A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dakin ta koma ganin basa nan yasa ta Kira shi, be daga ba tasan maybe sun kusa dawowa Zama tayi tana kallan ummu fuskar ta tayi ja dan kuka tana nan zaune tana saka wa tana kunce wa suka dawo.

Zama uncle yayi Yana sauke numfashi Yana nishi,
yace, “na kuwa ji dadin wannan Mike kafa da nayi kace azo a sallame ni nikam kasan fa irin condition basai na fada ba”.

Binaif yace, “Kar Kadamu yanzu nan Zan kokar ta”.

“yawwa haka nake so da ansa anyiwa mutum aure a kaishi gida mana yazo ya wani tare a nan ana Kula dashi”.

Ummusalma tsabar kunya jitayi kamar ta nitse a wurin ta yarda maza basu da kunya ko ta sisin kobo ce bare kuma su Saida wa wasu tana Jin su suna zancen su ganin ba shiru zasu yi ba kuma ummu ta tashi amma bata wani motsa ba kawai de tana motsi da idan ta ne.

Tace, “kun tashe ta fa?”

A tare suka juya ganin ta fara bude Ido tana cuno Baki wurin ya karasa Yana jera mata sannu.

Yace, “sannu ya jikin? me kika so? Ina ke maki ciwo? Zaki ci abinci? Kin sha maganin? Aje a siyo maki chocolate?”

Wata katuwar harara ta maka masa ta juya ta Mai baya ta rufe idan ta, sosa keya yayi ya kalli Binaif.

yace, “kaima haka kasha fama?”

Murmushi Binaif yayi yace, “nasha Mita de har yau kuma ina Kan sha”.

Ummusalma ce ta matsa wurin ta ta leka fuskar ta.
Tace, “me kike so?”

Hannun ta ta kama ta rike gam cikin muryan kuka da tsantsan shagwaba kuma a hankali yarda su kadai ne kawai zasu ji.

Tace, “please Yaya don’t go, uncle zai Kara kuma da zafi please”.

Sai hawaye, murmushi salama tayi ta goge mata hawayen ya zauna a kusa ganin haka yasa ummu juyo wa Kara kama hannun ta tayi cikin sanyin murya da rarrashi.

tace, “kiyi hakuri haka abin yake, dauriya ce kawai zakiyi idan kika daure zaki ga kamar ma ba’ayi komai ba kinji ko?”

Matsowa yayi kusa da su yace, “nifa banyi komai kadan ne fa ai za…”

” Haba yaya Dan Allah nikam ya isa ya haka”

Binaif yace, “suna san privacy zo muje wurin doctor din maybe yazo yanzu”.

Sai da yayi mata peck sannan ya fita.
Ummu de daura kanta a Kan cinyar ta ita kuma sai afkin rarrashi Basu jima ba sai ga su sun dawo da uban magani da takarda a hannun sa da’alama an Basu sallamar daman tasan za’a basu tunda uban naci yaje wurin.

A hankali take taka kafar har suka iso wurin motar su a baya tasa ta sukuma suka kwaso kayan Muja ta gani zata je pharmacy da’alama magani zata siyo,zuwa wurin ta tayi.

tace, “kinga mu an sallame mu sai wata ran kuma”.

Muja tace, “aikuwa muma an sallame mu amma sai yamma zamu tafi”.

“To shikenan Zan Kira ki ko zuwa gobe ne Isha Allah”.

Godiya ta Kara yi Mata sannan ta kuma bata wani kudin suka tafi, baya tashi ga ta zauna ummu ta rike hannun gam kamar Wanda zata gudu.

Binaif yace, “kinga ki dawo gaba ki bar masa matar sa”.

Aikuwa ummu tasa bata yi magana ba amma ta nuna bata so ai tuni ya shige gaba, sai da ya Shiga ya juyo yana kallan ta yarda ta wani narke a jikin ta.

Suna zuwa gida suka ga su Mas’ud a parlour an baje ana cin abinci da ta bar musu suna zuwa ta shige daki da ita.

Mas’ud yace, “bros gida kuka dawo ne haka?”

Sai da ya zauna yace, “to ya zamuyi da gidan Anty zamu wuce wannan yarinyar tasa kuka ita nan”.

Mus’ab yace, “maybe sabida mutune ba’a rasa Wanda suka zo ba”.

Zama Binaif yayi a kasa yace, “sauko mana muci abinci”.

Saukowa shima yayi suka zauna suka fara ci harda na mota aka dauko suna ci.
Binaif yace, “idan ka cinye kai da Mi Amor”.

“Ai daman ni ba’a sona a gidan nan kowa ni kowa ni har Karan gidan nan ma”.

Uncle yace, “ai Naga alama rabu dasu kawai”.

Binaif girgiza Kai yayi ya tashi ya zauna yana sha kunan uncle yace, “ya kamata muje gidan Baba Zan dauki abu buwa daga can mu wuce”.

“Ina zaku yaya?”

