A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ an tabbatar mana da yaranka hudune biyu Mata biyu Maza ita kuma sunanta Ummusalma hakane munsa da wannan labarin,

Wannan Karan bai iya basu amsa ba don bashi da tacewa yasashi cewa lokacin ku ya cika, wani yace’ a,a ranka ya dade da saura fa.
Sai dai ko Jin shi ma baiyi ba ya zuge glass yayi gaba abinsa, tashin hankalin da ba’a sa masa rana.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Karfe tara ta tashi ganin dakin ba haske dayawa yasata kallan dakin dakyau ta juya dayan barinta amma bayanan ita zatonta yana toilet,shiyasa ma tafara gyara dakin fita tayi ta amso mopper da tsintsiya wurin mai aiki tare da duster tazo goge side drawer taga Papern da ya ajiye mata dauka tayi taga menene aciki,

The beautiful morning dew and the lovely morning hue are symbolic of mi amor for you. Good morning mi precioso .

Rubutun yafi komai burgeta yarda aka tsara shi daki daki kai kace gasar rubutu yaje, numfashi ta sauke ta nade ta ajiye a wurin kasan pillow ta cigaba da aikinta sai dai kuma tunaninta yafi karkata ko yama ci abinci ya fita? Ko ina zaije bai sanar mata ba oho?duk yarda ta so yakice abin ya ci tura ta kasa . ko da tagama wanke toilet tayi,tayi wanka ta fito kallan kanta tayi yarda gashinta ya taso wannan three babies din da ya mata kuncewa tayi ta taje kanta dukda tasan ba tajewa zatayi kamar yarda ya taje mata ba haka ta taje Shi ta kulle a tsakiyar Kai, sai da ta shirya tsaf cikin doguwar Rigar ta kamar kullum ta yafa mayafi ta fito harta fita ta dawo ta dau wayarta ganin missed calls dinsu mus’ab rututu yasata Jan tsaki

tace’ yanzu haka damuna zasuyi da surutu bazan kiraba,

Umma tana zaune a parlour tana kallo,gaisawa sukayi Umma tace’ kije kice abinci,
Tashi tayi taje taci abinci ta dawo ta zauna suka ci gaba da kallo,Hausa film suke kallo ita ba ma’abociyar kallan Hausa film ba amma wannan da akeyi yaja hankalin ta sosai tana kallo sai dai kuma rabin hankalin nata yana kan kofar shigowa ita gani take bajimawa zaiyi ba, gaba daya kewansa ya addabeta yau kadai gashi bata da numbern sa,idan ma tana dashi tace masa me?
Umma taji

tace’ Salamatu ungo nan danno min waccen ‘yar zaki ga ansa filawa da kan mutum sai mota guda daya, yawwa donnuta naji shiru kuma ga rana tana neman yi,

Karban wayar tayi tana cikin dubawa taga numbern sa dayake ta taba kiranshi a wayarta, number ta kalla har zata dauka a wayarta sai kuma kawau ta hardace ta tanemo mata ta danna kira, wayarta ta dauka tasa numbern shi tayi saving,

Suna zaune sai ga wata Mata tazo gaisawa sukayi gaishe da ita Ummusalma tayi Umma tace’ ai wannan itace take bin Adamu baban audushakuru Kenan sunanta Safiya daga ita sai Rukayya Allah ya jikan rai itace auta, Kara gaidata tayi, sannan ta tashi ta basu wuri tare da daukan yarinyar da suka zo tare dukda katuwa ce zatayi shekara biyar.

Numfashi Goggo Safiya tayi tace’ Amma yarinyar nan da’alama Umma tana da nutsuwa,

Umma tace’ hmmm amma bata fara’a ba?
Batayi magana ba don tasan halin kayanta shiyasa tayi shiru,

tace’ Umma bari yazo ya bada kudin lefen matar shi,

Umma tace’ shashanci banza Kai wanne kudi kuma, dhi Wanda ya daura auren ne ai zai bayar dhi yace yana santa ne ko kuma shi yace a daura masa aure da ita ehh?

