A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yusuf Yana kallan ta yasab taci kuka ta gode Allah,
yace” mene ya faru?”

Zama tayi tana kara goge hawayen ta,
tace” aure za’a min”

” Then what?”

Yaseer yace” dawa?”

Tace”da uncle fa”

Murmushi Yusuf yayi kawai, yace” to sai me kuma? Dan za’a maki aure da Yaya bakomai bane ba, kawai ki yarda ki gode wa Allah kin san da Wanda za’a hada ki, look at Yay Sameera bata san da wanda za’a hada ta ba, bata San sunan sa ba, bata taba ganin Shi ba, kuma za’ayi auren”

Yaseer yace” ehh gwara ke sau dubu tunda he’s your favourite, you loves him and he loves you too,mene na kuka banga abin zubda hawaye anan ba”

Yusuf yace” haka ne,ummu karma ki wani ce bazaki yarda ba,ko kiyi musu dasu kawai ki yarda tunda kinsan Shi idan kince bakya San Shi na soyayya San dakike masa daga yanzu kike kallan Shi ahakan”

Shiru ummi tayi tana Jin su, a hankali ta sa hannu ta goge kwallan ta,
tace ”thank you”

A tare suka hada baki wajen cewa” first time in history”

Duka ta kai musu suna dariya, tace” ku tashi Ku fita”

Yaseer yace” angama matar big bro”

Yusuf yace” ai yanzu kin koma Anty,ko yaya?”

Tasowa tayi tace ”Allah Bana so ku fita Ku ban wuri,sanda nace ina so ai ba fada ba kuka yi”

Fita sukayi suna tsokanar ta, kusa da Sameera tazo ta daga ta,
tace” yaya sameera, ki dauka kece a matsayin ni, ki dauka kinsan wanda Abba zai hada ki dashi, Ka dauka kinsan n halin shi, you told me Wanda kike so sau biyu kacal kika taba ganin sa, sai haduwar da kuka yi a Sahad, uku Kenan, taya kuma zaki so Shi? Mutumin da Baki San halin shi ba”

Tashi Sameera tayi, cikin sanyin murya tace” ummu sau uku muka taba haduwa, amma muna waya, Yana da kyan hali na lura da hakan, beda wata matsala yana da abindm dariya barkwan ci gashi da mita duk nasan hakan, Amma bansan ya akayi zuciya ta, ta kamu da San Wanda be Sona ba, Mai son Wanda be San inayi ba, mesan wanda be damu Dani ba”

“Kide fadar haka”

“Ummu kenan na fada masa fa, Nan da wata hudu aure na amma ko magana ya kasa min, bare …”

Kuka ne yaci karfin ta, ta kasa fadar sauran abin da zata ce, girgiza Kai ummu tayi,

tace” gobe za’a daura aure na,ki fadawa su yusuf Bari na tafi”

Fitowa tayi tagan su a parlour,suna ganin ta, Yusuf yace” da girman kujeran ki”

Harara ta Galla musu tace” azo a rakani”

Yaseer yace” ko Baki fada, idan daukan ki ma kika ce ayi sai ayi ai”

Sun rakata sun dawo yaseer, yace” Allah sarki an maka kwace”

Banzan kallo ya watsa masa, yace” Bana San munafinci, san nata da nace ina yi da ne, sai kuma she’s not my mate”

Yaseer yace” wai aure tab Allah sarki yanzu sai a school zamu ke hadu wa fa ko?”

“To Dan gidan ku a gidan ta zaka ke zuwa kome?”

“Wallahi daza’a barni gidan Zan koma da Zama kasan Allah”

“Kaima san Ya mas’ud ba bare zaiyi”

“Ai wannan Dan hana rawar gaban hantsi ne”

“Abokin nawa”

“Shidin”

“Aikuwa zai na sanar dashi”

“To meye ne ina ruwana”

Sai bayan Isha suka tafi gida, suna Shiga Kenan suka wasu hadaddun motoci guda uku iri daya gasu bakake har wani sheki suke yi dukda dare ne amma fitilun wurin sun haska su,

Mas’ud yace” woww bb wannan fa”

Sai da suka fita sukaje wurin motar Binaif yace” biyu nawa daya na Mi Amor”

Mas’ud yace” wacce mi amor din? Tama isa?”

Murmushi kawai yayi ya zaro key din guda biyu ya Mika masu yace” Happy birthday”

Ya wuce ya barsu a wurin, sanda rewa sukayi suka kasa motsi sai yayi nisa Yama kua Shiga parlour suka taho da gudu suka rungume Shi,

Mas’ud yace” amma shine Ka…”

“Shishish, bansan Jin komai”

Mus’ab yace” bb mun gode sosai mun…”

“Haka ma godiya ce, farin cikin Ku har yau har gobe shine nawa.

