A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’ wai meyasa kike karanta wannan papern ne?
Ummusalma ta kalleta

tace’ ba papern nake San karantawa wacce ta Bani nake so,
Wacece ita?sahr ta tambaya
Kwallace ta zubo Mata ta share sannan

Tace’ I love her, she’s my friend,for me she’s my blood sister,and she she ran away from me,
Muryan ta ne yafara rawa kuma batasan yarda zatayi Mata bayani ba ta gane shiyasa ta fada Mata wannan kalmomin maybe zata iya ganewa,sahr kallanta kawai take tana San Mata tambayoyi Amma tasan she’s not ready to answer all her questions,is better for her tayi shiru, numfasawa tayi ta dafa ta tace’ sorry abinda zata iya fada Mata kawai Kenan ta tashi ta barta. Binta da kallo tayi har ta kulewa ganinta itama tashi tayi ta tattara masu materials dinsu ta fara tafiya kanta a kasa tana tunanin bata an karaba taji tayi karo da wani abu materials dinsu gaba daya suka zube daga hannunta dagowar da zatayi kirjinta ne buga lokaci daya, hawayen da take makalewa tun dazu ne suka sauka Saman kumatunta rufe idanta tayi ta bude sai ganinsa tayi Yana tattare kayansa tare da nata gaba daya,dagowa yayi yasa hannu ya share Mata hawayen cikin wata irin murya mai sanya

yace’ kidinga kallan gaban ki idan kina tafiya kinji ko?
Daman yasan ba magana zatayi ba don Shi duk a zatonsa kurmance da gaske, Mika Mata kayanta yayi

yace’ don’t repeat it ok?
Ita de tasan ta karba Abu Amma batasan meye ba,tana kallan Shi har ya kule sannan ta maida kallanta ga abinda yabata kayan sune ai,ta sa hannu ta ida share hawenta tayi gaba abinta amma wannan Karon nrml tafiya takeyi, tana Shiga taga sahr ta barbaje tana video call da yan gidan su,yau birthday dinta kuma ta manta shine suka Kira ta,ita tasan sahr ta manta ranar birthday dinta don tasan yarda taci buri a wannan birthday din,ajje kayan hannunta tayi ta Shiga wanka,har lokacin waya take da yan gidan su shiryawa tayi tafita balcony tafara zane,har tagama tana jiwo muryan sahr na waya da yan gidan su, lokacin magriba ne yayi zuwa tayi ta alwala data fito wannan Karon ta gama, wanka zatayi.
Bayan sunyi sallah sahr

tace’ yau birthday Dina Amma Baki tuna min ba ko? Kallanta tayi batace komai ba,cigaba tayi

tace’ yau tunda bamuyi abinci ba mu fita restaurant muje muci abinci Kala da Kala,
Tana fada tana daga Yan yatsu tana fari da ido,
Kallanta kawai Ummusalma keyi amma batayi magana ba,tashi tayi tafara shiryawa don idan ba haka ba sai su ja lokaci suna zaune tana shirga masu wani shirmen,ita ma sahr tashin tayi tana shiryawa tana zabga magana ita kadai, doguwar Riga ta zaro guda biyu a kayanta kusan kusan iri daya ce rigar kallan ce kawai ta bambanta,Mika Mata tayi tace tasa,sahr zata iya cewa bata taba sa irin wannan ba kullum cikin Riga da wando take sai Veil kuma Veil din ma a wuya take rataya,sai kuma skirt,karba tayi tace” thank you.
Sosai sukayi kyau ba kadan ba damma sahr ce kawai tasa jambaki, umsalma kuwa ko powder batasa ba,takalmi suka sa iri daya Wanda yanzu kusan komai zasu siya to iri daya zasu saya,Amma Banda kayan sawa,fitowa sukayi suka hau taxi suka fada masa inda zai kaisu.
BĂ yan ya sauke su suka shiga cikin restaurant din Sahr ce taje ta fada musu abinda suke so, bayan ta koma kuwa hotuna kawai take daukansu, sahr tayi tayi da ita tayi ko Dan murmushi ne Amma ina haka ta hakura ta kyaleta,Amma kuma tayi kyau sosai, suna cikin hotuna ne aka kawo masu abincin su Basu ankaraba taga ancika masu table da abinci,kallan sahr tayi kallan irin wazai ci??
Sahr da tasan zancen taki kallanta.tashi ma tayi ganin Basu kawo Mata cake ba,zuwa yayi

