A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Wai me ake cewa naji ana wani Amarci kaza me yake faruwa”.

“Ni ba wannan ba please bb Ka taka Mota mu tafi”.

Binaif yace, “revenge ne ai”.

A tare suka ce “revenge?”

“Ehh revenge ne Nima haka kuma min har Gwara nima ina dan sauri”.

Koma suka yi suka kwanta sun tuno abinda sukayi can.

Mus’ab yace, “Amma ai Twinny ne Bani fa fav ne yake tukawa ai”.

“Naji wannan”.

Shiru sukayi suka rabo dashi Mas’ud ya cika ya cika yayi fam.

Uncle yace, “yanzu idan mukaje gida kamar minti nawa zamuyi sai Ka kai ni sannan sai Ka kaisu ko inaga haka zaka ai ma”.

“Uncle hakan za’ayi yanzu kallan ball zaka yi ni kuma na huta”.

“Haba bb Haba bb this is cheating wallahi”.

Banza sukayi suka rabu su sukaci gaba da hirar su, ganin sun tsaya a gidan farko uncle yaje ya bude suka Shiga yasa su mamaki komai iri Daya dana bb marabar kawai su ba Field Shi kuma da akwai beyi parking ba ya tsaya ya kalli chatty.

Yace, “Chatty Ka gidan Ka nan zaka iya fice mun daga mota na kawo Ka”.

Rasa bakin magana sukayi Basu taba tunanin nanne gidan su ba kusan Kullum sai sunyi maganar gidan daga waje iri Daya ne su uku a jere Ashe harda daga ciki ma iri Daya nanne ga shinan ko ina haske. Jiki a sabule ya fita shima uncle fita yayi Dan sunyi waya da Ummu tace tana gidan Mas’ud hakan yasa ya fita tare da daukar ledan Mas’ud guda daya suka Shiga cikin gidan.

Haka ma gidan Mus’ab shima iri Daya ne kasa jure wa yayi ya rungume Shi bayan ya fito, shine ya raka Shi har parlour shine ya Shiga ciki sai ga su sun fito da Neena gaisa wa suka yi yayi musu dan nasiha sannan suka tafi shida Neena gidan Mas’ud suka wuce be Shiga ba suka fito suka tafi, Neena suka Kai mayar sannan Ummusalma ta tafi da ita da pretty suka tafi.

Gidan Mas’ud .

A Hankali ya tura ya shiga tana kwance bayan tafiyar su tana tunanin Jin muryan sa da tayi….

Ta rufe fuskar ta mayafi bata San san da ya karaso har ya tsugunna a saitin fuskar ta ba, sai da yasa hannu ya Bude faskar ta ta sannan ta bude ganin sa da tayi a gaban ta yasa razana lokaci guda kuma tana neman guduwa hannun ta ya rike gam ya dawo da ita shima ya zauna rungume ta cikin kunne ya rada mata.

“Your husband is here”.

Sai anan ta samu wani irin nutsuwa sai kuma tasa kukan da tasan na farin ciki ne wani irin yanayi suka tsinci Kan su a ciki dakyar ya iya ce su tashi suyi sallah.

Bayan sunyi sallah ya sukayi addu’a ya mata tambayoyi sosai kuma ya samu gamshashshiyar amsa hakan ya masa dadi, sai dai hawayen da take yi ne ya kasa sanin takai Mai Mai na meye nan take zuciyar Shi ta bashi amsa da bata Sanka wani irin dokawa yaji kirgin sa yayi nan take yaji babu dadi amma dayake yayi gadan boye emotion sai be nuna ba sai ma ya wani murmushi da yayi ya tashi ya fita ya dauko cup da plate ya dawo tana nan yarda ya barta Zama yayi ya zuba musu madarar ya Mika Mata cup din ta madarar kawai Tasha duk yarda yayi da ita da ta ci wani abu kinci tayi haka ya kyaleta ya Gama ya kwashe ganin be dawo ba yasa tayin wanka ta fesa turare da humra tasa karamar rigar bacci Mai laushi sannan ta kashe wutar dakin ta kwanta tare da kunna lamp sai anan wani saban hawayen ya zubo mata Jin sakamakon zuciyar ta da ya Raya Mata kila ma Abba ne ya mamamika masa ita Baya San ta, sai wani saban hawayen ya kuka zubo mata Jin anbudw kofar an shigo yasa ta tsayawa da kukan tana neman hadiye Shi. Zama yayi a bakin gadan ba ita yake kallo kamar yarda ita ma bashi take kallo ba.

Yace, “kiyi hakuri, bansan ta ina ba zan fara nayi abinda naji zuciya ta yarda da abinda aka fada min kuma Nayi, na bi san Rai na da zuciya ta na auro ki”.

