A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sakar Baki sukayi suna kallan sa, Zakiyya tace’ shikenan angama da shi,an masa kulla kulla daman nasani ai ba’a banza ba, wallahi,

Shiru sukayi babu Wanda ya tanka Mata samun wurin sukayi suka zauna suan jiran fitowar su.

Aka gado ya ajjeta yafara goge Mata hawayen ta,
yace’ kiyi hakuri kinji?
Murmushi tayi Mai kyau tace’ bakomai ai, komai zai wuce,
A zuciyar ta tace komai zai wuce idan na koya masu hankali, zasu San sunyi da Ummusalma,

Murmushi yayi Mata ya zauna a kusa da ita ya tallafo kanta har suna Gogan hancin juna suna Jin numfashi juna,ita de kulle idanta tayi sabinin Shi dayake kallanta, dankwalin ta ma ya zame Mata Shi,muryan can ciki ciki,

yace’ kin hakura?

Daga masa Kai tayi,
Murmushin mugunta yayi, don kawai ya mantar ta damuwar dake damunta,
yace’ namaki magana kina daga min Kai ko? Dazu kince min uhm uhm, mekenan?

A hankali ta bude ido tayi sauri ta mayar ta kulle ganin irin kallan da yake mata,
tace’ a,a fah,

A,a me?
Wai mema yake damun kine?

Nifa bakomai,

Bakomai?

Daga masa Kai tayi,

Wani murmushi yayi yace’ laifi biyu, kinki kallo na kince na koma dodo, na biyu kince….

Ware ido tayi tace’ a,ina? Yaushe na fada?

Yace’ ya Zama uku,

Tace’ wallahi bance ba,babu abinda nace,kawai kace wai nace,

Yace’ naji wannan,

Yarda fah?

Ahhh shima ai,naji na kasa yarda?
Yace’ yawwa jikin yadena ciwo ko?

Har ta daga Kai,tayi sauri tace’ ehh ya jimama da denawa ai, kwantar da ita yayi ya bi shima ya kwanta ya Dora kan sa a kirginta ya rungume ta kamar yarda take masa, ya kuma Kara Dora Mata kafa ya kanainayeta
yace’ Tunde jikin ya dena ciwo yau akwai new harka, what I mean,basai na fada ba, kin gane,

Tace’ ni wallahi bangane ba,

Daman haka nake so karki gane, Amma kina so ki gane?

Daga masa Kai tayi da sauri tace’ eh,eh,

Kamshin jikinta gabadaya yasa masa kasala,har wani gyara kwanciya yake, shiru yayi itama tayi shiru ganin fa ita take cutuwa,

tace’ Ka dagani, zafi,ciwo,

Banza yayi da ita,sai ma Kara gyara kansa da yayi,
Tace’ Ka daga ni, ciwo fah,

Yace’ kedawa kike magana,haka?

Dakai mana,

Yace’ a,a bade Dani ba,

Tace’ Haba Mai gida,Ka daga ni mana Allah da zafi gashi kaki kwanciya daidai,

Yace’ ina haka kike min kema?

A,ah de,kaji ma an Kira sallah Ka tashi Ka tafi,daman Baka taba zuwa ba,

Yace’ bakomai ai bansan wurin ba shiyasa,
Amma to da kike cewa na daga ki ciwo da zafi,idan har kin nuna min wurin Zan daga, idan ba’a nuna ba kuma nacigaba da kwanciya,
Yafada tare da gyara kwanciyar sa, a jikinta,

To kada gani Zan fada,

Dariya yayi yace’ yarinya Kenan sai da na bushe anan gidan duniya sannan kikazo,Dan haka ba wannan zancen,

Wayyo kadaga ni, to, Allah zafi, kuma wani iri nakeji ba…..
Sai tayi shiru bata karasa ba,

Dago kansa yayi ya kalleta, ganin yarda take wani juya kai a Kan pillow idanta a rufe,ta Shi zaune yayi ya Dora hannunsa a Kai irin besani din nan ba,

yace’ to ai Naga meye kike juyi da Kai irin dadin ko?

Hannunsa zata cire ya rike hannun
yace’ babu wannan zancen, dorawa hannu fa kawai Nayi shima hannun zafi?

Daga Kai tayi, tan lumshe Ido, wannan ai cuta ce, matsawa yayi yace’ daga Kai ko?

Bude Ido tayi ta tashi zaune tace’ Allah da zafi kawai Kai sai kayi ta wannan kayi ta wannan nidai a,a,

Sauka tayi tace’ nidai Sallah zanyi, da Ido ya bita sai da ta Shiga toilet ya kwanta ya lumshe Ido

yace’ zakiyi bayani, wasan yara akayi,bakin ki garau ba, hmmm.
Yana kwance ta fito daure da towel ta yafa wani akai, tasowa yayi,
yace’ meye na wanka kuma? Kuma ni Banji kamshin soap ba, kuma Naga de babu abinda akayi,

Turbune fuska tayi tace’ zafi naji fah,shine kawai na kora ruwa,

Zafin ne harda su Kai kuma?