Binaif yace, ” inda Ka aike mu zamu”

Cuno Baki yayi. Gaba ya tashi ya fara kwashe kayan ya Kai kitchen, yace, “kuma banzan yi wanke wanke ba”.

“Kunfi kusa”.

Gaba de yayi yaje suka yi tare da sannan suka fito.
Mus’ab yace, “yane zaka raka ni?”

“Ina din?”

“Wurin mi amor”.

“Yawwa Kai jiya wai wa Muka gaisar ne?”

Murmushi yayi yace, “siriki na, kuma yau Zan koma”.

“Uhm lalle Kam”.

Tashi Binaif yayi ya Shiga dakin, tana kwance a cinyar ta tayi bacci, zuwa yayi wurin ta ya zauna.

yace, “zamu fita yace ki Kula da ita sosai”.

Hararan sa tayi tare da murguda baki.
Yace, “ohh! Nidin? Zan dawo Naga alama jiya da nace nayi missing anga nayi kadan ko? Bakomai bashi ne wannan a rubuce”.

Tashi yayi zai fita yaji tace, “Ka siyo min ice cream”.

Ko ansawa beyi ba bare tasa ran yaji.

Tare suka fita dasu mas’ud suka ajje su a asibiti sannan suka wuce gidan Baba sosai baba yayi mamakin ganin sa kuma wai an sallame Shi itama Umma tayi mamaki sosai amma Basu wani kawo komai a ran su ba abinda zai dauka ya dauka daga nan suka wuce gidan sa dake ring road Binaif ya Kira ‘yan aiki aka share komai gidan fes yake babu wani gyara da za’ayi sune har wurin furnitures sun kuwa iya zabe kayan masu kyau dasu masu kyau dasu. Binaif ne ya bada shawarar suje wurin Anty Safiya ta hado lefe, sunci sa’a a off take bata da aiki tare suka tafi da ita sosai akayi siyayya a mota ya zauna sabida yanayin jikin nasa Basu suka dawo ba sai yamma likis sun gaji kuwa angama komai da ya kamata.
Anan ummu ta kwana a cewar ta baza ta koma ba indai haka aure yake to ta fasa auren, tunda dare ya fadawa Anty Shifa ya Gama komai kawai gobe a kai masa matar sa Abie kuwa ya goyi bayan sa ita de Umma bata so ba amma hakan zatayi.

Washegari Ummusalma ta Kira Muja anan muja take ce Mata zasu koma kauye tace da Mus’ab ya turo, abin ya bata mamaki Amma tace to shikenan shima yarda aka sa na mas’ud wata biyar shima haka aka sa nashi.

Ba’a akai ummu ba sai da tayi sati ta warke ras sannan aka kaita.

????????????????????????????

Daddy ne zaune a parlour ya Tara yaran sa su hudu Yana musu nasiha Mai shiga rai sosai sai da ya gama.

Yace, “Saima daga yau kune zaku ke aikin cikin gidan nan har ke fati da kike zuwa makaranta kafin ki tafi ki tabba kin gama aikin ki”.

Saima tace, “amma Daddy taya hakan zai faru?”

“Ta yarda ya faru, kuma ba wai a gas zaku yi ba inda ake aikin layya anan zaku yi kunji ai?”

Ya daure fuska tamau hakan yasa su daga Kai yace kuma suje su fara.

Fati tace, “wai yaushe Anty zata dawo?”

Ji yayi murmushi zai kwace masa ya sa Shi Kara Shan kunu yace, “bata fada muku ba?”

Saima tace, “Hajiya ma bata fada ba”.

“To Nima bansani ba”.

Yace, “yawwa Ku tashi kuje akwai iya ladi itace zata koya muku komai da komai da ya kamata”.

A hankali kowa ya fara Mike wa sukam wannan aikin ai wahala ce babu yarda suka iya suna tafiya ya biyo bayan su yaje ya samu inda zai ke hango su suna kallan sa yasan idan ya barsu da ita baza su koya ba tun daga Kan hura murhun kowa ya fara cin kwakwa tun ba’aje ko ina ba, gashi sun dauka Daddy Zai fita sai suka ga sabanin haka dan da aka tafi salla ma wani kasurgumin arne Daddy ya kawo security wanda sam Baya jin Turanci sosai bare kuma hausa babu kuma sauran rahama a tattare dashi ga wani uban kulki da ya rike a hannu ya rataya bindiga a baya tuni suka Shiga taita yin su, kwana daya kwana biyu shiru sune har sati suna aiki dukda suna samun hutu idan sun gama amma kullum sai sunyi safe rana dare kuma a murhu kawo yanzu Kam sun kwantar da hankalin su sun iya ba laifi Dan da zaran lokacin daura abinci yayi wata zata tashi taje tayi Shara Kam kullum da safe kafin aci abinci sai sunyi har fati sun gyara ko ina tuni aikin yabi jikin su sun saba kuma sunyi hankali don Daddy na Zama dasu sosai suyi hira wasa da dariya dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page