A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

yace’ student ba magana ?
Sosai taji kunya ya kamata, batayi maganaba

yace’ Nima Zan iya zama friend din? Kamar yarda yata ta Zama? Friend or sister?
Sister tace, om thanks yace shima Yana barin wurin,suna tafiya itama taja trolley dinta ta fito Allah ya taimaketa ta ga mai adaidaita ta hau,sunan unguwar ta fada masa suna tafiyar taga anyi sauye sauye sosai wasu wuraren an same wasu kuma sunanan an gyarasu,taga sauyi bakadan ba shekara shida ai ba wasa ba ne,tana masa kwatance har suka iso kofar gidan,don dakyar ma ta gane Saida suka tambaya sannan ta gane, suka sauka ta fito da kudinshi ta bashi har ya amsa

yace’ Hajiya fa wanann ba kudin mu bane kalla tayi taga dollar ce ita ta manta shaf da tayi canji a airport ai, numfashi taja,

tace’ to gobe ka dawo zaka kaini wani wurin inba damuwa, badamuwa yace
Trolley dinta ta dauka tayi hanyar wani gida gidan ta kalla sannan tayi knocking…….

By : Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

         11

Tasan dai by this time watakila ma sun rufe gidansu,agogon hannunta ta kalla,taga lokaci zata Kara knocking taji an bude kofar,matar ta da ta bude kofar tace’ wacece?

tace’ Ummusalma ce,
Saida ta maimaita sunan sannan tace shigo mana kya tsaya daga nan kuma,
Shigowa sukayi,sosai taga canji daga gidan,ansake ma fasalin gidan anyi parlour sabanin da,da dakuna ne a jere (sai kace islamiyya), trolley din matar ta ja Mata suka Shiga parlourn nasu,Zama tayi Akan kujera,

Tace’ ina yini,
Da lafiya matar ta amsa mata sannan

tace’ lafiya kuwa? Na ganki acikin dare haka?
Ya zamana dole ta canza ta dawo Ummusalma ta tada, idan har tana so ta cimma burinta,kowanne Saida bayani yake iyiwa. Numfasawa tayi

tace’ yanzu na dawo daga karatu,kuma naji babu Wanda nake san ji irin labarin su Neena I mean Amina,
Matar( makwabciyar su Amina)

tace’ Ummusalma su Amina fa tashi sukayi daga garin nan a yarda suka ce min kenan,don kinga a lokacin ma da suka tashi kudin haya ne Basu dashi,shikuma mai gidan yace bazai daga masu kafa ba,shine ya kwashe kayan su masu amfani zai siyar a lokacin ne Amina tazo da kudi,ta bashi sannan ya hakura ganin kudinsa, yace Amma dole sai sun tashin masa daga gida,kinji yarda akayi,shine ma sanadin tafiyar su,
Lumshe ido tayi ta jingina da kujeran,tana cigaba da ji,
Itama matar cigaba tayi,

tace’ tunda suke da mai gidan hayar Basu taba Jin kansa ba da Abban Amina Yana kokari sosai ganin ya bashi kudinsa,to tunda Inni ta fara rashin lafiya shikenan kuma komai ya canja bansan meke damunta ba Kona tambayi Amina bata fada min sai dai ta shashantar da zancen ma, kamar basa so mutane su San meke damunta haka na dauka de, koda zasu tashi Basu fada min inda zasu je ba saidai tace garin zasu bari,
Bude idan ta tayi ta tashi

tace’ Bata da yaya? Ko kani haka de?

Gaskiya nidai tunda nazo unguwar nan ita kadai nake gani, kuma ita kadai ce a wurinsu,kuma ban taba Jin ta bani labarin yayun ta ba.
Numfashi ta kuma ja

tace’ to yau uwa fah? Wakika sani?

Bansan Yan uwansu ba Gaskiya,sai dai abokan arziki,don munyi rashin mutane kamar su,daga Abban har Inni dukan su mutanen kwarai ga kuma Amina Wanda kowa yake Santa,ta kasance mutum mai shiga Rai,kuma duk wanda yasanta to tabbas ya sanki,wani irin kauna take miki,idan kana San faranta Mata to Ka ambaci sunanki, bansan ya Zan kwatanta maki yarda take sanki ba.

Amma suna cikin wannan halin taya Baffa ke biya Mata kudin makaranta?

Yana aiki ai,yana gadi a wata makarantar primary private ce school din sannan kuma yana Saida fruit kuma yana aikin kafinta bansan ya yake yi ba Yana biya mata kudin makaranta amma de wannan aikin yakeyi,

Ya sunan makarantar?

