A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Daga Kai tayi alamar eh, murmushi yayi yace’ to Zan fada Amma sai ranar da na Rama Nima,
Tace’ to ni Ka karasa min tsifata,
Tsifa ko tajewa, ai nagama,yaushe zaki je Anty safiya tamaki wani,
Turo Baki tayi tace’ a,a niba naso,
Okay shikenan,Bari muga ruwan wanka zao zuber Kan ko kuma zai Karu?
Ya tsine fuska tayi tace’ bangane ba?
Zaki gane ai,
Turo Baki tayi tace’ to dagani naje Nayi wanka, tunda yanzu kawai Sai dai kayi ta fadar magana a nannade kana kulleni, bazaka fada min ba,
Daga ta yayi ya tashi tsaye yace’ to jeki kiyi, ni ina nan,
Tace’ to meye na tashi tsayen? Ka zauna mana, Ka jirani na dawo,
Tashi tayi ta tafi,ta hau stairs din kofar parlour Kenan, taji saukar ruwa a kanta, a sukwane ta juyo ta ganshi da tiyo a hannu Yana fesa Mata ruwa, gaba Daya ya jikata, saukowa tayi itama tadauka guda dayar da tagani a wurin ta fara zuba masa suna dariya abinsu, gaba Daya sun jika gidan, da ruwa shine ya an Kara da buga gate din da ake, Ya ajje yaje ya leka yaga waye, Wanda yagani ne yasa Shi budewa suka shigo, suna shigowa,
Mas’ud yace’ ya haka Naga jikin….
Bekarasa ba yaji saukar ruwa a jikin shi beyi wata wata ba ya ansa ta hannun Binaif ya zuba Mata, sukaci gaba dayi Ita da Binaif shikuma Mas’ud Shikadai yake zuba masu, Mus’ab tsayawa yayi Yana kallansu, wani irin tunanin yaji ya fara zuwa masa, wannan abun sak ya taba faruwa yarda suke din nan, ga suna nan hango wasu yara suna wasa Amma dishi dishi yake hangowa be farga ba sai da yaji Ruwan a jikinsa, hankalin Shi ya dawo kallan su kawai yake bako kiftawa, Yana kallan su Yana zaga yesu so yake ya ga suwaye Amma ina, ya kasa ganin hakan, ruwan da za’a zuba masa suka ganshi a kasa ya Fadi ya dafe Kai,haka mas’ud ya tsugunna ya dafe kansa,da gudu suka karasa wurin su,
tace’ Chatty lafiya?
Mus’ab me ya faru, Mas’ud kunyi magana mana, Binaif yake tambayar su,
Dakyar Mas’ud yace bakomai, sannan ya tashi ya Shiga ciki, haka shima Mus’ab, a wurin suka barsu, ..
Kallanshi tayi tace’ meya faru?
Hannunta ya kama suka tashi tsaye yace’ maybe sun tuna wani Abu ne, makamancin hakan,ya faru,
Batayi magana ba, suka Shiga ciki, direct dakin sa suka wuce suka barsu a parlour,
tace’ Ka Shiga kayi wanka, nikuma zanje dakina, Nayi?
Zama yayi akan stool yace’ jeki hada min ruwan wankan,
Batayi musuba taje ta hada masa zata juyo Kenan tayi Karo da mutum,ya hankada ta cikin ruwan. ..
Koda suka fito shine ya taje Mata kanta tas ya shafa Mata mayika, ya daure Mata da ribbon, ya dauko Mata doguwar Riga tasa, ta daura Dankwalin a kanta, shikuma yasa kana nan kaya,
A parlour kuwa a kasa suka zauna suka daura kansu a kan kujera sai da suka natsu,
Mas’ud yace’ maka tuna, nakasa tuna komai,na kasa,
Mus’ab yace’ Naka sa hakan? Na kasa tunawa, ina ganin Yara de suna wasa da ruwa kamar haka amma nakasa ganin fuskar su,na kasa hakan,
Shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa sai kuma can, Mus’ab yace’ wai baza su fito su bamu abinci ba,
Mas’ud yace’ idan Baka San hanyar kitchen to wannan ba fitowa zasuyi ba,
Yace’ ohh su bb da Mata, Kai Baka mamaki ne?
Mus’ab yace’ wanne mamaki kuma? Bana yi, kaima very soon zamuyi naka ai,
Yace’ wannan gaskiya ne mana, Dan yanzu bawani tsoron yarinya kaidai Bari Malam,
Haba de, wai me Kake cewa ne,
Mekuwa nake cewa,kawai zancen ne yake tahowa Shi daya,Kai dai Bari Malam,an barka a tasha,
Kana Santa ?
Wa nake so? Wannan yarinyar? Taab ko tunata ma banayi,
Um,um fah?
Kai kasan Allah Bana tuna yarinyar nan, kuma naji ance idan kana San yarinya zaka kake tunata ko? Har ga Allah wataran mantawa nake da ita,
Nasan de yanzu tana sanka ai,
Sai tayi taso, ni rabu da ita kaga, harda wani na turo Mata numbern sister na, hmmm wannan yarinyar?