Shiru yayi beci gaba ba.

“Bansan wanne irin mutum zaki dauke ni ba all I know is I Love you!”

Jin karshen Kalmar tayi kamar a mafarki shine kuwa yake cewa yana Santa?

“Bansan wanne lokaci bane bansan kuma wanne rana bane naji hakan ya faru dani, my love for you I know is beyond imagination it’s a strange kind of addiction I can’t stay without you even for a moment there is something which attracts me to you with you everything is fresh like dew Amor I just want you to know that I will always love you till my last breath I don’t know whether my words make you clear how much I love you”.

Tashi yayi ya zago inda fuskar ta take ya hau gadan shima ya kwanta suna fuskan tar juna Yana kallan ta tana kallan sa. Bata san me zata ce masa ta wani Zama speechless ta Rasa bakin magana cewa zatayi tana San Shi? Ko me zata fada ma.
Besan meke Jan Shi na ganin kirjin ta na bugawa da sauri da sauri yasa ya Kara matso da fuskar Shi sosai ya mayar da Kan sa pillown ta runtse ido ta tayi Jin bugun zuciyar na Kara ruwa, shidai besan mene ba haka kawai yake Jin wani iri a jikin sa kuma bazai iya Barin koma mene ba bata Ankara ba kuwa taji bakin ta a cikin nashi ware ido tayi tana kallan sa tun tana iya hana kanta kin biye masa kuma de na biye masa su Chatty ba kanta.

A bangaren Mus’ab kuwa komai ya tafi normal da yake yarda suka tsara abin su sai dai Jin wank bakon Al’amari Muja taji sosai ta sha wahala ba laifi.

Washegari da safe aka aiko musu abinci daga gidan Umma Binaif aka kawo wa ya basu.

Shiga daki yayi Yana cika Yana batsewa.

Ummusalma tace, “a’ah lafiya? Ba drivern gida Umma bane?”

“Shine mana har wani mu baza’a kawo mana abincin ba? Abincin su fa kadai aka kawo”.

Tana daga kwance kawai tayi juyi ta koma dayan barin.

Tace, “idan Ka Gama cikar taka ni bacci nake ji”.

“Me Kenan?”

Dan juyowa tayi.
Tace, “idan Banda abinka Kai saban aure kayi ko me da za’a wani aiko maka abinci”.

“Sabo ne mana almost 70 days”.

“Naji wannan”.

Murmushi yayi Yana kwanciya a kusa da ita tare da sa Hannun sa ta cikin ta.

Yace, “shiyasa Naga jiya kin…”

Tasa Karshen zancen shiyasa ta juyo a fusace maimakon magana taji bakin ta a nasa sun dulmiya basa Jin kira, sai da suka lafa.

Tace, “Ba bugun kofa nake ji ba?”

Shafa kanta yake Wanda ya sha kananan kitso Yana rike da hannun ta Yana kallan zanen lallen ta.

Yace, “oho koma waye kuma sai munyi wanka”.

Ware ido tayi tace, “nidai banzan yi da Kai ba Ka Kara wahalar dani Ka wahala fa kafin kayi yafi dari”.

“Dari ko? Naga Darin kike so Kkenan, kuma Naga Fansheke nake yarda gobe ma idan ance tafi wanka bazaki ba”.

“Revenge?”

“Idan Kin fada hakanne”.

Tashi zaune tayi tace, “da’alama ‘yata ta tashi Bari nayi wanka sai Ka rike ta kafin na fito ko?”

Kafin yayi magana wuf ta sauka ta shige toilet ta fara, tana gasa jikin ta Dan ba laifi ta Saba da ruwan zafi a wannan jegon nata, tana Shiga yarinya ta fara kuka Jin tana kuka yasa tayi gaggawa ta fito dukda ta dan jima tan zuwa ta karbe ta ta fara jijjaga ta ta danyi shiru sannan ta bata ta Tasha sai Shiga anan ya Shiga wanka kafin ya fito ta tafi dakin ta ta Mata wanka ya shirya ta sannan itama ta shirya cikin atampa har yau bata San zani a dole kawai take sawa skirt ta saka tayi kyau abinta sai kanshi suke zubawa ita da ‘yar ta shigowa yayi, ya dauki pretty sannan ya karaso Inda take a gaban madubi.

Yace, “bakije kinga waye ba?”

“Nifa na manta ma da ana bugawa kaje kaga waye”.

Fita yayi da pretty a hannun sa yaje ya Bude yana Bude wa yaga Chatty.

Hanya ya bashi ya shigo shikuma ya cukume ya daure fuska irin an bata min Rai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button