A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
????????????????????
Daddy tsaye a bakin kofar part din su Binaif yana knocking,ya jima a tsaye a wurin tun yana yi ahankali har sai da yayi da karfi tukunna, yaji alamar tafiya sannan ya hakura,Yana budewa yaga daddy tsugunna wa yayi ya gaidashi, maimakon ya amsa sai,
yace’ meye sunan??
Kallanshi yayi alamar be gane ba,
Daddy yace’ ita waccan kurman,ya sunanta,
Bakinshi na rawa ya furta Ummusalma Muhammad,
Iyayenta ba,
Sun rasu daddy,
Daddy be jira cewarsa ba kawai yasa kai ya juya ya shiga mota, binaif yana tsugunne har Daddy da driver suka tafi, sannan ya tashi ya koma ciki daman wanka yake,Yana so ya fita ya shaida mata, abinda ake ciki, jiya har ya kwanta yaje ya karbo yar karamar wayar da ta turawa Daddy sako, Sannan ya karbi address din tsohon gidan su,yaje ya zauna a wurin masu gadin unguwar wanda yawanci da daddare suna zama suyi ta fira anan ya zauna yaturawa Mama text,Yana nan zaune yaga police ko ba’a fada masa ba kuma yasan tracking numbern akayi.
Shiryawa yayi cikin bakaken suite ya bade jikin shi da turare,ya dau yar jakar ya fito, direct dakinta ya nufa lokacin tana kwance babu abinda takeyi sai tunaninsa a wannan lokacin, knocking yayi a kofar dakinta,hijabi ta dauka ta fito ganinsa da wannan shigar yasa,
tace’ ina zaka je haka? Ba Daddy ya hana ka fita ba?
Wani irin makirin murmushi yayi,
yace’ fita ta zama dole,kuma batun Daddy kawai kyaleshi yama manta, takardun nan zaki bani,na company guda daya,
Juyawa tayi ta dauko masa bata gani na kowanne bane kawai daukowa tayi wanda tasan na company daya ne, bashi tayi ya kalleta cikin ido ya sakar mata murmushi
yace’ sai na dawo,
Tsayawa tayi a wurin,ta daskare wannan killer smile din dayayi ya tafi da imaninta, juyowa yayi
yace’ Ba Allah ya kiyaye ba adawo lafiya ko? Shikenan to tunda ba za’a min ba,bari nayi,
Muryar ta ya kwai kwaya
yace’ Allah ya kiyaye Allah ya dawo da kai lafiya Allah kuma yabda sa’a byee sai Ka dawo,
Bai jira cewar ta ba ya tafi kuma daman yasan ba abinda zata ce,
Batasan lokacin da tayi murmushin ba, sannan ta rufe kofarta ta.
zama tayi a bakin katifar ta,tana murmushi,
tace’ wai shi bai yarda ba magana ta yayi to nidin haka nake magana ne? Kawai sai tayi dariya abinta,
Yanzu kam ta lura yana abu kadan zatayi dariya idan ma batayi dariya ba zatayi murmushi, ko jiya da daddare sai da yasata dariya, kwanciya tayi tana cigaba da murmushin ta ita kadai.
Yana fita ya ansa key a wurin drivern gidan ya fita,bajjima da fita ba yaji wayarsa na ringing ganin sunan Daddy yasa shi dagawa yana dagawa kuwa yaji Daddy yace' duk inda kake kayi gaggawar zuwa masallacin bayan layin mu yan zunan kayi sauri ina jiranka kar ka bata min lokaci,
Ya kashe wayarsa,kwana kawai ya karya ya shiga bayan layinsu mutane yafara gani a wurin masallacin tun kafin ya karasa, karsawa dai yayi yasamu wuri yayi parking sosai yaga motocin mutane da dayawa a wurin babu abinda ya kawo sai ko daurin auren abokin Daddy ake? Ba mai bashi amsa haka ya shiga cikin mutanen har yayi nasaran shiga cikin masallacin yafara hangen inda zai gano Daddy amma kuma yana cikin mutanen hakan yasa shi neman juyawa ya koma don har ya shigo cikin masallacin sosai, Daddy kuma ya hango shi, hakan yasa yayiwa liman magana, yana dhirin fita yaji an ambaci sunanshi kara daga kafar da zaiyi yaji ance Ummusalma Muhammadu guri kuwa ya kaure da fatiha, idan kunansa yaji dai dai cewa akayi an daura masa aure da ita. Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un.
Shi bama ta tashi yakeyi ba ta ita yake yi kawai tunanin ta yafarayi hankalinsa bai dawo ba sai da yaji wani kawunsa nacewa ai ga angon ma. zo nan ayi hoto, suka janyo shi,wani kuma yace’ ohhh yaran zamani ranar aurenka da kayan nasara aka yi shi ni bantaba gani ba sai kace bikin kiristoci kai jama’a,
Wani yace ango ranar aurensa dariya yake shikuma wannan dakum-kumin murtuke fuska yayi, yana jinsu dai suna jansa har aka fito harabar masallacin,hoto akayi ta dauka wani yayi yake wani kuma kawai gashi nan dai ga shinannan ne…..
