A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’daman nasan kece ai kowa yafita sai ke,ke kullum sai kin tsaya kinyi sallah ko?kinga yau banshiga ba ko? Wallahi makara nayi fa shine aka bani wanan aikin nikuwa naki Shiga class,kinga nagama bari nazo nakai wannan Kaya sai mu tafi tayi sauri ta tafi, Ummusalma kawai kallanta take har taje ta dawo suka fara tafiya,kamar daga sama taji Ummusalma

Tace’ meke damunki???
Juyowa tayi ta kalli ta,bata taba zata wani zai iya gane damuwarta ba musamman ma Ummusalma datake ganin kamar batda damu da kowa ba amma kuma sai taji sabanin haka,bata kalleta takuma maimaita Mata tambayar
Wani hawaye ne ya zubo Mata da sauri ta goge kar tagani yake tayi sannan

tace’ bakomai kawai de Babane beda lafiya shiyasa,
Ummusalma kallanta kawai take kallan nan na ban yarda ba,Amma de bata furta komai ba,daidai nan drivern ta yazo,Jakarta ta bude ta Ciro kudi taba

tace’uhm
Kallanta Neena ta tsaya yi batareda ta amsa kudin ba, hannunta ta jawo tasa mata kudin ta Shiga mota ta tafi
Tana nan tsaye har motar ta bacewa ganinta hawaye ne ya zubu kan kuncinta ta kalli kudin

tace’ Nasan zaki kewata dayawa Amma daga yau bazaki sake ganin na ba am sorry Ummusalma,
Tana magana tana goge hawayenta,sannan ta kama hanya ta tafi..

????????????????????
Yunwa take ji yau bata biya ba eatry taci abinci ba kodan da wanne ma kudin zataci bacin duka tabawa Neena,
A zuciyar ta

tace’ komai yake damun ta?gashi bansan gidan suba danaje naji ko me ya faru da ita ko wannan Dan iskan saurayinta din nan ne da yake takura mata?
Juyi kawai take tana tunanin Neena,har ta fara bacci sai ga Yusuf da yaseer sun shigo kasancewar yau ba islamiyya,suka tashe ta ta masu zanen su bayarda da iya haka ta tashi, taje ta bude wata kofa a cikin dakinta suka Shiga kwaso kayan drawing din sannan ta bude musu balcony dinta na dakin suka zauna ta kalli yaseer batare da tayi magana ba, da Shi Kenan zata fara don haka ya gyara zama ya fara zayya no Mata mutumin da zata zana masa,
Tunda yafara take ganin wannan zanen nasa hauka ne kawai Amma kuma ga mamakinta sai taga zanen Yana making sense har taji interest Akan zanen sosai,har ta Gama bayan ta Gama ta kalli zanen sosai ta itama mutumin jiki ya Mata kyau bakan ba, tana kallan zanen taji yaseer Yana cewa yauwa na manta Yana irin wannan abinnaki(tusar jaki) asamar girarsa Saida ta diga taga yamafi kyau.
Yusuf ne ya matso

yace’ saura ni yaya,
Zana masa tayi sannan suka maida kayan drawing din suka ajje zanenna su daman a nan suke ajjewa sannan sukayi sallah a dakinnata….

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????

????A BAKIN WAWA????

    _Akan ji_ _magana

      3

Fitowa tayi ta barsu a dakin, ko da ta sauko taga ba kowa a parlourn, kitchen ta nufa nan ma ba kowa tsayawa tayi tana tunanin me zata ci,har ta bude fridge sai kuma ta nufi store ta dauko indomie,cikin lokaci kankani ta gama abinta,tana cikin juyewa Indo ta shigo,da sauri taje taza amsa ta karasa juye Mata,amma ko kallo bata ishe taba,ta gama juye abinta ta tafi,Kallan ta Indo ta tsaya yi har ta fita ta rufe kofar sannan ta sauke ajje yar zuciya tana

cewa’ ohhh matar da da ko ruwan zafi zata sha sai an dafa Mata amma yanzu itace keyin komai da kanta cikin ko harda wanki taabbdi,
Takarashe da tabe baki ta fara hada kayan wanke wanke.
Koda ta fito sai ta tarar da Mama tana waya cikin harshen fillanci,bata kalleta ba ta haye sama abinta,Shiga tayi taga Yusuf da yaseer sun dauko kayan wasan su sun hargitsa dakin,kallo daya ta masu taje wurin carpet dinta inda aka sa kujera da center table ta zauna,juyowa tayi ta kallesu suna wasan su alamar basu ganta ba Kenan,tasan hankalin na gun wasa Basu ga abinda ta shigo dashiba don da sun gani tasowa zasuyi suce sai sun ci ,kallan su ta cigaba dayi,daga bisani ta tashi ta je kusa dasu kawai hannunsu ta rigo ta zaunar a gaban abincin sannan taje ta bude fridge bakomai a fridge sai ruwa,Itakam bagadaya tama manta badan yanzu ba ta bude ta gani,ruwan ta dauko ta zo ta zauna, kowa ya dau spoon suka fara ci, Yaseer ne ta

yace’wai yaya salama a’ina kika iya abinci yanzu da naga Baki iya ba, amma yanzu kuwa idan kikayi kamar bake ba eh?a’ina kika iya?
Yasan bazai samu amsa Amma kuma de tambayar sai yayi ta indai har ta dafa masu wani abu, Yusuf ne