Zansu yayi suka Shiga ciki, Umma na zaune ita kadai tana kallo, abin ta,

Tace” sai yanzu zaku dawo?”

Binaif yace” wani abun farin ciki ne ya same mu Dan Allah yau karki yi fada kinji Umma”

“Jarababbiya Ka maida ni Ashe bansani ba Ka kyauta”

Binaif yace” ai idan ana neman masiffiya an same ki”

Cokalin abinci ta dauka ta wurga masa tace” Dan zakaraw’a kai yanzu zaka cewa Safiya jarababbiya ne? Ka rena ni, gidan nan Zan Bari bazan zauna ba”

Tabe Baki yayi yace” Dade yafi dan Bana so daman ki zauna yaran su koyi fadan ki, kinga Baban su Mas’ud yau muka hadu da su da maman su”

“Alhamdulilla, Alhamdulilla, Alhamdulilla, Allah Kaine abin godiya, taya hakan ta faru?”

Binaif tsab ya bata labari, Umma tace” Kai kaga, Abu sai kace almara, Ikon Allah Kenan, azo a kaini Naga Iyayen ‘yan albarka”

“Haba Umma da Daren nan? Ai sun rufe gida yanzu”

“Allah ya kaimu gobe”

Mas’ud yace” bb banga Ka Shiga daki ba”

Mus’ab yace” bafa ta nan”

Umma tace” ahaf ina zai Shiga daki ba mata Ashe shiyasa bata dawo ba tana nac wurin Iyayen ta hakan ma yayi kyau ai”

Banza yayi dasu ya koma doguwar kujera ya kwanta ya rufe idan sa, Yana Jin su suna masa tsiya ya kyale su, a haka bacci ya dauke Shi yasan idan yaje daki ma ba bacci zaiyi ba, har suka Yana kwance a parlour ranar nan yayi bacci.

Washegari da safe suka tafi gidan Baffa har Umma sai da aka daura auren ummu sannan su Baffa suka wuce Umma ta koma gidan ta, Daddy kuma ana daura aure ya wuce airport ya tafi Adamawa sunyi murbab zuwan sa sosai shine yake fada masu auren da aka yi da kuma samun Iyayen su sosai hakan yasa su murna,be wani jima ba ya dawo, kasancewar tafiyar jirgi ce befi mintoci ba yasa yayi sauri,

Matan sa ya gani a zaune suna hira tare da ‘ya’yan su guda hudu, ya kallo yaran kawai girgiza Kai,

yace” Ku same ni a Sama”

Ya wuce dakin sa, sai da yayi wanka ya shirya ya fito ganin su da yayi a parlourn sa ga kuma abinci, ya zauna ya dauki remote ya fara zanja channel sai da ya Kai labarai tukun,

yace” Mas’ud da Mus’ab Wanda suke gida nan ada kafin su koma gidan Umma nasan da cewa kune kuke aika ta komai…”

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ????A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

   56

Har wani sauri yake yi yaga ta wuce ta, Yana gaba tana bayan sa har suka isa dakin a kusan tare suka shiga suna Shiga suka ga su Yusuf a dakin Shi kuma Yana kwance yana kallan su suna fa Hiran su Banda Ummu Dan ca tace baza ta zo ba.

Mas’ud murya kasa kasa yace, “kun fada masa?”

Yaseer yace, “a’a Ummun ce tace Kar a fada”.

Wuri ya samu ya zauna ita kuma Ummusalma fita tayi ta Kira ummu a waya Jin abin da suka ce, tana daga wa.

tace, “me yasa kika ce kar a fada masa?”

Ummu daga can tana kwance a daki haka nan taji yau duk jikin ta yayi sanyi ga wata irin kunyar Uncle da take ji ta Rasa dalili tasan su Baba da Abie ba fada masa zasu yi ba tunda Binaif ne ya ruki da a daura din sun zaci zai fada koma ya fada.

Tace, “yaya salama fa kunya nake ji shiyasa”.

Murmushi tayi har hakora ya fito dimple din ta ya loma.
tace, “yanzu de idan Anty zata barki to ki fito asibiti ki taho min da abinci da freshyo”.

“To Allah yasa ta barni idan nazo zan kira ki sai ki shigo Dani”.

Murmushi tayi tace, “to sai kinzo”.

Juyo wa tayi da murmushi a fuskar ta sosai kana gani zaka san abin ya bata dariya amma maimakon tayi sai take yin wannan murmushin, kicibus suka yi dashi yana tsaye Yana kallan ta ba wayar ta ta yake ba kawai kallan ta yake ta yarda ta Kara masa kyau da fari na musamman.

Daga masa gira Daya tayi tace, “kallan fa?”

Murmushi yayi Yana sa hannun sa a dimple din ta yace, “I miss you”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page