A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shikuwa da yaje gida kayansa ya fara hadawa masu muhimmanci yazuba a karamar trolley,kayansa na sawa kuma dayake a goge suke kawai zubasu yayi a cikin katuwar trolley dukda haka Basu cinye ba sai da ya Kara da wata,ya kwashe komai masa masu amfani sai abinda ba’a Rasa ba,ya Kai mota,sai da ya Gama komai lokacin shabiyu ta Gota Shi Yama manta da zancen ya kaimata kayanta sai da ya fito har ya Shiga zai tafi ta tuna,fita yayi yaje ya bude motar da Daddy ya fita da ita,ganin bude yasa ya dauko Jakarta.

Dakanshi ya bude gate din don yasan zuwa yanzu mai gadi yayi bacci,Dan ma ya fada masa zai dawo kar ya rufe,shiyasa ma yaga gate din bude sai dabya shigo ya tashi mai gadin da ya rufe, kayan ya fara jida Yana kaiwa ciki,yasan dayan dakin su Mus’ab ne don haka ya kai kayansa dakin kusa da Umma sai da yagama kwashe kayan tas sannan ya zo don kashe kallo da rufe kofa yaje ya kwanta,ganinta da yayi Akan kujera tana baccinta hankali kwance ta daura hannunta daya tayi pillow dashi dayan kuma Akan cikinta, murmushi yayi ganin cute bakinta ya Kara tsukewa, film din da take gani ya kalla Nafsi Al’akhar, ganin yarda ya dauki macen yasa Shi ware ido ya kalle film din ya kalleta har suka tafi talla Hannunsa yasa cikin sumar kansa

yace’ to ai su film ne,nikuma gaske ne, Yama za’ayi na fara daukanta,taaab ai bazan iyaba ma.
Kuma Shi de bayasan tashin ta,komawa yayi ya leka dakin Umma ganin tana baccinta ga kuma mai aikinta nan itama a gadanta yasa Shi komawa,ya Duka a hankali wai karba ta tashi, dauketa, itakuwa tunda ya dauketa ta tashi amma bata bude ido ba,gabanta kawai taji ya gudun tsere Akan gadan dakin ya ajjeta ahankali, harda su furta yawwa bata tashi ba,jere akwatuna yayi a gefe guda Allah yasa ma yayi wankan Shi daga can gidan, wardrobe din dakin ya bude yaga blanket da bedsheets da’alama anan Umma ke ajje su, lafiyyayu ya jawo guda biyu tare da bedsheet guda daya, Akan gadonya durasu sannan yaje ya janye center table din dayagani a gaban kujera yayi shimfidar sa ya yaje ya kulle ya kashe kallo tare da kulle kofar ya dawo ya kashe masu haske sannan ya kwanta, gaba daya ya gaji kuma gani yake daukanta da yayi yasa masa ciwom kafada( sai kace Wanda ya dauki buhun shinkafa ????♀️), addu’ah yayi ya shafe jikinsa,sai dai kuma ya kasa bacci juyi kawai yake ga gajiya ga kwana a bakon wuri gashi kuma a kasa, dakyar bacci ya dauke Shi.
Tana jinsa duk abinda yake sai da taji yayi bacci tukun itama baccin ya dauke ta……..

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

  21 

Da asuba ta rigashi tashi,itama ta Dan makara don har anshiga masallaci dakin ba wani haske sosai kasancewar babu wani security light a wurin kuma babu farin watan da zai hasko ta window,wayar ta fara dubawa tunawa da tayi a bakon wuri take yasata tashi zaune sosai, tunawa tayi yayi shimfida a kasa yasa sauka a hankali daga gadan tana tafiya har tazo bakin kofa ta lalu min switch din dakin ta kunna Amma ganin babu nefa yasa cewa kila sun dauke, a haka tana lalube har ta lalubo kofar toilet din, Dan ma jiya da zatayi sallah nan tashiga shiyasa bata wani sha wahala ba,tayi abinda zatayi ta fito, lokacin har an idar da sallah a wani wuri, hasken da tagani ya tabbatar Mata da andawo da nepa, inda yake ta kalla yayi daidai Yana bacci da’alama kuma baccin ya masa dadi, parlourn ta fita ta dauko hijabinta da ta ajje jiya tana kallo, dadduma ta shimfida ta tada sallah sai da idar ganin beda alamar tashi yasata zuwa inda yake,ta fara bubbuga pillown da yake Kai,Amma ko motsi beyi ba,hannu tasa tafara,

cewa’ Kai,Kai,Kai, Kai Ka tashi an idar da sallah,
Amma ko motsi beyi ba,haushi ne ya kamata Tama Rasa me zata masa ya yashi Kara buga pillown tayi amma a banza sai kara juyawa da yayi dayan barin ya juya Mata baya, wani takaici ne ya Kara kamata kawai takara sa hannu ,

