A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
????????????????????
Mama na zaune a parlour ita a tunanin ta su yusuf sun fita tun jimawa,ganin yanzu har goma tayi kuma tasan suna da school . Itama yau batajin zata fita Sameera ce ta fito ga dukkan alamu baccin be ishe taba, da kayan bacci a jikinta ta sauko, Zama tayi,
tace’ mama yunwa nake ji,
Mama tace’ to saidai ki tashi ki girka don,na bayarwa masu aiki,kuma kila sun tafi dashi,
tashi tayi badan tana so ba,saidai don ba yanda zatayi, indomie ta girka ta fito,tana cikin ci sai ga Ummu nan tazo da sallama ta shigo har kasa ta durgusa ta gaida mama ta gaida Sameera,
tace’ Mama su Yusuf fa? Nakira wayan yusuf a kashe shikuma yaseer baya picking ince dai lafiya gashi kuma muna shirin makara.
Mama tace’ a,ah daman wai basu tafi ba ? Nifa zataci tun tuni sun tafi,jeki ki duba,
Tashi tayi ta nufi dakin,yanda suka barshi ahaka ta same Shi, wayan yaseer akan gado ga missed calls dinta nan rututu, dubawa tayi part din nasu Basu ba alamar su, nan fa ta fito ta fadawa Mama sosai hankalin mama ya tashi,Sameera
tace’ jiya dana sauko don Shan ruwa wurin shadaya saura nagansu suna rigayen fita na zaci ma wurinki zasu zo,
Ummu tace’ wanne wuri na kuma da daddare haka?
Mama bata tsaya Jin ba’asi ba ta fita waje wurin mai gadi,
yace’ ai Hajiya Bansan sun fita ba sai karar bude gate danaji ko da na fito har sun tafi sun bar gate a bude nama zaci wani ne ba lafiya shiyasa,
Aikuwa ta fara surfa masa ruwan bala’i wani abinmma batasan tana fada ba,dakyar su ummu sukayi controlling dinta suka maida ta ciki,waya ta dauka ta kira Abba ta fada masa, bai wani dade ba ya karaso, sosai shima hankalin sa ya tashi kafin kace me gari ya karade ana neman yaran ‘ya’yan M & M da U & U, sai dai babu su babu labarinsu, babu kuma wani evidence da suka bari ko kadan ba, kuma ma dadin dadawa har motar aka dauke, a iya bincike Yan sanda sunce sai dai idan barin garin sukayi tunda gashi ko me irin kalar motar su babu, dajin haka kuwa yan jarida suka fara tambayoyi akan me zai saka su gudu? Shin me aka musu zasu gudu su bar garin, batare da ansani ba? Abba dukda yasan an sanshi a gari Amma baizaci haka kowa yasanshi ba infact baimasa cewan ansan yana da yaya ba sai da wannan abu ya faru, Idan hankalinsa yayi dubu to ya tashi yarasa inda zai sa ransa yaji sanyi.
Yana daki aana kwance yaji wayarsa tayi kara alamar shigowar sako, kamar bazai daga ba sai kuma yadago ko labarin ‘ya’yan sa ne sai dai abinda ke rubuce a jikin message din ya fi ma batan ‘ya’yan nasa tada masa da hankali, zufa ce take karyo masa ta ko ina babbar rigar dake jikinsa ta jike sharkaf da gumi, Ya karanta sakon yafi a kirga, bawani Abu bane da sakon Amma Shi a ganin sa wani abu ne, Mamace ta shigo ta ganshi da kuma waya a hannunsa batayi magana ba ta karbi wayar ta ga abinda ke jiki,
tace’. Alhaji banga komai a cikin wayar nan ba dazaka kara tada hankalin Ka,
Kallanta yake irin bakisan me kike fada ba, kallanta yayi na kallan Baki da hankali kallo na ma’anoni daban daban bema San ya fassara kallanta ba,gani yake ma idan ya bata amsa Yana da lokacinta,
Ganin kallan ya ki karewa ne ya sata,
tace’ haba Alhajina yanzu me aka rubuta a jikin wannan Abun? Abinda ya dace shine mu nemo ‘ya’yan mu daga baya sai mu nemo wannan,nasan wanda ya sace su to tabbas shine zai turo wannan sakon, mene na tashin hankali kuma?
Shi baimayi wannan tunanin ba tabbas ya yarda da ake cewa mace tana da hikima kalakala amma ake cewa sune masa karamar kwakwalwa,dukda haka dai bayarda yayi ba don shi wani tunanin ya dauko Wanda yasa ita bata kawo Shi a ranta ba,kuma bazai fada mata ba har sai ya tabbatar da gaskiyar lamarin.
Beyi mata magana ba ya cire babbar rigar ya tashi ya shiga bayi, wanka yayi ya fito ya shirya ya kuma fita, don jin labarin ko an Samu wani abun kuma, sai dai har dare babu su babu labarin su.