yace’ can I ?
Kamar daga sama taji maganar shi,juyowa tayi ta kalleshi yana tare da yarinya bata fi sa’ar su yusseer ba,duk da gabanta ya Dan fadi,Amma ta daga masa Kai, yarinyar ya fara jawa kujera ta zauna shima ya zauna,sahr tana zuwa bata lura da su Bama

tace’ yau saikin ci komai anan wurin sabida yau birthday nane, tana daukar ta hoto,sai da ta zauna sannan ta lura da su gaisawa sukayi don ita sahr Bama ta taba ganinshi ba tunda bata business bare tasanshi, cake aka kawo musu tace su fara ci, baiji komai ba kuwa ya fara ci,itama Ummusalma ci ta farayi a hankali a hankali kamar bata so, AA da sahr kuwa surutu suke kamar da can sun San juna,ita dai kallansu take, kallanta ta Kai Jan yarinyar taga idonta na kan cake din da’alama Shi take son ci don ba abinda taci,batayi magana ba taci gaba da cin abincinta.

Uncle cake zanci ni bazanci abinci ba,
lomar dazata Kai ce ta makale a hannunta ita bata Kai bakin ba ita bata rufe sakamakon Jin abinda yarinyar ta fada . Bata Ankara ba taji

yace’ bazaki ciba tunda naki ne,ya maka mata wata harara ba shiri yarinyar tayi kasa da kanta,
Kallansu Ummusalma tayi daman ya iya Hausa?ita tunda tazo baji anyi Hausa dukda tana ganin hausawa Amma Basu fiye yin hausar ba. Sauke cokalin tayi ta ajje sannan ta jawo cake din ta yanka,ta fara sawa sahr sai Shi ita ma tasa tasawa yarinyar,har aka gama babu Wanda yake magana sai sahr da ke daukan hotuna ko gajiya batayi.sunje zasu biya sukaji wai ya biya kudin,sosai sahr tamasa godiya ita kuwa Umsalma kuwa ko kallanshi bata Kara yiba kawai mamaki take daman Dan Nigeria ne? Har cikin school yakaisu sukayi sallama ya wuce,suna Shiga kuwa sahr ta adda beta da tambayarta waye Shi?

Tace” kinga nasan de ba saurayi bane don kina mugum kama dashi daman kina da yaya anan bansani ba?
Kama?ta maimaita,sahr

tace’ ehh mana ,sosai kuke kama dashi.

Kinga bama kama dashi please kidena wannan maganar ma,
Ganin batasan zancen yasa sahr cewa Naji na daina to ina gift dina kinsan de zaki Bani gift ko?

Dauko wata takarda tayi da tayi ta Mika mata,ta tashi ta wuce toilet,
Budewa tayi taga mene aciki,ganinta tayi a tsaye cikin Riga da wando sai Vail din da take sawa a wuyanta hannunta kuma rike da takardu ta na murmushi,sosai abin ya burgeta,ta jima tana kallan zanen sosai ya kayatar ta,wai yau ita aka zana sai ta kwashe da dariya, Ummusalma na fitowa ta rungume ta tana Dariya,

tace’ waye ya zana yayi kyau kuma na gode,
Bata kula taba ta shirya tayi sallah tajanyo books tafara karatu,itama haka ta gama santin zanenta tayi wanka tay sallah.

    Kwanci tashi akace asarar mai rai su Ummusalma sun Gama  jarabawar su sai tafiya gida,Amma banda ita anan zata  zauna bazata je ba,sahr kuwa sai zumudi take na zuwa gida.

