A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bakomai kawai yanzu abun ya Fado min,

Yusuf yace’ finally yanzu kin dawo kamar da ko?

Murmushi kawai tayi tace’ da dimma bansan mezanyi ba, Amma yanzu nasani,ji nake Bana da damuwa Sam,

Sai da suka Dan taba hira sannan suka tashi suka tafi, lokacin har an kusa magriba, part din shi ta shiga tagan Shi a parlour Yana aiki a system, wayar taje ta dauko ta zauna a kusa da Shi ta daura kanta a kafadar Shi tana kallan abinda yake, aiki yake a cikin system Dinshi kamar na office Dan harda Zane Zane tagani yanayi,
Waya tayi take Kira shiyasa batayi magana ba, kuma ba’a daga ba, zata Kara Kira aka Kira, daga can aka ce,

Talaka kawai meyin flashing kinsan mu kudin wayar mu Baya karewa, menen zaki kirani eh? Kizo ki kafa yiwa mutene dinkimkim kina yin shiru ehh? Baza kiyi magana ba?

Tace’ ohhh Dan na yabeka kayi aiki mekyau shine zaka kake fada min magana ko? Ta kaci gaba kasan Idan Ka bata Mata Rai zai fada ma kabata hakuri,

Yace’ Haba lil sis kinsan yarda nake kaunarki kuwa,

Kake kaunar ta de,

Ahh Dan Allah ruga min asiri ba haka bane ba, wallahi Bana Santa bamma San mene San ba,

Tace’ to naji,
Ya akayi? Kaje?

Yace’ najeni,wasu Kaya ne za’a shigo da wasu,yau din nan aka kawo su, engines ne da machines, sai kuma wani sabon business da zasu fara iya su manya,na Kaya Sawa Suma sunzo, sannan kuma company din ya samu karbuwa har a Chicago to yanzu sun hada hannu da su, shine fah Akan wannan aka wani ce babu aiki, yau,

Tace’ okay, a wannan aikin da zakuyi na satin nan Ka tabbatar da anyi komai ba daidai ba,yarda wa’ancan zasu ji labari,nasan sunsa kudi,dayawa dole kuma sai an biyasu kudin su, sannan ka tabbatar business din nan ba’a fara ba,

Taya Kenan zanyi hakan?

Kai kasani, kuma,
Tace’ kaifa physics Ka karanta ina?

Yace’ ehh,

Tace’ to kayi aiki dashi mugani anan,
Ta kashe wayarta,

Ta Kira Mus’ab sai da suka gaisa cikin mutumci yace’ komai Yana tafiya yarda Muka tsara lokaci kadan ya rage komai ya kwabe,

Tace’ hakan yayi kyau glip kaci gaba da kokari,

Yace’ ok,ina mijinki?
Yana jinka,
Ki gaidashi,
Sukayi sallama ta kashe,

Tace’ wai daman kana aiki ne?

Yace’ ehh mana,

Tace’ yayi kyau, wannan ginin na meye?

Yace’ tambayar fah?

So nake nasani,

Yanzu fah kinfiye magana dayawa,

Tace’ idan kuma Nayi shiru ace Nayi shiru ko?

Yace’ a,a,
Yace’ yanzu kin danne min kafada idan na Rama ace ba haka ba,

Tashi tayi tace’ kama ji an kira magriba Ka tashi Ka tafi,kuma karka jima,
Ta tashi ta tafi dakinta, tayi alwala tayi sallah bedawo ba har tayi Isha tayi wanka ta Shirya tadawo parlour ta zauna tana Zama suna dauke nepa takaici ya kamata,ta cika tayi fam, ta leka dakinsa shiru, kwafa tayi ta koma daki ta kwanta ta kashe fitilar wayar ta Kenan taga an medo da nepa,kin tashi tayi ta kashe wuta ta rufe ido taji ya turo kofar dakin, ya shigo daga Shi sai vest da gajeran wando, gadan ya hawo,

yace’ Lafiya?
Banza tayi da Shi,

Yace’ ok Bari nagani ko wurin da aka ce Yana zafi ko ya dena,

Tashi zaune tayi rufe Ido ta fara ruwan masifa yafita ya barta ita kadai a gida, ba kallo ba komai, bata Kai karshe bata ji ta hade bakinsu, Yana Mata wani irin salan Abu data kasa fassara Shi,Tama kasa gane kansa, su Ummusalma anji bakon yanayi tuni ta fara karbar sakon itama,abunda yake Mata jiya nafila jiya batani komai ba Ashe kukan dadi jiya tayi yau tayi na dalili yau tazama cikakkiyar Mata jiya kawai sha’ani aka sha,bata sani ba, yau ake bidiri.