Yace’ kaifa ka fiye surutu,komai sai kayi magana,ni Bana san surutu,

To sannu yaya babba ai sai Ka hanani mutum da bakinsa a hanashi surutu
Kaikasani,
Har suka gama sunayi,ita dai bata tanka masu ba,a haka suka gama Yusuf ya kai kwannan kitchen ya dawo sukaci gaba da wasansu,ita kuma wanka ta Shiga,koda ta fito basa dakin kuma tasan zasu dawo wani Abu akaje daukowa,sai ta Gama tunaninta kamar kullum don kusan shine yake cinye Mata lokaci,a gurguje ta shirya cikin wata Abaya maroon sai tayi rolling da mayafin rigar,tasa takalmi plate ta dauka jaka ta fito ko powder babu bare kuma janbaki, lipgloss kawai tasa shima dan kadan badayawa ba,Shiga dakin su tayi taga suna neman abun su daman tasan wasan be kare don indai babu islamiyya to haka suke wuni wasa har magriba,karasawa wurinsu tayi a hankali

tace’ yusseer(Yusuf da yaseer)
A yare suka jiyo ganinta da Shirin fita sunsan metake nufi,a gurguje suka fara cire kayansu zasu canja,itakuma fita tayi dakin Abba knocking tayi,taji ba,a amsa ba tasan baya nan Shiga tayi taje tadau kudi,ta fito ta sauka kasa, Sameera tagani zata fita itama taci kwalliya kuma tasan be wuce gidan su kawayeba a yarda take cewa mamannasu,Amma itakam tana tantama Akan fitanta kwanannan,ace duk Thursday, Friday dakuma weekend mutum bayayi a gidan su,tabe Baki tayi kawai,tasa Kai zata fice Mama dake kallanta cikin kakkausar murya

Tace’ina zakije baza ki fada min ba ehh?
Shiru tayi bata tanka ba Amma de bata fita ba

Wai ba magana nake maki ba iyye?nace ina zaki je?
Namma shiru

At least kyafadi inda zakije ai gudun samun matsala ko kuwade,
Tafada a Dan raunane,
Namma bata tanka ba kuma ba ita take kallo ba juyawa tayi tana kallan kofa kamar ba da ita ake ba daidai nan su yusseer suka sauko da gudunsu sukayo wurinta ganin da tayi yasa ta bude kofa suka fita,
Mama kuwa ta bude zatayi magana Kenan sai ji tayi an rufe kofa,Baki a sake,

Tabdijam dole ma nayi maganin yarinyar nan don wallahi bazan yarda ba taabb kaji yarinyar,inaaaaa bazan yarda ba ai,komaea tayi ta zauna ta dauki waya ta Kira yayarta.

????????????????????
Driver na hango ta fito ya taho da saurinsa,durkusawa yayi zai gaida ta ta Mika masa hannu,alamar ya bata key di bata yayi ta tafi ta barshi a wurin,tashiga ta kunna motar alamar tana jiran su,sukuwa fada suka fara ko nacewa shine a gaba ganin haka yasa driver tashi da sauri yazo

yace’ kaga Kai Yusuf Shiga baya Kai kuma yaseer Shiga gaba, Idan zaku dawo sai daya ya dawo gaba daya ya koma baya, ba shikenan ba?Amma kuzo jay tafada de
Shiga sukayi kuwa don sun yarda da wannan shawarar,suna shiga kuwa taja suka fita, a motar sukadai suke rawar su kuma suke kidansu agogon motar ta kalla taga 5:30 tasan kafin su dawo magriba yayi,wani store ta shigo tayi parking inda ake parking mota.
Jerawa sukayi suna tafiya sun sata a tsakiya,sun birge na birgewa wasu kuma suce ko kyau(daman dole ba kowa ne zaka masa ba Idan kana da masoya dole daman kana da makiya haka nan rayuwar take).
Siyyaya sosai tayi na kayan da bata dashi,ta siyowa Neena chocolate dayawa itakuma ta siyo biscuits
Yusseer kuwa ai anjida Kaya harda na wasa kayan zaki kuwa ba,acewa komai haka suka gama aka masu total,ta biya suka fita,dagannan sukaje suka sha ice cream sanann suka nufo gida, lokacin da sukazo masallatai dayawa sun idar kasancewar a hankali take tafiya kamar mai tausayin kasa.
Bakowa a parlourn da suka shigo,su suka baje anan ita kuma tayi dakinta sannan taje ta kuma daukowa Sauran kayan,sallah tayi,ta cire kayanta tasa na bacci tadauko Qur’an ta karanta sosai,kuma tayi hadda har Akayi Isha tayi sannan ta kwanta,ta Lula cikin tunanin neman mafita,yau ko adduar ma batayi ba tayi bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page