tace’ Ka tashi mun makara fa,kaga gari yafara wayewa Ka tashi,Kai Kai tashi, Ka tashi zaka makara fa Kai, Kai,
Ganin be tashi ba yasata nufar toilet ta debo ruwa a hannunta kafin ma tazo ya zube dankwalin kanta ta cire ta jiko da ruwa tana zuwa ta matsa masa Shi a fuska, bawani firgita ba don tunda tafara cewa Kai Kai din nan ya tashi haushi ya ishe Shi wai kai,shine ma Kai,irin batasan sunansa ba,shiyasa yayi banza ya kyaleta yana jinta ta Shiga toilet yasan ruwa zata zuba masa shiyasa da yaji ruwan be firgita ba, Yana tashi kuwa ko kallan inda take beyi ba ya Shiga toilet.
Ita kuwa tabe Baki tayi ta cire hijabinta ta hau gado ta kwanta abinta,tana ji ya fito ya tada sallah daga nan kuma bacci ya dauke ta, shima da ya idar da sallahr ko kallanta beyi ba koma zai kwanta yaga wurin ya Dan jike, kashe wutar dakin yayi yaje ya kwanta a bayanta ya juya Mata baya Yana kwanciya yayi bacci.

Basu suka farka ba sai goma da kusan rabi a kusan tare suka farka Amma ta Riga Shi bude ido ganinsa da tayi a Kan gadon yasata Kara ware ido sosai tana kallansa,ta kalli shimfidar tunawa da tayi ta jika masa yasata komawa ta kwanta ta zuba masa ido tana kallo, yarda yake sauke lumfashi hankali kwance eyelashes dinsa tubarkallah dagaye dasu sai hancinsa maidaici da bakinsa pink Amma beyi pink sosai ba,fari ne Shi sosai irin farin fulanin daji kuma asalin fulani,shiyasa Suman Kansa take a kwance dukda tama fitowa yake askewa amma yanzu ya Tara ta dayawa, kallansa kawai take batare da san tana yi ba,samun kanta tayi da murmusawa,
Jin kallan bazai kareba yasa shi bude idan sa,aikuwa sai a cikin nata da sauri ta rufe idanta,gabanta na faduwa,Shi dariya ma ta bashi sai da tagama kare masa kallan sannan kuma ta wani rufe ido,Shi yarfa tayi saurin rufe idan ne ma ya bashi dariya.
Murmushi kawai yayi ya tashi zaune, tunawa da Fishi yake da ita yasa shi,

cewa’ ke,ke,ke,ke, ke ki tashi mana,
Wani haushi ne ya kamata wai ke sai kace besan sunanta ba? Kefa? Aikuwa ta bude idanta ta kumbura Baki itama ta tashi zaune tana Shirin sauka a gadan

yace’ ke, ke, ke Baki iya gaisuwa ba ne? Zaki wani tashi ki fice to idan ma kin fita ina zakije?

Ina kwana, tafada tana Kara tanke fuska tana cin magani,wata irin dariyace ta ciyo Shi dukda Baya kallanta da ta gaida Shi Amma yasa ba Dan taso ba tayi,wato ba dadi Ashe Shi kuma tamasa, sai ya murmusa ya kuma Kara daure fuska shima

yace’. Haka ake gaida miji ne? Wani ina kwana? Ko kallansa ba bakiya ba wannan wardrobe kika gaida Bani ba,kuma suna Baki fada ba,kawai kika ce ina kwana, in fact ko wanka ma bakiyi ba daga tashi sai a kafa gaidani gaskiya ban amsa ba. Yafada Yana tashi tare da bude akwatinsa ya dau abinda zai dauka ya shige toilet,Yana Shiga kuwa ya kalli kansa ya madubi yasaki dariya yace’ yarinya Dani kika daura indai nine wani Kai hmmm yanzu aka fara.
Itama Kara kumbura Baki tayi,

tace’ har wani nice ke ah kamanta keke ba ke ba, tashi ta fara ta gyara dakin tsab ta nade bargon daman bawani jikewa yayi da yawa ba har bushe, neman magana ne kawai Akan gado ta ajje su ganin akwatinsa yasata janyowa takaisu wurin wardrobe tunanin fara laya masa su tayi,hakan kuwa tayi babbar ta bude ta fara jera kayan kowanne daban ta jera kanana daban manya ma daban,tasa takalmansa a kasa, inner wears kuwa data buda ta ga sune aciki sai ta barsu bata fitar ba, ta takardu kuma itama daga kasa tasa a dayan site din Wanda zata jera nata kayan, sannan ta mayar su daya cikin daya ta rufe ta ajje su daga lungun Dan lungu ta dakin beda wani datti sai Freshener data gani a kayansa Wanda ta jera su Akan mudubi yasa ta fesawa lungu da sako na dakin, tana cikin fesawa yav fito bayan ta yaje ya tsaya tana jiwo kuwa ta bige dashi ja Baya yayi da sauri ya rufe ido ya daura hannunsa Kan idan sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page