????????????????????????????????????

Tana kwance tana juyi a Kan gadan dakin tun sanda suka sato ta bata Kara ganin fuskar ko Daya daga cikin su ba, yau kwana biyar zuwa hudu Kenan kullum sai dai a kawo Mata Kaya abinci, yakasa gane inda aka kawo ta. Tayi tunanin sune suka sauya mata wuri Ashe basu bane, Tambayar ta anan shine INA AKA KAWOTA??

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

40

Inni tace’ kina San Ji? Kina San Jin dalilin hadaki da ita?

Neena tace’ Inni ba’iya kadai inasan jiba,ina San Jin dalilin komai ma, ina san,…..

Baffa yace’ Ummusalma bakowa bace a gareki face yayarki, Ummusalma iya kawa take a gareki ba,

Kallansu take kallan irin mekuke fada haka?

Inni tace’ Amina bake Daya muka Haifa ba, mun haifi Rai har hudu kafin ke, kina da yayu Maza guda uku sannan Ummusalma,

Tace’ banfa gane inda kuka dosa ba,

Baffa yace’ bazaki gane ba,

Shiru kowa yayi tana juya maganar su, to idan hakane suna ina?

Asalin mu ‘yan kafacan ne dake kaduna, Na kasance ni Daya ne a wurin Mahaifina, ina karami mahaifiyata ta rasu, na taso da shakuwar Mahaifina haka shima ya shaku Dani sosai, har na Kai shekara goma a lokacin Yan uwan sa suka dameshi da yayi aure, daga nan yayi aure tunda yayi aure alakar dake tsakani na dashi ta fara nesa, ganin haka sai makwabcin mu Wanda matar sa ke kula Dani,duk wani da uwa keyiwa dansa to itama tana min wannan abun, Baban Umar ya dauke ni ya mayar Shi wurin Shi dukda idan na dawo daga makaranta har yamma ina nan sai dare nake komawa, har na dawo wurin Shi da Zama gaba kidaya yarinyar Shi babu abinda muke da ita sai fada, Maryam kullum muna cikin fada da ita, gashi makarantar mu daya aji ne kowa da nasa, ko a makara Allah ya zuba Mata tsokana idan tayi sai ta taho wurina na tare mata,amma da zaran ance mun koma gida sai fada babu jituwa a tsakanin mu.

Wata rana mun munje makaranta a lokacin ankawo wani sabon zuwa Mai suna Mahmud, an fita break duk Wanda yasani to yasan Maryam duk ‘yan ajimmu sun Santa ko a wurin tsokanar ta,kuma sun San kauwata ce,
Tazo a jin mu nemana bakowa ajin sai Mahmud saban zuwa nan, Yana note Tace’ Kai Dan Allah ina yayanah yake?

Banza yayi da ita wai tace masa Kai,
tace’ wai Kai ba magana nake maka ba? Ina yayanah kanaji kayi shiru, Yayanah Muhammad nake cemaka,

Yana tashi ya kifa Mata Mari, yace’ waye Kai din,amfa damaki nasan inda yakre ko ance maki nasanshi, wuce ki ban wurin marar kunya,

