A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
yace’ kinga Wanda kika sani ne?
Kallanshi tayi da mamaki,da’alama ya jima Yana kallanta bata Kula dashi ba,
Murmushi yayi yace’ karki damu kawo nakai maki,amma sai kin fada min suwaye su a wurin ki.
Yafada Yana shigowa cikin kitchen din, numfashi taja ahankali cikin muryan da shikadai ne zaiji
tace’ kannai na,kuma Bana san su ganni,don na tabbata yanzu nemana sukeyi.
Murmushi yayi yace’ to shikenan anything for you,
Yafada Yana daukan tray din.
Yana fita kuwa ta tafi dakinta ta Shiga wanka,Da murmushi dauke a fuskarsa ya fito ajje masu tray din,
yace’ sannunku,
Yusuf ne ya tashi ya Mika masa hannu suka gaisa ,sai yaseer shima ya Mika amsa,ummu ta gaidashi,ya amsa ganin yarda Yusuf yake cika yake batsewa yasashi kallansa dakyau,
yace’ abokina lafiya kuwa? Zo muje waje kasha fresh air,
Yafada Yana yakamo hannunshi,shima Yusuf din beyi musu ba ya bishi ta kitchen ya bi dasu, a garden suka zauna , sanan yaje ya zubo masu abinci da lemo, don yau ji yayi Yana san cin girkinta dukda be taba ciba amma Yana da yakinin zaiyi dadi, ya ajje masu a tsakiya yace’ bismilla,
Yusuf kallan abincin yake dambun couscous, an barbadeshi da dambun nama, baisan sanda wani murmushi yayi escaping lips dinshi ba, Yana mai kallan abincin, Banaif kallansa yayi,
yace’ lafiya kuwa?
Numfashi ya sauke Yana mai Kara murmusawa yace’ lafiya qalau kawai dai na tuna wani Abu ne,
Can u share with me? Yafada Yana Kai loma bakinsa,
Murmushin ya kuma yi,
yace’ Favourite food din Yaya tane, idan kana so kayi bribing dinta to Ka kawo mata dambun nama,ko na couscous, Amma fa idan na dambun couscous ne to sai Ka barbada masa dambun nama,
Wata yar kwallace ta taru a idansa ya gogeta sannan yayi murmushi,
Yana cigaba da kallan abincin, shima ajje spoon din hannunsa yayi dukda Loma daya yayi kuma abincin yamasa dadi sosai,
yace’ ko zan iya sanin me Yaya tafi so da wani abu daga cikin labarin ta? Ya tambaya da murmushin da yake karawa mutane nutsuwa,
Kara goge kwallan idon sa yayi sannan ya Kai loma daya bakinsa,wani murmushin ya kuma yi
yace’ lokacin I was 10 Amma idan yaya tayi girki to nasan girkinta saboda dadin Shi,nida yaseer mukanyi mamakin inda ta iya girki haka lokaci guda,
Yaya tana san wasa,zuwa park,ice cream, biscuit, drawing, games, basketball, da sauransu,Amma tana san surprise tana so a mata itama kuma tanayi,
Shiru yayi ya budi Baki zaici gaba yaji wani kamshin turare ya daki hancinshi,lumshe Ido yayi ya bude yace har yau bansan sunan wannan turaren ba amma nasan irin shi Yaya take sawa,
Shiru yayi yakuma yin wata lomar zaiyi magana yaji yaseer nacewa” idan labarin Yaya ne bazai taba karewa ba,
Ya karaso shima ya zauna, yacigaba, ya kalli Binaif,
yace’ meyasa kake San Jin wani abu daya danganci yayarmu?
Murmushi yayi yace’ saboda tana San abinda nake so,tana san favourite food dina kuma ance yawancin masu San abinci iri daya, to halin suma zai zo daya haka ne?
Kallan juna sukayi suka yi wani murmushin da iya su kadai suka san shi, yaseer,
yace’ bamu Sanka ba, amma koma meye kana San Jin wani abu daya daganci yayar mu hakan na nufin u mean alot to us,muna San duk wani mai San yayar mu,
Shiru yayi Jin muryan Shi zata fara rawa, Yusuf yacigaba,
yace’ idan muka baka labarin Yaya daidai yake da kaima Yayane a wurin mu, amma bamu San ya zaka dauki maganar Tamu ba.
Shima daga nan shiru yayi,ganin sunyi shiru yasa Shi cewa” to yanzu ina Yayar take??
Wani irin murmushin takaici Yusuf yayi yace’ muma bamu sani ba,karshen ganin mu da ita yau kimamin shekaru shida da wata daya da kusan Sati Kenan,babu ita babu labarin ta,
Lomar abincin da Kai bakinsa ce ta makale, yaseer ya bashi ruwa ya kora,
yace’ bangane ba?