Mama kuwa idan ta kwanta to batasani ba don ko shingida batayi ba abinda take cewa kawai shine yaranta ina suke? ( Sai kace Wanda akace Mata an San inda suke anki fada ).
✨✨✨✨✨✨✨
Tana komawa gida tun daga bakin gate ta saki wata uwar Kara sai da yasa kowa ya fito tana karasowa kuwa parlourn ta zube tana kuka, tana cewa an sace su an sace su shikenan an yanka su,sun mutu, sai da Anty ta tsawatar mata tukunna tayi musu bayani, tana gamawa kuwa ta kuma zubewa tana kuka, daga karshe ma hotunan su ta rungume a kirjinta a haka tayi bacci, sallah kawai yake tada ita daga inda take tana parlourn a rakube kallo daya zaka Mata ta baka tausayi sosai. ( Allah sarki ummu).
????????????????????
Yau ta tashi cikin wani irin farim ciki dukda fuskarta tana nan kamar kullum ba fara’a amma ita a yarda take ji wani irin dadi da nishadi ne yake kwasarta, batasan dalili ba, musamman idan ta tuna Mr lizard ( Binaif), akan abinda ya faru jiya,sai ta samu kanta da murmushi ga kuma su yusseer wanda basu zo ba a jiyan, a haka ta gama aikinta taje taci abinci tayi wanka, koda ta fito gidan bakowa tsit yake, lokacin har sha biyu tayi kasancewar yau bata tashi da wuri ba, kitchen ta shiga ta daura abinci ta dauko silalliyar kaza ta daura ta don ta narke ta soya,tunda tazo ake cin dafaffiyar kaza yau kam ko suna so ko basa su sai sun ci soyayyiya tunda ita tana so, sai da tayi ta soya ta, ta bade ta da yaji, ta dauki na dauka ta rufe sauran a flask, Naman rago ta dauko ta wanke ta daura,tuwo ma zasu ci yau.
Sosai tayi tuwon semo da miyar kubewa bushshiya Tasha manja da nama, Saida ta gama ta kuma gyara kitchen din, bude Fridge tayi ta dauko lemo mai sanyi ta dauko namanta ta fito bakin kitchen din da kofar dakinta tasa takalmi ta baje tana cin nama tana korawa da lemo tsabar dadi har wani lumshe ido take irin yaushe rabo, zuwan shi kenan don yasanar da ita abinda ke faruwa ganin wani sinadarin farin ciki a tare da ita yasa Shi tsayawa Yana doubting ya fada mata ne ko mar ya fada, gashi yanzu sai cigiyar yaran ake, tunda yazo ta lura dashi amma tayi kamar ma bata ganshi ba, karaso wa yayi ya tsaya akanta,dago Kai tayi ta kalleshi, ta maida kanta ga naman da take ci,kujera ya dauko ya zauna yana kallanta, tashi tayi ta Shiga kitchen bata jima ba sai gata tafito dauke da kwano a hannunta tuwo ta zubo masa da naman da ta soya, beyi musu ba ya karba, ta zauna ta cigaba da ci, shima sauka yayi daga kujerar ya zauna a kasan tiles din wurin ya nade kafa yafara zirawa,sosai yaci Saida ta lura ya kusa koshi,
tace’ inaji meke tafe da Kai?
Sosai yayi mamakinta, Kenan tasan da magana a bakinshi, sai da yacinye tuwon tas ya kai kayan kitchen ya dawo ya zauna
yace’ bansan ta ina xan fara ba ai, cewa zanyi an sace Kannan ki ko ya zance?
Kallanshi tayi tace to me Zan masu don an sace su sai me??
Ni zaka fadawa kome ko kuma nice ubansu kaje can ka fadawa babansu amma nani ba,
Dukda cewa ahankali take magana amma sai yaga kamar ranta ya baci daya fada mata din dan yayi wani iri bacin rai yake hangowa karara a tare da ita, tashin da tayi zata Shiga dakinta ya sashi saurin riko hannunta a sukwane ta juyo zatayi magana ya riga ta
Yace’ meyasa? Meyasa zakiyi haka? Why? Fada maki nayi fah don kisan halin da ake ciki amma shine zaki min haka?
Bata Kula Shi ba tace’ menace ma game da rike mun hannu?
Sakinta yayi ta wuce ta tafi ta barshi a tsaye ,ya rasa yazaiyi da ita yana so su Saba kodan tarin tambayoyin dake kansa ya sauke mata su.
Tana Shiga ta kwanta a katifa tana tunanin. Tana Jin ya tafi tazo ta kwashe plate, wanke kayan da suka bata tayi,ta koma bata Kara fitowa ba gudun kar su Kara haduwa dashi, tana Jin yan gidan suna mitar tuwon da tayi Amma bata fito bama bare a zagi iyayenda bata san su ba.