By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana
19
Driving yake amma gaba daya jikinsa yayi sanyi hankalinsa kuma ba’a driving din yake ba, tunani yake akan wannan auran, yadai san Daddy be sanar Mata ba, akan me kuma zaiyi wannan abun, aure fa ba abin wasa bane haka kawai ‘ya ba tashi ba ba komai ba, “Ya ilahi Daddy why??
Abinda da ya furta lokacin da yayi parking a bakin gate dinsu, sai dai kuma ya kasa fita yana zaune kawai ya dafe kanshi da yafara ji yana sara masa, horn yayi aka bude masa ya shiga ko gama parking baiyi ba ya fito key din ma a jiki ya barshi, a parlour ya baje ya kwanta yana wani irin tunani na daban, shikadai yasan me yake sakawa yake kwancewa.
Ya jima a wurin ahaka har wurin 12 yana nan bai motsa ba jin wayarsa na ringing Allah yaso bai barta a mota ba ya tuna sanda Daddy ya kirashi da ita ya fito a mota,shi dai baisan sanda yasata a aljihunsa ba sai ji yayi tana ringing.
Daukowa yayi ganin number da har zai share sai kuma yayi tsuka ya daga, abinda aka sanar dashi yasashi saurin mekiwa,bayan ya kashe wayar shi yama manta da abinda ya fita yi badan an kirashi an tuna masa ba, daki ya Shiga yayi refreshing sannan ya fito key yafara nema sai kuma yayi tunanin ko ya barshi a mota ne .
✨✨✨✨✨
“Yanzu Adamu abinda kayi ka kyauta Kenan ko me? Uhm, yarinyar nan fa ba ‘yarka bace, sannan da kace min iyayenta sun rasu ita bata da me riketa ne ko me? sannan kuma wannan yaro ba mace bace da zakayi masa auren dole, Ka duba mana wannan lamarin, gashi kuma kace min yarinyar kurma ce,kawai don san a cuceta ko kuma me?
Kanshi a sunkuye yake bashi da daman tankawa yasan bai kyauta ba shi kawai abinda zuciyar sa ta Raya masa Shi yayi,
” Ba magana nake ma ba, kana jina kayi shiru ka kyale ni ko? Wato yi ki gama ko?
Bude Baki yayi yace’ amm… amm.. umma ki..
” Rufe min baki wani amm amm umma,daka san zaka bani hakuri ka aikata ?
Wani mutum ne dake gefen Umma,
yace’ kiyi hakuri kuskure ne mun rigada munyi,kuma kinga bamu da ikon da zamu warware wannan aure, har sai mijinta ya saketa tukunna, Allah kuma baya san saki, umma kiyi hakuri kuma watakila ma dalilin aure nan sai kiga Allah ya shiryeshi,…
” aww da mai yake aikatawa? Ta kastse shi,
Daddy yace’ umma nema yake ya lalata masu yarinya fa a idona nasha ganin hakan tana faruwa shiyasa ma kikaga kawai na yanke wannan hukuncin.
Umma tace’ ehh lalle ne shi Audushakurun Kenan? To bari kaji ko duk jikina kunne ne bazan yarda ba,kawai dai ka cuci yarinya kawai shine magana. Kai kuma dan kaga inajin maganar ka shine aka dauko ka kana can wata uwa duniya amma kadawo saboda wannan auren ko? To shikenan ya zanyi kun dakeni kun hanani kuka bazanyi magana ba,kun nuna min ni ba abokiyar shawara bace shikenan ai aikin gama ya rigada ya gama.
Sai tayi shiru,Suma shiru sukayi babu wanda ya kara magana, sai can ta kalli Daddy,
tace’ kaje ka dauko min ita yarinyar,bazan laminta ba zamanta wannan gidan,kashe ta zasuyi daman ga aba kurma,
Daddy yace’ umma da kin barta acan din inaga hakan…
Zaifi ko? Yanzu ma ja zakayi dani ko? Baka sanar dani ba auren sannan kace zamanta a wannan firin din zaifi. Bana boka bana Mallam amma ko kaffara banayi na tabbata wallahi wannan shegun matan naka ne suka hada tuggunsu da munafinci suka fada maka,Kai kuma ka hau dokin zuciya ka dauka. To billahillazi bazan dauka ba,kai da kaina ma zani gidan bari gari yayi sanyi zanje na dauko ta,kuma yarda baka fada min kayi masa aure ba koda subutar Baki karka kuskura kafada masu tam.
Tashi tayi tana dingisa yar kafarta