Dawowa tayi dakinsu taga yarda sahr take zumudin tafiya,sai duk taji babu dadi sam,zata tafi ta barta,Amma sai dai kokadan bata San komawa gida, koda kuwa na kwana daya ne, ahaka ta gama shirya kayan ta a trolley,tare sukaje airport din suna zuwa shima Yana tare da wata mata da wani dattijo kana gani zaka ce iyayen sane dukda ba kama suke ba Amma yarda yake kaffa kaffa da su zaka tabbatar da hakan sai wata kuma sai yarinyar nan ta rannan, Allah Allah take kawai su sahr su tashi ta bar wuri,don kallo daya tamasa ta dauke kanta,sai satar kallo kuma da takeyi musu ganin irin nishadin dake tare da su,,su sahr k c na tafiya itama ta tafi.
Duk wayanci kowa ya tafi sai kalilan na nesa dakaffa c tafi ba,Kayan ta take gyarawa Saida tagama tsab ta share dakin ta goge ko ina,Zama tayi a bakin gadon ta dauko envelop din da kudinta suke ciki,kirgawa tayi taga saura kadan kudin ya kare,yanzu ya zatayi? Zama tayi tana tunanin yarda zatayi gashi tana bukatar kudi kuwa shekara shida ai bawasa bane,Zama tayi tana sakawa tana kwancewa, daga bisani ta tashi tayi wanka ta shirya ya fita,tana bin restaurant da store haka ko zata samu aikin da zata iya, dakyar ta samu a restaurant,shima wanke wanke ne daga safe har Azahar sosai hakan ya Mata dadi kuwa, tahowa tayi tana tafiya a kasa taro tagani anyi ita a zatan tama accident Akayi Amma tana Shiga cikin taron Dan ta wuce taga Ashe wai kudi a kasa Wanda zai yi Zane,idan kayi Zane a baka kudi idan bakayi daidai ba Kaine zaka biya,batare da ta yanke shawarata daga hannu,aka ce ta fito kuwa ta fito,aka nuna Mata abinda zata zana,cikin 10 minutes kuma zatayi,takuwa ce zata yi,don ita zanen mutane ne ke bata Mata lokaci tunda kuwa ba na mutum bane alhamdulilla,
Cikin lokaci kankani ta kammala zanen ta 6 minutes ta dauka tanayi ita aganinta ma ta jima tanayi,Amma ga mamakinta sai gani tayi suna cewa tayi sauri,sosai zanen ya samu karbuwa ga jama’ar wurin, ogan ne ya Basu address dinsu incase idan tana da sha’awar aiki tare dasu karba tayi suka bata kudinta dayawa.
Cike da annushwa takoma daki,ta samu aiki biyu Kenan don ba tan Tama sai ta nemi wannan aikin zanen, godiya tayiwa Allah da yabata baiwa wannan zanen,sosai tayi murna da dukda bazaka gani ba a fuskar ta amma Itakam ahakan ji take fuskanta a sake take.
Washegari da wuri ta shirya ta fice wurin aikinta tana zuwa ta wuce kitchen sosai tayi wanke wanke,kuma ita kadai,bata Gama ba sai 2 tagaji kam ba laifi kafafuwanta da bayanta sun gaji bakadan ba,koda ta kwanta bacci juyi kowai take dakyar tayi bacci, washegari ma haka tayi aikinta ta gaji sosai ita sai tagama na yau yafi na jiya,dukda ta gaji Amma haka ta wuce wurin address din nan da aka bata tana zuwa kuwa suka ganeta sunyi murna sosai da sosai, da zuwanta,aiki suka bata tana zanen wani nature,karba tayi tace’gobe zata dawo dashi bazatayi anan ba,fadar inda take tayi da komai da komai nata,zasuke nemanta.
Kafin ta saba da ayyukanta guda biyu ta wahala bakadan ba kullum kuma take zuwa bata fashi tun kafarta da bayanta na ciwo har ta Riga da ta saba,bata fashi,kuma bata makara Akan lokaci take zuwa ta tashi Akan lokaci,Suma kuma daman sun fi San haka don su basu San wani abu ba wai shi African time ba.
Ahaka take samu kudinta ba laifi har aka dawo school,sosai result dinta yayi kyai don babu C B dinta ma befi biyu ba zuwa uku sosai hakan yayi Mata dadi Suma kuma school din sunga kokarinta ba kadan ba,tunda suka dawo bata fasa zuwa aikinta ba Amma kuma sai ta koma na dare daga 6pm zuwa 10pm abinta,bangren zanenta kuwa zuwa take ta karbo zanen idan ta dawo komin dare sai tayi,sai ya zamana lokacinta ya ragu batada wani lokaci sai na aiki da karatu,dadinta ma yanzu sunce tadena zuwa da weekend saboda karatunta hakan yayi Mata dadi.
sahr tayi tayi da ita ta dena taki,ko kallanta ma batayi bare ta tanka Mata ganin haka yasata yin shiru……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button