A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana kwance a Kan gado gaba daya ta kasa bacci tunanin Shi kawai take tasan yanzu yakai kololu a bacin rai,abinda bata so game dashi Kenan, wayarta ta dauko da tun sanda tazo take son Kiransa amma takasa gashi yanzu kowa yayi bacci Banda ita, wayarta ta janyo ta tana kallan sunansa da tayi saving dashi ko ta Kira? Danna Kiran tayi ta runtse ido tanaji tayi di sau daya tayi sauri ta kashe, tana sauke numfashi Kara dannawa tayi namma haka, sai da tayi biyar idan tayi ringing daya sai ta kashe,

Yana kwance Yana tsuka Jin wayarsa tayi wani munafikin flashing yasashi Kara Jan tsaki da karfi, sai kuma yaji anayi ba’a dena ba janyo wayar yayi Yana kallan number idan aka Kara Kira sai ya Kira yayi rashin mutunci wallahi,aikuwa ji yayi tayi wannan karan haske kawai wayar Shi tayi ko Dan ringing din ma batayi ba aka kashe, a zuciye kuwa ya Danna Kira,

Tana ganin Kiransa gabanta ya fadi mezata ce masa,har Kiran ya katse ba a dauka ba,wani Kiran ne ya kuma shigo sai da ya kusa katsewa ta daga tana saune numfashi,beji sautin komai ba sai numfashin da ta sauke, shiru yayi itama haka sai can ganin batazayi magana ba ya Shi

cewa’ da kinsan Baki da ta cewa kika kirani ? Kika katsemin bacci na mai dadi?

Wani Abu taji ta hadiye me kama da bacin rai, itama

tace’ tunda ni nafi kowa hauka sai na kiraka yanzu ko? To Bani na Kira ba, inaga Nafisa ce don ni ina parlour ma kallo nake sai yanzu dana shigo Naga wayan Yana ringing ita kuma ta Shiga toilet,

abinda ya hadeye yafi nata daci Jin maganar yayi wani iri wato Bama ita ta Kiraba,Shi Yana nan ya kasa bacci ita kuma tana can tana kallo,Jin yayi shiru alamar ya Shaka dayawa yasata cewa’ kayi shiru nikuma kallona zanje inci gaba daman Abu nazo dauka Naga wayar na ringing,

Takaicine ya sashi kashe wayar,zata sani ne ai zaya dawo ko? Allah ya kaimu lokacin,

Itama ajje wayar tayi wato tana nan tana tuna halinda zai Shiga shikuma Yana can yana bacci ko? Addu’ah tayi ta rufe Ido aikuwa bacci ya dauke ta,

Shima dakyar baccin ya dauke shi,don ma gobe weekend daya kwala….

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

         23

Kwanciyarta Kenan tana Shirin gyarawa da kyau tayi bacci, marairaice wa tayi,

tace’ ban iya kwana da haske a kunne ba fa,

Ko kallanta beyi ba,
yace’ damuwarki,

Itade tasan batayi masa lefi ba,haka kawai daga cewa yau ma sai na tuna maki? To jiya me ya tuna Mata? Babu yarda ta iya ganin ranshi ya baci haka nan kawai taji bata san ya kara jin wani haushin, tashi tayi taje takunna ta dawo ta kwanta ta rufe Ido kasa baccin tayi juyi kawai take ta juya nan ta juya can ta mirgina nan tayi can har karshen gadan take kaiwa daga nan ta dawo inda take, duk idan ta a rufe yake,daga karshe bargo ta Shiga ta rufe har kanta tukun ta samu tayi bacci,

Yana kallanta kamar zai kashe wutar,sai dai bai kashe ba juyin da take kamar yarinyar da take rigima da bori ga gashin kanta ya tattaso, ajiyar zuciya ya sauke sanda yaga ta rufa da bargo, bedena kallanta ba sai da ya tabbata tayi bacci sannan hankalin sa ya koma ga system dinshi,yaci gaba da aikinsa, yana nan har har karfe bakwai sannan ya tashi ya Shiga wanka cikin bakaken suite ya Shirya ya dauki abinda zai dauka yasaka a jakar Shi, har yazo kofa zai fita sai kuma ya dawo yaga window a rufe sabida acn da taka kunna jiya Amma bata saki labulen ba,dukda dai gari ya gama wayewa dawowa yayi ya sakar mata labulen ya kunna Mata ac ya kashe fankar,dukawa yayi saitin da take ya bude bargon da ta rufa dashi ganin dan gumi a gaban gashinta yasa shi saka hannu ya goge mata ya ida cire mata bargon aikuwa ta kudundune a wuri daya Zama yayi ya ya dauko biro da takarda yayi rubutu ya ajje akan bedside drawer, ya sunkuya yayi pecking dinta a goshi da bakinta dan motsi tayi alamar an dameta murmushi yayi ya kuma pecking dinta ya tashi ya fita tare da kashe mata wutar dakin.

