A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dago Kai tayi ta kalle ta, yarda take Mata wani irin murmushi har dimple dinta ya Loma, bata san sanda ta daga Mata Kai ba,

Numfashi taja tace’ muyi wani Abu mana?

Ummu yace’ meye Shi yaya?

Ummusalma tace’ ina so ki Zama kawar sameera, Bana San ganin Sameera na yawon zuwa wannan partyn Dan Allah ki taimaka min,

Tace’ amma yaya bakya ganin abinda su Mama suka maki?

Kama hannunta tayi tace’ Ummusalma sunan mu Daya,nasan kuma masu irin wannan sunan suna da zuciy Mai kyau kamar yarda taki take da kyau, kina da kauwa?

Daga Mata tayi,
tace’ to kina so ace kema kauwarki tazama haka?

Shiru tayi tana sauraran ta, tacigaba tace’ ummu tunda ni banzama abinda suke so nazama ba,why not mu Hana faruwan abida ‘yar su zata Zama? Macece fah,kuma kema macece, bakya tunanin idan aka tashi zaginta baza’ayi la’akari da cewan ba Duka aka taru aka Zama dayaba, Amma Duka kudin goro za’ayi mana, ciki kuwa harda ke, ?

Ummu tace’ yanzu mekike so ayi?

Good girl, ina so kizama kawarta, ki hanata aikata abinda takeyi, ki raba ta da Friends dinta, kizama kece kawarta kece sirrinta,kece komai nata kinji ko?

Shiru tayi tana tunani sannan tace’ Amma taya hakan zai faru? ….

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

43

Tace’ sabida me?

Yace’ Shan abun Mai sanyi sosai sanda ake period yana da zubar Shi a bangon manhaifa bayan wasu shekaru, zai jawo uterus cancer or tumor,

Tace’ ya akayi kasani?

Be kamata ba ko? Ni nasani ke Baki sani bako?

Nidai bance ba,

Yace’ cin cucumber ma Yana Toshe wasu abubuwan period a bangon mahaifa hakan na iya sa Miscarriage,

Shiru tayi bata kuma cewa komai ba,
Mas’ud yace’ wai me kuke cewa sai wani kuskus kuke yi kudai, mu ba mutane bane baza’ayi da mu ba?

Mus’ab yace’ menace maka? Daman ai na fada maka dazu dazun nan,

Mas’ud yace’ ai naji yanzu,kaga wannan Mai fuskar masallacin nan kaidai a barta kawai,

Tace’ chatty Ka dameni,Zan sa a ajje Ka, kabani a hankali tam,

Yasan shima ba karamin aikin bb bane ya sauketa shiyasa ya canza maganar da cewa” wai yaushe Ummancy zata dawo ne,

Mus’ab yace’ Umma ita da garin nan sai bb ya haihu,

Sai bb ya haihu ko sai waccan aljanar ta haihu,
Sai kuwa ya dawo tsakiyar su,
yace’ yaushe zaki haihu da?

Juyowa tayi tace’ gobe,

Hhhhh gobe fah, kina wasa kyanta ace bayan sallan cin nama ki haihu, kuyi addu’ah yaran nan yayi kama Dani, zakuji dadin Ku,

Kaga Ka koma baya,kana cika min kunne da surutu kawani zo Ka zauna a tsakiya sai kace wani yaro,

Laaaaa gwara ni ai badaga Baya bakina ya bude ba, ato

Binaif yace’ chatty Ka fita idona, na fada maka Baka ji ko?

bb why chatty instead of Ka hanata fada Amma shine kake fada? Haba bb,

Mus’ab yace’ kaima Ka hakura kayi shiru kaki,

Juyowa yayi yace’ Kai bafa nasan reni, Ka kiyayeni kasan na wuce Ka ko?

Dame Ka wuceni?

Budurwa mana,

Atare su Duka ukun suka saki tsaki, Mus’ab yace’ Amma lalle ma dako hiran Baka iya ba? Kai nifa yanzu Zan iya hira da yarinya, sabida wurin aikin mu wayanci Matane, kagane?

Fada a Baka ba?

Suna yi har suka karaso gidan mus’ab ne yaje ya bude gate, yayi parking suka fito suka Shiga ciki, a parlour suka zauna ta jingina da jikin sa, gyara Mata yayi ya kwantar da ita a cinyarsa ya cire Mata Hijabi, ya fara shafa Mata Kai,

Yace’ bacci?

Daga masa kai, tayi alamar eh,

Yana kallanta yace da su,
Ya aikin Ku,

Mas’ud yace’ aiki ta fara wannan aljanar?

Dagowa yayi ya zabga masa harara,

Mas’ud yace’ a,a fah Naga ita kake kallo to na dauka magana kuke,

Mus’ab yace’ komai Yana tafiya Normal,

Mas’ud yace’ ehh haka ne komai qalau qalau,

Mas’ud ya tashi ya Shiga kitchen ya hado cornflakes yazo Yana sha,

Mus’ab yace’ Ina nawa?

Kace kana so ne?

Amma kasan idan nine da Kai Zan hado ko?