Tace’ haba Umma kiyi hakuri mana,a ganina idan yayi komai da kansa zaifi rike auren da daraja kina gani fa yawancin eanda akayiwa auren gatan nan basa rike matar da daraja Umma aganina a barshi yayi komai da komai yarda zaiji jiki kudin sa zaiyi kuka kinga idan ya tashi zai rike ta hannu biyu kuma ma Babansa ya fada min labarin ta kinga kuwa wannan ne kadai gatan da zamu bata,Umma mazan yanzu ba irin nada bane nima zan iya yiwa Binaif komai kodan bashi ba kodan albarkacin mahaifiyar sa,Umma kiyi hakuri don Allah,

Jikin Umma ne kuma yayi sanyi da wannan kuwa don wannan tana gani ma nan da aka yiwa wani yaro aure a kusa da ita ma yaran ko wata biyu ba’ayi ba ya saki yarinyar gaskiya ne auren gata ma yana sawa a ki daraja mace
tace’ shikenan to ai kece daman uwar ‘da, kuma ki jamasa kunne idan ya kuskure ya tabo ni wallahi sai dai ya wayi gari yaga matar sa a can Ilorin baruwana ni ato,

Haba Umma kiyi hakuri mana kefa ana maki lefi wataran a rasa ma me aka maki don Allah kiyi hakuri ku rabo lafiya Umma,

Hmmmm to naji,
Daga nan kuma aka fara tattauna yarda zasuyi daman wurin aiki zata je nurse ce kuma sai karfe biyu zatayi shifting shiyasa ma tace zata zo yau din.

A dakin kuwa sosai yarinyar ta burgeta gata da surutu ganin kanta a tsafe gashi kuma tubarkallah dashi yasa tace’ ya sunanki?
Yarinyar tace sunana Rukayya Amma ana cemin Ummi shikuma uncle Binaif haka yake cemin wai Anty Ummi,
Murmushi tayiwa yarinyar tace’ sunan maman sa ai kikaci shiyasa yake cemaki Anty,
Yarinyar tace to yanzu tana ina?

Ai ta tafi bazata dawo ba har abada sai de muma mu bita,

To yaushe ta tafi?
Ta jima da tafiya ai,
Tace’ kinga Bari na maki kalba ko? Kinga kanki ba kitso kuma karfa Monday tayi a duke ki a school ko?

Da zafi fa nidai bana so ta fada tana niyyar tashi ta tafi janyota tayi tace’ a,a Anty ummi zan fa baki alawa dayawa kina so?

Daga kai tayi amma badan tana so ba, tashi tayi ta dauko Mata Allah yasa tana da sauran Wacce ta taho da ita daga London tama manta da ita sai da ta ganta a cikin Jakarta sannan ta tuna da ita.
Bata tayi tace’ amma sai kin yarda idan baki tsaya ba bani Kaya na zakiyi, ribbon din da ya sayo mata ta diba tayi tayi mata kamata Mata Kan dashi ta shafa Mata mai, kan yayi kyau sosai gashi mai laushi itama yarinyar har aka Gama batasan anyi ba don alawar ta take sha ba ruwanta. Kallan kallanta tayi a madubi tace’ laa kinga nayi kyau yimin hoto,
Murmushi tamata sannan tayi Mata hoto sukayi wani tare,itama ta cire mayafin kannata a haka sukayi ta hotuna abin su sai da Goggo safiya tazo tukunna suka dena,

tace’ lalle kin ciri tuta irin wannan gyaran kai haka,
Samun kanta tayi da murmusawa irin naji kunyan nan kamo hannunta tayi ta zaunar akan kujera itam ta zauna,

tace’ sunana Safiya zaki iya cewa Anty safiya ko sister ok?
Shiru tayi kafin tace’ Ummusalma nasan cewan Binaif zai rike ki da mutunci da amana, kema don Allah ki rike shi dahakan,
Dagowa tayi ta kalleta, murmushi tayi tace’ selfish ko?
Shiru ta kuma tayi daga bisani kuma,

tace’ kiyi hakuri da halin Binaif bani na renashi ba kanwata ce labarinsa kawai nakeji daga wurinta duk wayar duniyar da za muyi sai tace Binaif kaza Binaif kaza tana mutukar San shi, ita tafi kowa sanin halinshi sai kuma ni da take bani labari,Yana da dadin zama idan ka iya zama dashi,wani lokacin Yana da san barkwanci wani sa’in kuma magana ma baya so, baida san kanshi ko kadan sannan idan ranshi ya baci to bazaiyi magana ba koda kuwa yana Jin yunwa kuma bazai je ya zuba ba, haka yake wani irin juyyayyen mutum ne shi, abinda nake so dake shine Don Allah kiyi hakuri da kome zaki tarar ko mekyau ko marar kyau, hakuri shine komai, dan hakuri shine auren ma gaba dayansa musamman na yanzu maza basu da tabbas bazan yabe shi ba don Yana ‘dana sai dai cikin kaso tamanin haka halinsu yake, kiyi hakuri wannan hakuri Shi kadai zan iya baki shi kinji ko?

Batasan mezatace ba magana zatayi tace ta karba kome? Me kuma take son ji game dashi ? Abinda yake so? Me yake burgeshi ? Kome? Kallanta tayi ahankali kamar me tsoron magana

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button