Ummusalma tace’ metayi?
Juyowa yayi yace’ ohh salan gulma ko Kara sowa bakiyi ba, wani me tayi?
Kasowa tayi ya zauna tace’ ehh din metayi?
Yace’ ca tace na bata numbern ki,
To bata mana,mene aciki Dan Ka bata number na,
Yace’ to Zan bata,
Tace’ yanzu abinda zakayi shine,Ka hanata yawo,Ka rabata da friends dinta she trust you.
Tashi zaune yayi yace’ lallema yarinyar nan,ki renamin wayo, za’ayi na hanata Duka wannan? Ni Babanta ne ko yayanta?
Tashi tayi taje ta dauko bowl guda biyu da spoon aciki,sun zata su za’a bawa Chatty harda meko hannu,harara ta zuba masa ta mikawa mijinta, ta zauna a kusa da Shi, suka fara sha sannan,
tace’ tasan Ka zo yau?
Yace’ a,a ban fada Mata, ko kuma Baku sani ba, wata can daban,
Ya fada Yana hade Rai ba’a bashi ba,
Sai kuma yace’ wai Shi wannan fruit salad din ruwa ko kuma me? Mu ba mutane bane?
Mus’ab yace’ rowar Kenan ai,munzo ko ace mana sannu da zuwa
Ehh ba? Sai saukar ruwa da aka mana sallama dashi, ki Tasha malama kije ki zubo mana abinci ko Rai ya baci,
Binaif yace’ ranku zai baci yanzu nan ba yayarku bace ba? Kuke Mata magana with respect mana,
Kallan juna suka kalleta suka kuma kalllan juna sannan aka Mata kallan irin bata Kai ba,
Mas’ud yace’ bb kasan me aka mana kuwa?
Yana Shan abinsa yace’ a,a sai Ka fada,
Mus’ab yace’ sata aka mana fah, gaba kidaya kayan mu na gidan Umma babu Shi,ko tsinke babu, ni credentials dimmu ma nakeji,
Mas’ud yace’ jika wani credentials ni basu nake jiba, zuben da siya nake ji,
Kaifa daman ba mutum bane,ni to karatuna nake ki ato, yanzu ba’a cucen ba?
Karatune me? Karatun Da ba wahala?
Binaif yace’ aikuwa karatu Kona ihu ne da wahala,
Ummusalma tace’ mi amor ai kasan shifah aljanine,
Dariya suka kwashe da Shi ita da Shi, yace’ aww haka fah,Ashe fa aljani ne,
Mus’ab yace’ fisabilillahi bb muna fada maku Amma kuna mana dariya? Kamar Baku damu ba?
Mas’ud da yacika yayi fam,daman ga yunwa ga haushin Hana Shi abinci ga haushi dariya da cemasa aljani, tashi yayi fuuu ya fita yaje ya kwaso jakar su da suka dawo dashi,
yace’ twinny taso mu bar gidan nan, an tsane mu sosai da sosai ai bamu San tsanar takai haka ba, bakomai, nadena zuwa gidan nan kuma Nima idan Nayi aure kar azo min ato ande ji ai,
Mus’ab tashi yayi yace’ yau ina bayan Fav bro,
Ummusalma tace’ Ku kuka sani, wannan yace twinny wannan yace fav bro alasa bitter ne,
Ku fice daman kunzo kun jika min carpet da kujera a je,
Binaif yace’ Umma ta gaida Aisha,
Daman ni an dameni an hanani sakat da mij…..
Bata Kara taze tana Shan abinta,
Sakar Baki sukayi suna kallan su, sannan Mas’ud ya jinjina Kai yace’ taabb to na fasa tafiyar, anan Zan kwana ma, ko yakace,
Mus’ab yace’ kuma mazo mi Hana su sakat? Kaga zamu rage masu Jin dad…
Yo muma rage mana,su Suma siya da kudin su, sai muga ta tsiya tunda an nuna ba’a San mu kuwa sai mun zauna, mu ai daman so muke mi Hana Jin dad…..
Shiru yayi sakamakon cokalin da ta wurgo masa, tacet Baka da kunya ko?
Daure fuska yayi yace’ oho de,
Tashi tayi ta dauki bowl din Binaif da ya Gama ya wuce kitchen, daga nan ta daura abinci, tana yi tana wani Abu har ta Gama abinta tajera a dining koda ta fito ba sanan, wanka taje ta sake ta material Mai kyau Riga da skirt to fito, a waje ta gansu da tsintsiya a hannun Mus’ab shikuma Mas’ud Yana zaune sun baje carpet sunsa cushions suna Danna waya, Kara sowa tayi tace’ meye?
Yace’ fav ne mana, bece min kowa ya gyara daki ba,sai da na taya Shi muka gyara daki daya tas aka jera kayansa sai ca yace bazaiyi sharing daki Dani ba,wai idan Yana hira karami Dani inajin abinda yake fada, shine ya shige toilet yayi wanka, Yana fitowa nace masa ai dole sai ya tayani shine ma wai Dan kar na dameshi shine ya fito wurin bb, kijifa dan Allah,