Bansani ba Gaskiya wannan Abban su Sadiq ne ya fada min(mijinta) Amma idan ya dawo Zan tambayeshi Insha Allah yanzu baya nan.
Shiru sukayi sannan

tace’ Amma Ummusalma bakya ganin idan neman su zamuyi ai ya bar makarantar tunda tashi sukayi ko?

Bana ganin sun bar garin nan,kece ta fadawa haka,Amma dole suna garin nan,kuma zai ci gaba da sana’arsa ko kuma ya sake wata,dole cikin biyu za’ayi daya.
Tashi tayi

tace’ kinga ko sallah banyi ba,Bari kiga na tashi na tafi,

Yan gidan ku Amma Basu San zaki dawo ba ko?
Ta tambaya tana tashi don ta rakata,ta fara Jan akwatinta

tace’ ba gida ba zani,hotel zanje na kwana gobe Insha Allah Zan dawo,
Ta fara tafiya tana Shirin barin bude kofar parlourn,da sauri matar

tace’ wanne irin hotel kuma?
Don Allah kizo mu zauna anan tunda kinga mijina baya nan? Daga ni sai yara kuma ba yau zai dawo ba, tana fada tana rike da akwatinta don karma ta fita, kallan matar tayi taga har zuciyar take maganar,Amma sai

tace’ ki barshi kawai zanje na kwana a can din,karki damu,

Yazaki ce Karna damu,kinga Don Allah ki dawo mu zauna kinji ko?
Bayarda ta iya don itama ba San kwannan hotel din take ba,suna cikin haka aka dauke nepa, matar taja Mata akwatinta ta kunna masu bulb din DC, ta Kai akwatin ta dawo taja hannunta ta kaita daki,

tace’ dakin yara na ne mata,sun tafi hutu,sai Maza ki zauna anan ki huta ai yafi de,yanzu kiyi wanka sai kiyi sallahn naki,
Da kallo ta bita har ta fice a zuciyar ta tace'”daman akwai mutanen kirki a duniya haka? A gogon dakin ta kalla taga 11:50,bata zaci lokacin ya kure haka ba, agurguje ta fada bayin,Dan karami ne toilet din babu bathtub sai makwarara kawai,kuma ba ruwa don ga containern ruwa nan,a hakan de tayi wanka ta ta daura towel din data gani,tana fitowa kawai ta bude akwatinta ta dauko rigar bacci tasa,tasa hijabi tayi sallah,tana cikin sallah matar ta shigo ta kawo Mata abinci, tana idar wa kuwa ta zanjo tray din abincin,tuwon semo miyar kubewa bushashiya da Banda Tasha manja,harda man shanu da yajin kalwa acikin wani da bowl wato ko tana ci sai tasaka, zubuwa kuwa tayi,tunkafin tafara ci yawunta ya tsinke,irin dadin nan????
Aikuwa taci sosai don kulli biyu taci,ga kuma wani lafiyayyen ginger taci tayi nak da ita, wani dadi takeji Kanta ita zata iya cewa ma tunda kafin ta tafi bata ci ta koshi kamar na yau ba.
Tattara komai tayi ta nufi parlourn duhu tagani ba haske dawowa tayi tadau wayarta sannan ta fito, kofar data gani ya Mata kama da ta kitchen ta nufa,ta ajje kayan sannan ta koma ta zauna, Qur’anin tagani ta dauko ta Karanta daga bisani kuma ta fada duniyar tunanin yarda za’ayi ta Gama abinta cikin kwarewa, tana zaune Jin tafara bacci yasata kashe bulb din ta kwanta, addu’ah tayi sannan sai bacci.
✨✨✨✨✨✨✨
Da Asuba Saida maman Sadiq ta tasheta sannan, tsabar gajiya,bayan tayi sallah komawa tayu ta kwanta,sai bacci batawani yi bacci dayawa ba ta tashi ta gyara dakin ta wanke toilet,ta fito bakowa a parlour alama de Basu tashi ba,shima gyarawa tayi, tayi wanke wanke ta bude parlour ta fito ta share tsakar gidan ta wanke Shi tas kasancewar tiles ne kuma Dan karamin ne tsakar gidan,bayan ta gama ta dawo parlourn ganin nepa yasa ta daukan Burnern da ta gani ta kunna sannan tasa turaren wuta,iya parlour tasaka,ta Shiga daki tayi wanka ta shirya cikin doguwar Riga sannan ta fito lokacin yaran ma sun tashi an masu wanka,su biyu Maza gaidata sukayi suna cigaba da kallansu,itama Zama tayi suna kallan tare,tama manta yaushe rabonta da kallo cartoon akeyi kuma mai kyau cartoon itama ya Mata kyau bare kuma yara,suna cikin haka saiga maman Sadiq ta fito daga kitchen gaisawa sukayi,maman Sadiq

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page