Zaka gane ai,
Yaseer yafada sannan ya cigaba da cewa” tunda ta tafi makaranta London bamu Kara Jin labarin ta ba,sai ranar da zata dawo Nigeria suka hadu da ummu wacce muka zo tare ita, ta bata sakon gaisuwa sannan tace ta amsa numbermu, har yau muna jiran kira daga gareta har yau babu labarin zata ma kiramu din, sai dai tunda ta amsa munsan zata Kira,
Zuwa yanzu kanshi ya kulle sosai ,yama rasa wanni tunani zaiyi, kallansu kawai yake baikara masu wata tambayar ba gudun kar ya kuma fadan abinda zai Kara sashi cikin wani yanayin bayan Wanda ta saka Shi aciki again ga kannanta sun Karasa shi aciki, kallansu yayi yaga suna cin Abincinsu hankali kwance sunayi suna kora da lemo, ummu yazo,
tace’ kutashi mu tafi,na gaji wannan budurwa taka ta fiye surutu wallahi,duk surutuna ta fini, ta dameni ta shanye ai wannan ga shegen iyayi, ni bazan iya ba kutashi mu tafi bakuma zamu Kara zuwa gidan nan ba a toh kuna jina ai?
Ganin sun Mata banza yasata cewa da’ace na iya mota wallahi bawanda ya isa ya kawo min raini ban taka shiba,har wani ina cewa ku tashi mu tafi kunsamu gidan mutane wato kuna zira abinci sai kace gidan ku ko?
Yusuf yace’kin dame ni fah,idan zaki ci ki zauna kici nasan yunwa kike ji,
Kumbura Baki tayi ta samu wuri ta zauna spoon din da ya ajje ta dauka tana cika Baki, binaif kallanta yayi, yace’ daman fadan yunwa ce Hala ?
Ita sai anan ma ta lura dashi,wani irin kunya ne ya kamata
Girgiza Kai kawai tayi,ganin ya Basar ya jasu da hira yasa itama ta sake tana zira abinci, sosai suka ci suka koshi, sannan ya raka su wurin mota, ko sallama basu yiwa Fati ba Saida suka fito sannan ummu ta kirata ta fito sukayi sallama suka wuce, lokacin anyi kiran sallah la’asar don haka suna zuwa gida suka wuce sallah, da suka dawo kuwa wanka sukayi suka saka kayan shan iska,suka fice kasan layin su inda ake ball, badan suyi ba sai dan suyi kallo…
????????????????????
Da yamma ta fito ta zauna tana tunanin yarda zata fara aikinta hankali kwance lokaci yayi da zata fara gudanar da aikinta, lokaci yayi da zata nunawa duniya itace mai kudi ba wani Wanda ake cewa shine ba, lokacin mai da martani yayi,batare da sun sani ba. Murmushin takaici tayi shima ko second daya bayi ba ya bace, Allah Allah take wani satin yayi don ta gudanar da komai cikin sauki. Lumshe idan tayi tana cigaba da tunanin ta. Ga wata iska da ake kadawa gwanin ban dadi, doguwar Riga ce a jikinta wacce ta Mata yawa shiyasa ma iskar ke Shigar ta lungu da sako, sai wani mayafi da ta yafa akan rigar, tana zaune bata da alamar tashi, sai dai Jin wani Abu na motsi a jikinta yasata bude ido kafar ta duba sai ganin kadangare tayi Yana motsi alamar Yana so ya sauka ko ya tafi, ya jima tsaye a akanta yana kallanta Yana mamakin yarda zaizo ya jima amma bata San da zuwansa ba haka ma dazu a kitchen yayi, ganin bata Kula dashi ba kuma ga kadangare a kusa da ita yasa Shi daukan dan tsinke ya kada kadangare aikuwa ya hau kan kafarta azontanshi zatayi ihu ne yarda mata keyi Amma ga mugun mamakin Shi sai gani yayi tasa hannu ta dau kadangare ta wollo Shi wurin da yake bai sauka a koina ba sai jikin Shi,ai wani irin wawan tsalle da yayi tare ihu, yasata kallan wurin, kadangaren da ta wulgar ne a wurin, tsakanin sa da Allah tsoro yakeyi bana kadan ba, ita a tarihin rayuwar ta bata taba tunanin namiji na tsoron maciji bama bare kuma kadangare first time in history aikuwa me zatayi inba dariya ba ta kyalkyale da dariya, dariyarta take har cikin ranta,dariyan da ta jima batayi ba, itace harda su rike ciki tana dariya abin ba karamin dariya ya bata ba wai babba Kato dashi da tsoro, shikuwa rigar ya cire ya yar da kadangaren sannan ya maida kallansa ga ita, be taba ganin murmushin taba, kuma baitaba Jin labarin a wurin su mus’ab ba, daman ina zai ga murmushin ta da ba wani sabawa sukayi ba, Amma gashi yau yaga dariyanta, gani yayi dariyar ya nata kyau,kallan kurilla ya fara kare mata, bawata fara bace ta azo a gani amma za’a Kirata da fara,don farinta ma ya fara dishashewa saboda aiki, sannan tana da hancinta daidai,sai dai akwai ido tubarkallah dasu,sai kuma abinda ke Jan hankalin sa game da ita shine bakinta dan matsitsi, dashi, gashi kuma mai shape din love ne????, sai dimple dinta,