✨✨✨✨✨

Anyi komai da komai da ya kamata ayi na siyar da company din Abba guda daya Abba Jin kudi ninkin wanda ya bayar yasa shi saurin amincewa,

yace’ sai dai kuma ban taho da takardun ba,sai zuwa gobe Insha Allah zan kawo maka,

Binaif kallansa ya dawo gareshi wani killer smile yayi yace’ ai bakomai an zama daya,

Shidai Abba harga Allah Baya San wannan murmushi nashi tunda suka zo ace mutum yake fama da murmushi da kuma yayi tunanin ko haka nature din shi yake sai ya basar,

Abba yace’ to shikenan hakan ma yayi tunda ga shedu sun shaida komai mai saukine,

Binaif yace’ ya kake ganin zuwa Monday kafin nan zamu iya fara namu aikin?

Abba yace’ ehh badamuwa tunda kaga weekend zamu shiga ba?

Jinjina kai kawai Binaif yayi beyi magana ba, tashi sukayi suka fita dashi da lawyern sa guda biyu sai kuma wani shima, bayan sun fito sukayi wurin da sukayi parking motar su Barr Aliyu

yace’ Wato Binaif kana ganin hakan ba matsala bace?

Binaif yace’ babu wata matsala ai,

Dayan barristern Barr Ibrahim dattijo ne don yama kusan retired yace’ Abinda nake so na fada maka kenan,kaga fa mu mun bashi kudin mu amma kuma ba’a bamu takardun ba, kuma yakamata mu da mukazo siyan abu a zagawa da mu ko ina mu ga yarda ake aiki,muga ma’aikatan da sauran su,

Binaif yace’ ai Baffa wannan duk nayi wancan lokacin da nazo kuma naga komai da komai yarda suke aikin su ba matsala,batun kuma takardun ba komai tunda yace gobe? Ai ina ganin kawai ba matsala,koba gobe ba yace ni mai iya jinkiri ne,

Bar Aliyu yace’ to shikenan ni zan tafi ina da aiki a office,
Musabaha sukayi sannan kowa ya shiga motar sa yayi gaba amma Shi Binaif me makon ya tafi da ya fita daga cikin company n sai ya samu can tsallaken titin yayi parking,waya ya daga yayi kira daga can dayan,

yace’ ku karaso daga kusa,
Ya kashe wayar ya jima a wurin yaga motar da yaga Abba yazo da ita ta fito sai kuma ‘yan jarida suka baibayeshi kamar jira suke ya fito kuma ba damar ya tafi don gaba daya suka baibaye motar tashi,ganin haka yasa shi yin gaba abinsa ya tafi,

Abba kuwa yana ganin ‘yan jarida yasan za’a rina don tun sanda aka sace su Yusseer ake zarya ko an maido masa dasu kome wani ma tambayarsa bata da amsa shikan besan tsakanin lawyer da ‘dan jarida wanda yafi tambaya ba, zuge glass dinsa yayi nanfa kowa yayi korarin yi masa tambayoyi kallansu yayi yarda kowa yake masa tambaya,

yace’ yanzu tambayar wa Zan fara amsawa? Ku min a hankali mana daya bayan daya na baku Minti ashirin zuwa talatin, wani daga cikin Dan jaridanne yayi karaf,

yace’ ance wai an kashe ‘ya’yan shin haka ne?
Wani kuma yayi sauri

yace’ ance kuma Ka Kai kudin kimanin naira Millon dari shin haka ne,shiyasa ma ka saida wannan company?

Wadannan tambayar ta ruda Abba iya rudawa bai kai ga magana ba kuma wani,

yace’ ance kana da yarinya wacce zatayi kimamin shekaru 23 ka tura ta karatu yanzu shekara shida kenan.
Wanda yayi tambayar farko yace’ kuma munji labarin bata taba zuwa gida ba kaima baka tana kai mata ziyara ba shin ya abin yake ne? Wata irin zufa ce ta ketowa Abba betaba tunanin wannan tambayar ba Shi yama manta da batun wannan yarinyar Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un yake furtawa,cikin wata irin dakiya wani Yana shirin yi masa wata tambayar,

yace’ mekuke cewa ne? Kunce ance kunga kena ba abakina ba, yarana kuma ba mutuwa sukayi ba sannan ba wani kudi da aka karba a hannuna game da yarinya kuwa banganta ba bamma Santa ba,ni yarana uku ne,
Cikin wani irin sauri Wanda yayi tambayar farko,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page