To ban hado ba,kowa yana da hannu,kafa,Ido,sai kaje Ka hado nadena yiwa Gauro bauta ato,

Mus’ab yace’ na Shaka, time will tell,

Shima tashi yayi ya bude fridge ya dauko yaga fruit salad ya a cikin bowl kawai ya dauko, ya dauko spoon, ya fito,

Ya zauna yana sha,

Mas’ud yace’ Kai, meye wannan kake sha? Kuma ko Ka hado Dani ko? Dan tsabar rowa, Bama hadowa kayi ba wannan dauka kayi, Dan banga Ka jima ba,

Dora kafa yayi Akan center table Yana shan Kayansa,sai da yasha spoon biyar ya dago,
yace’ kasa Gauro Shi daya yake hada abincin sa, sai hakuri fah,

Binaif girgiza Kai yayi ya dauketa da ta Riga tayi bacci yayi dakin sa da ita, fitowa yayi ya gansu suna dramar su, ya wuce dakinta ya dauko mata kayan bacci, yazo zai wuce,

yace’ idan kun Gama ga key nan ku dauki nan Ku rufe mana gida sai da safen Ku,

Sun jima suna dramar su sannan suka tafi daki, shima a dakin sai da aka sha rigima da suka kwanta kuma aka fara hira.

Sai da yayi shirin baccin sa tsab yasa mata rigar baccinta dukda yasan ta tashi dama bawani dauketa yayi sosai ba, ya kashe wutar dakin, ya kwanta ya janyota, tana gaba shikuma Yana Baya, hannun sa na yawo a jikinta,

yace’ nafa dauki shawarar Mas’ud,

Shiru tayi irin Mai baccin nan,
Yace’ ohh baza kiyi magana ba ko?
Namma shiru, yace’ to shikenan Bari Nayi abinda bakya so, tunda kinki kulani,

Da sauri tace’ na’am me ma kace?

Murmushi yayi yace’ ai kinji,

To wacce shawara ce wannan? Ya Baka kuma?

Ya kamata ki haihu bayan layya, aikin Santa,

Tace’ kaiko?

Danayi me? Daman Nayi missing dayawa gobe ne ko?

Ehh gobe bakonka zai zo,

Yace’ ba wannan ba,

Juyowa tayi ta kwanta a kirjinshi,
tace’ nikam kadena wannan abun Bana so, wani irin nakeji,ba dadi,
Wanne Abu to tunda ba shiba?

Yace’ yau fah kwana uku,

Wai meye kwana uku,

Kekam Baki da gane Abu Sam, kuma yanzu zaki zo ki cucen, matsa can ki kwanta,

Dariya tayi sosai sannan,
tace’ kafin Ka Rama ba?

Ohh kin gane wannan Kenan ko? Zan kuwa rama,

Rungume Shi tayi dakyau tace’ bacci nake ji kamin addu’a,

Tama sa peck tace’ Saida safe Mai gidanaaaa,

Matseta yayi a ajikinsa yace’ maimaita,

Tayi bacci fah,

Murmushi yayi yace’ to shikenan sai da safe,

Tace’ ban yarda ba, da abinda Ka Shirya,

Nima fah baccin nake ji, me Zan Shirya kuma?

Bata Kara magana ba shima shirun yayi,Yana cigaba da shafa ta, yasan ba bacci zata iya ba,tunda tace bata so, sai da bacci yayi gaba da Shi sannan itama ta yi.

Asuba tagari

????????????????????????

Yaseer yace’ yanaga kin biyo mu Naga daga gidan ku muke ko karatu zakiyi?

Tace’ ehh zanje wurin ya Sameera ne,

Mezata Baki?

Ina ruwanka, bafa nasan sa Ido,

Karasa Shiga cikin gidan sukayi tace’ ina ne dakin ta,

Yusuf yace’ Sama zaki hau,zaki ganshi na farko shine,

Hawa Saman tayi,tana zuwa ta Shiga tare da sallama,tana kwance akan gado ta amsa,
tace’ ummu kece?

Ummu shigowa tayi ta zauna a bakin gadan, tace’ nice ya Sameera ya gida? Ya jikin Abba kuma?

Tashi zaune tayi tace’ da sauki,

Tace’ ya ganki haka? Baki da lafiya ne?

Murmushi tayi kadan tace’ lafiya ta qalau kawai de banji dadi ne,

Ayyyaah sannu, wayarta ta gani a Kan bed drawer hakan yasa ta ajje ta ta, a kusa da ta sameera,

tace’ ya Sameera tuba nayi,

Tuba kuma Ummu neme Kenan?

Kedai Bari, kinsan munyi sauka ai,

Eh,

To kuma kinsan ba hadda bane, shine in fada maki duk na manta wasu wuraren damma wai fah a haka Karatun ya ginu,

Sameera tace’ ai daman indai Baka biyawa to da matsala, zai gudu ne ya barka,

To shine fa nace gwara nazo kike min, shine Mama tace nake zuwa wurinki,tunda kina gida duk dare kamar karfe Tara zuwa goma mun Gama sai su Yusuf su rakani na koma gida Koma kawai nake kwana a nan,tunda yanzu ke Daya ce mama bata nan,daman mama na tana ta so kuyi zancen,itama za suje London gano Uncle Dina, kinga sai muke kwana tare mu tashi tare daman Bani da kawa shikenan Yaya Sameera tazama kawataaaaaa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page