A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ummusalma tace, “a lokacin da su Mas’ud suka bani labarin su tare da naka haka nan naji ban yarda su Hajiya ba hakan yasa na fara aiki a gidan saboda abu biyu na farko sabida Kai na Biyu kuma saboda idan ina aiwatar da komai nawa babu Wanda zaiyi tunanin nice sabida ina aiki a gida.
Zuwa gidan sai ya zama naji abubuwa da yawa Dan game da Kai da Maman ka, sannu a hankali nagane duk wata duk wata suna zuwa wata anguwa duk da wata na Daya a gidan da satittika nagane hakan sabuda zancen da suke yi ga kuma abina suke kulla maka wani zancen ba da Hausa take ba da yaren Bole take kasance war ta yare sai akayi sa’a na iya yaren sanda ina junior sosai kuma Dana ji sai naji ban manta ba duk wani abu da za suyi nasan dashi har business din da Daddy besan sunayi ba nasan suna yi ita da Anty da taimakon kawar su Bari na gidan sai ya Zama na bana Jin komai sai dabara ta fado min na nasa iya ladi aiki a gidan take dauko min maganar su idan da Hausa sukayi zata sanar min idan kuma da yaran su tayi zata yi recording ta kawo min a boye a haka har wata yayi ranar da za’a kai mata nasa Saminu Wanda suka ce su yusseer suka bita har gidan a daren kuwa aka dauko ta aka kawo ta nan”.
Shiru sukayi kowa Yana kallan ta ta dago ta kalli Binaif tace, “Sanka ne yasa ta tafi bar Ka bata a lokacin kana tsananin bukatar ta San ka ne yasa tayi haka bakomai ba babu uwar da zata haifi yaran ta ta tafi ta barshi a ranar Ka godewa Allah Ka samu Anty ummi wacce ta rike ka a matsayin uwa”.
Wani hawaye ne ya digo daga cikin sa a diga akan Pretty yarinya sai ta fara kuka irin tana taya Baban ta kukan farin ciki kallan yarinyar yayi ya tashi ya kai mata ita sannan yaje wurin Maman shi ya zauna a kasa ya Dora kansa akan cinyar ta sai kuka kasa jurar kukan sa tayi ta tashi ta fice daga gidan ma gaba Daya ta koma gidan Maman Sadiq tana zuwa Ummu ta karbe ta ta goya ta Zama tayi itama ta fara ci abinci.
Neena tace, “ina kika je?”
Harara ta zabga mata tace, “inda kika aikeni”.
“Haba Salma Dan Allah wai tunda muka hadu fa babu wani zancen arziki da ya taba hada mu wai laifin me nayi maki Dan Allah”.
“Mtsww tambaya ma kike? Bakiyi komai ba”.
“Haba dan Allah idan dande naganki har sau dayawa ban maki magana ba kiyi hakuri komai ya wuce ai yanzu”.
Banza tayi mata bata amsa ba wato har sau dayawa ma ta ganta amma ba magana hakan yasa ta Kara kume wa da ita kadai tasan tayi abin ta sai da maman Sadiq tasa Baki sannan tace ta hakura.
Mama kuwa itama kukan take ta kasa hanashi bare itama ta Hana kanta,dakyar ta samu.
tace, “kayi hakuri Abdul am sorry”.
Kukan ya tsayar ya dago Yana kallan ta, goge mata hawayen yake yi itama ta fara goge masa a tare suka sakar wa da juna murmushi.
Tace, “yaro na Ka girma ko?”
Murmushin Jin kunya yayi ya dauke Idan sa daga gare ta, ya maida kan sa cinyar ta ya kwanta yasa da’a ce Anty ummi ce Kan sa zata fara shafawa haka ma Ummusalma sun San abinda yake so, murmushi kawai yayi ya lumshe Ido.
Tace, “bansan irin godiyar da zan yiwa matar Ka ba ban san mezan ce mata. Amma Ka rike matar Ka dakyau ta Kai duk inda ake so mace ta Kai ya hada komai kuma ta maka komai ba kowacce bace zata ji labarin Ka ta shigo cikin rayuwar Ka ba amma ita tayi hakan, Abdul idan ka butulce mata baza ta Kara yarda da kowa ba ka, itace ta silar hada mu, tasa sunana tun kafin ta hadu dani, and Abdul Karka biyo ni halina na zurfin ciki beda amana beda dadi sai cutar da Kai da wauta da sa mutum nadama duk Mai irin halina Ka bashi shawara da ya dena”.
Shiru tayi bata yi, sannan ta kawar da duk wani Abu da take ji.
Tace, “labarin Ka fa”.