Wannan Mari da yamata Shi yafi komai tsaya Mata a Rai, Sai da ta nemoni,tana kuka ta fada min yarda akayi, ina zuwa Nima na dauke Shi da Mari,Akan me zai Mari kauwata, daga nan fada ya kaure a tsakani mu, na masa Duka ya Kai karata,Nima aka dakeni, da muka je gida lokacin Babana yayi tafiya, Baba Umar yace’ muje mu mu masa sannu da zuwa da yamma kuwa mukaje nida Maryam, Ashe Mahmud Dan matar Baban mu ne, ban saniba, sabida ban taba ganin sa ba, muna Shiga yace’ ai nine na masa duka, baba bebi ba’asi ba ya kamani ya jibga a gaban Maryam Ashe Maryam ta nade abinda ya fada masu, muna fita tayi ta Bani hakuri, nace Mata bakomai, muka koma gida jikina duk ciwo tace’ Bari taje ta Kira Inna, nace Mata to,Ashe da ta fita Gidan mu ta koma, a zaure ta tsaya tace’ wai ana Kiran Mahmud, gudu waje, Mahmud na fitowa ta dutse ta kwada masa ta fasa masa Kai,bata barshi ta kuma bula masa kasa ta buga masa warning tayi tafiyarta, tundaga nan muke fada da Mahmud ba wani ba wa Maryam ba, har girman mu na kammala secondary school dina, na samu BUK Amma Baba yace bazani ba, Mahmoud ne zashi yafini kokari bazaiyi asarat kudin sa ba, banyi musu ba sukayi cuwa cuwan su komai ya komai na Mahmud Bana Muhammad ba, Baba Umar ya samu min diploma a Kaduna dayake Allah yabani baiwar zane sai yace na Karanci fannin zanen, banki ta tashi ba nafara karatuna,har shekara uku lokacin Maryma ta gama makarantar ta, a lokacin kuma Mahmud dayazo hutu yace Maryma yake so, Baban mu ya nemi da ba’a Shi Babanta yace zaiyi shawara tukunna, da tambayeta wanda take so tace ita babu Wanda take so, yayi yayi amma tace babu,kowa ya aura Mata zata zauna, ta dauka ni za’a aura Mata bata San Mahmud bane, sai da Baba ya tafi nake fada Mata Mahmud za’a aura mata, tace batasan zancen ba,da kanta taje ta samu Baba ta fada masa ita ni take so ba Mahmud ba, haka yaje ya samu Babana ya fada masa yayi hakuri,
Bayan auren mu da wata biyu baba Umar ya samu min aiki a Lagos yace na tafi can, tunda Noma daman nakeyi da gonarshi, a haka akayi muka tafi da iyalina, acan na fara aiki ina aiki dai kuma na fara kasuwanci daga nan na fara canji, shikenan hanyar kudi ta fara budewa har nafara fita kasa she, daga nan kuma na fara gina shaguna na canji, da abubuwa har na fara aiki da turawa suna zuwa suma suga yarda ake aikina, daga nan wani bature ya Bani shawarar Nayi company a kasar su,zai Kula min dashi tunda na kasa yi a kasata, koda Nayi shawara da Baba Umar yabani Gogan bayan yin haka haka ma, Inna banki ta tasuba nayi muka fara har aka Gama shine ya tsaya Akan komai akayi aka gama,ana gamawa na dankawa matata Shi, bata so ba,Amma Felix wannan baturen Shi ya karfafa Mata gwiwa ta ansa, tunda ganan kuma na fara gina company da shawarar, da ikon Allah kuwa kasuwa ta bude ga aikina ina samun nasara, gashi kuma na Karo karatu.
Wani zuwa hutu da mukayi Baba yace ga Mahmud ya Gama makaranta amma babu aiki, result dinshi beyi kyau ba sabida haka na Bashi wani shago yake Kula da Shi, na ginawa Baba Umar shago da Baba, banyi musu ba nace yake Kula da companyn Abuja Wanda ya Gina ba jimawa,
Bayan wani lokacin Allah ya azurta mu da haihuwar Umar ranar da aka haifeshi ranar na mallaka masa wani fili babba a garin Lagos, lokacin Mahmud yayi aure,kuma a lokacin sunzo Lagos shida matarsa da yayar matar sa, washegarin da ta haihu za’ sallame mu,sai ga su sunje ganin yaron, a asibiti Yana dakin da ake ajje jarirai, sukaje ganin sa, bayan yayar matar sa ta tafi aka ce wai yaro na ya yarasu, koda naje sai naga bashi bane,sabida Maryma tasa masa wani Dan box acikin towel din Shi,Wanda ta siyo a Paris da mukaje, tayi kuka taso ayi bincike amma baba Umar ya Hana yace haka Allah ya kaddara, Bayan wani lokaci Allah ya bamu ‘yan biyu Mas’ud da Mus’ab, daga nan aka min transfer zuwa Abuja na koma Abuja da Zama shikuma Mahmud ya koma Kano, duk wani kulla kullan Mahmud nasan yanayi,duk wani cuta da cuwa cuwar nasan dashi kawai Nayi shiru ne, nasan Bani yake cuta ba kansa yake cuta kuma da ikon Allah sai Allah yayi ban taba faduwa ba sai ma gaba da nakeyi, Nasan na Allah basa karewa, ‘yan biyu suna da shekara hudu Allah bamu Ummusalma, tunda ta taso Allah yayi ta da tsokana da fada tun tana rarrafe Sam basa jituwa da Mas’ud dayake Shi Sam beda hakuri koya ta ya kushe she sai ya rama, sabanin Mus’ab da duk inda yaje sai ya kawo Mata alawa, har tayi shekara biyu tana maganar tana gudun ta ko ina ga tsokana babu Wanda take yiwa sai Mas’ud lokacin tana cemasa Masud wai mas’ud, shikuma yayi ta bala’i, Baya amsawa, idan be amasa ba kuwa to ya Shiga uku tayi tabinsa tana Kiran sunansa kenan, kuma tayi ta makale masa idan sun dawo,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button