa nan sai shida dasuka rage,aiki ya Dan ragu Amma de dukda hakan muke yin komai a gidan Banda girki, shikuwa Abdulshakur Wanda ake kiransa da binaif mukuma muke cewa BB big bro,mamansa bata gidan har yau kuma bamusan inda inda take ba kuma shima bai fada mana ba……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button