Murmushi yayi Idan sa a rufe yace, “labari na Mai dadin jine amma labarin ta beda dadi ji sai dai na Baki shi idan zaki ji”.
“Nace bazan ji ba? Ina san ji”.
A hankali ya bata labarin ta tsab har kawo haduwar su da Iyayen su komai ya fada mata.
“Allah sarki sai gashi yanzu kamar ma ba’ayi ba haka rayuwar take”.
Dagowa yay ya kalli inda take ganin bata nan yasa Shi maida kansa cinyar ta labari suka shiga yi be fada mata anty ummi ta rasu ba sai dai tana san tambayar sa amma tayi de shiru sai aka kira magriba suna nan sai dai idan an Kira sallah suje suyi tare suka ci abinci tana bashi a Baki du sai yaji wani iri be sababa Amma da matar sa wannan normal ne kawa ita din ce be sa ba sai Duka gama.
Yace, “ya kamata mu tafi nasan ana ta kirana wayan na mota ki taso mu tafi”.
Baza ta iya musu musu ba tace, “to Bari na hada Kaya na”.
Yace, “wanne Kaya kuma Mama? Ki Bari kawai tunda gidan zaki Bari”.
“Sabbin kaya tasa a din kamin fa kwati har uku kayan sallah ma akwati guda aka min kuma kace na barshi?”
Yace, “to muje na dauko maki”.
Sai da suka fito da kayan Duka ya zuba a but sannan ya Kira ta yace su fito su tafi,
Suna tafiya ya Kira Daddy yace si hadu a gidan Baffa yasan su Baba na can tunda safe suka je kuma yasan sai dare zasu koma suna, sude su Neena daga Kaida da Sukayi shikenan Basu kuma ba.
Daddy ya Riga su zuwa sabida Shi a hankali yake tafiya, suna zuwa Kowa ya fita Mama kuwa kallan gidan take tana mamakin ina suka zo su?
Kowa ya fito suka Shiga sune karshen Shiga aikuwa kowa Yana nan har su Fati Umma ma tana nan Daga Binaif sai ita.
Hakan yasa Daddy cewa, “kazo Ka ajjeni anan ina da abin…”
Bama tsayawa yayi ba tashi tsaye yayi ganin wacce yake kallo bakin sa ne ya furta.
“Laihat?”
Sunan da baza ta manta sunan da abin kaunar ta yake yafada Mata Kenan Laihat kowa kallan sa ne ya dawo wurin Ummusalma kuwa Sama ta hau Dan ta huta tayi bacci kafin anjima cikin dare pretty ta tashe ta.
Kowa yayi mamaki sosai da sosai sai da aka nutsu sannan Binaif ya fada musu yarda akayi itama ta fada musu, namma fa kowa ya shiga fada masa sunan sa da waye shi ita kuma kawai tana murmushi sai da kowa ya gama sannan mas’ud ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna a kasa.
Yace, “ni sunana Mas’ud yayan Aljana Salamatu matar bb yaran ki kenan, kuma a matsayi na sirikin Shi yayar matar Shi baya ce min Yaya har itama sai wani Chatty suke cemin kamar wani cinnaka kuma ko? Na fada maki Mama nanda jibi za’a daura min aure Nima na….”
A tare suka masa rufdugu su uku Binaif da Uncle sai Mus’ab.
Tace, “me yayi zaku jefe Shi haka?”
“Laaaa mama ai indai sune haka suke min da Basu Zane ni Bama? Ai su suke ramar ni”.
Murmushi tayi Dan sosai Mas’ud ya birgeta kuma ya Shiga ranta sosai nan da nan suka saba sosai sukayi hira da yaran sannan suka tashi suka hau Sama suka kyale manyan, Baba ne ya nemi da a hada auran ta Dana su Mas’ud tunda gobe su Inna zasu zo bikin zaiyi waya a zo har Baba.
Washegari kuwa sai su Inna sosai anyi kuka anyi dariya sun kuma godewa Ummusalma tare da Iyayen ta Saida komai ya lafa kuma aka hau hira.
Suna Sama suna zaune sai ga Mas’ud da Mus’ab da kayan wasa harda mota ta Shiga irin ta yaran nan sun shigo da ita kowa kallan sa ya fara yi.
Neena tace, “Ya Mas’ud wannan?”
Yace, “dalla ta genios ce ta fara shiga”.
Ummusalma tace, “yarinyar da bata fara Zama ba balle ta Shiga a tura shine zaku fara koya Mata gagara ko?”
“Ke ‘yar ki ko ‘ya ta”.
Binaif yace, “Allah ya Baka Hakuri Yaya tuba take”.
Zuwa yayi ya dauki yarinyar ya fara daga ta Sama Yana Mata wasa shikadai sai can ya gaji ya zauna.