To mene na tambayar wai?
Ta daure fuska kamar ba yanzu zatayi kuka ba,

Yace’ Ana aasfi ya Madam,

Shima ya shiga, yayi wanka lokacin tasa jallabiyar da wacce tasa da asuba, ta tayar da sallah shima goge ruwan jikin sa yayi ya tayar da sallah, sai da suka idar yace Yana zuwa ya fita,

Yana fita yagan su a parlour ya daure fuska
yace’ Mariya Ki kwashe iyalanki Ku barmin gida,koda wasa koda wasa koda wasa wallahi kada Ku Kara tako min koda kofar gate din nane, Idan ba haka ba,hmmmm duk abinda na maku ku kuka sani,

Tace’ Binaif ni yayarka kake fadawa haka? Kasan me matarka ta mana kuwa?

Yace’ kome ta maku kuka sani, abinda na gani kuma nasan zaku aikata dashi Nayi amfani ku tafi nace,kafin kuga Yara Ku da Ku kanku a titi,

Khadija tace’ lalle dole kace haka mana, banza mijin tace Ku tashi mu tafi aikin banza a hofi kawai,

Sun tashi hae sunje bakin kofa yace’ kuma wannan abincin da yaranku suka ci fah? Sweetheart ce taci da zan kwashe ko kuma ‘ya’yan Ku?

Habiba ce ta dawo tace’ Ai kasan bamu san kitchen din ma shiyasa, yace’ sai Allah yayi nasan ku da sa’ido ko a kwashe cikin salama ko kuma de….hmmmm ya koma ya barsu a tsaye a wurin sunyi shiru, Habiba ce ta kwashe sannan suka tafi.

????????????????????????????????????

Bayan sun gama waya ya jima Yana juya maganar Binaif me Kenan?…

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

38

Ya Rasa yarda zaiyi? Yasan Yana San Binaif,Baya so yake nuna son sa,yanzu ma Daya aka Kaya?
Shiru yayi Yana tuna abinda yace masa yanzu,dole ya dau mataki kafin yazo yayi wani abun.
Har lokacin meeting din su na jam iya Yana nan Yana tunanin mafita, sai da yamma ya nufo gida.

????????????????????????????????

Kwankwa sawa suke babu sararawa, yusuf dake cikin mota me yake inba dariya ba, addu’ah ma yake Allah yasa Kar a bude,

Yaseer yace’ wannan amarya ina, bata hadu ba,

Ummu tace’ Ina kuwa ta hadu tazo ta rufe gida ko wayace Mata ana rufe gidan Amarya?

Yaseer yace’ cigaba da kwankwa Sawa,Bari ma asa dutsi yarda zata ji,

Dutsi suka dauko suke yi, sukeyi shiru, tsayawa sukayi Dan hutawa, Ummu tace’ Allah ya so mu ma yamma ce da tuni ta shanya mu,

Yaseer yace’ so take ta looser sweet da chocolate,

Ummu tace’ mu kuma mu looser Alkhaki?

Dariya sukayi, yace’ nifa najima banci ba,

Tace’ Nima haka,

Kamar daga Sama sukaji ance, ku gyara a bude maku,

Juyowa sukayi a tare suka ce Yaya?

Murmushi yayi yace’ to ku matsa, bazata ji ba tana can ciki,

Bude masu yayi yace’ ina Yayan naku,

Yaseer yace’ Ka ganshi can a mota, yayi parking a kofar gidan can wai Dan kar ace tare muke,

Murmushi yayi yace’ Bari na bude masa gate sai ya shigo da motar jeka ce masa ya shigo,

Zuwa yayi ya fada masa shikuma ya bude gate din, Ummu ta hau kan Dan step din dake kofar parlourn ta tsaya shima yaseer zuwa yayi ya tsaya
yace’ kinga gidan nan harda wurin yin ball? Zakiyi ?

Tace’ daga zuwan mu ko? Sai an nuna halin,

Yace’ kuma basa bawa zamuyi da matar ba? Kinga sai muke zuwa,

Tace’ kaima kasan hakan bazai faruba,kasan yayan Fati ne kuma yusuf bazai zo ba,

Zaiyi magana yayi shiru sabida ganin su da yayi sun taho, karasowa Yayi ya bude musu gidan suka shiga wani kamshin dadi sukaji su Duka sai da suka ja ajiyar zuciya daman daga makaranta suke,sun gaji sai sukaji daman su kwanta su huta,

Yace’ ku zauna bari na Mata magana,

Zama sukayi Ummu da yaseer a kujera Daya shikuma babba aka a one seater aka wani kame Yana latsa waya, Ummu ta matsa kusa da yaseer cikin Dan rada rada,

tace’ Dan Allah gidan nan be maka kyau ba?

Shima cikin rada radar ya Mata magana,
yace’ nifa duk field din yafi min kyau,zamu ke zuwa da weekend Muna buga game ko?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page