A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Asuba tagari 

????????????????????

Alhaji lamarin yarinyar gaba yake yi ba baya,
Kallanta tayi

yace’ meyafaru kuma,

Wai yau ina Mata magana yarinyar nan don ta renani nizata yiwa shiru ina Mata magana? To infada maka yau ko daga kamma da ta Saba batayi ba,bifa gaskiya nagaji wallahi a toh a San yarda za’ayi atoh
Kallanta kawai yake,don zai iya cewa shikam ya gaji da ita ya kagu ta kawar da kanta daga garesu.
Numfasawa yayi sannan

yace’ wato saratu ke naki duk mai sauki ne ni abin dake daga min hankali karatun ta, wanne course zamu turata ta karanta?

To wezai hana karanci bagaran lafiya kaga tunda bawani kokari ne da ita ba bazata fito da result me kyau ba kuma ba asibitin da zai dauke ta aiki,

Hakan yayi idan lokacin yayi sai a nema Mata Oxford university ko?
Amma de kinsani da sauran lokaci tunda befi sauran one month ba su fara exams ba,

To shikenan Allah ya kaimu
Ameen ya furta sukaci gaba da kulla kullansu.

 Washagari da wuri tayi Shirin makarantar ta fito lokacin 7:10 bakowa a parlourn sai mai aiki datake gyara  parlourn,ta fita

Drivern tane ya taso suka tafi,
Bakowa a class din sai ita tazauna a seat dinta ta fara karatu kamar kullum har aka fara shigowa Amma ba Neena ba labarinta,abun ya bata mamaki ta kalli agogo taga 7:45 Amma bata zoba ahaka de har teacher ya shigo ya fita bata zoba har akayo Break fitowa tayi ko zata ganta tunda jiya tace tazo late bata Shiga class ba haka ta gama zagayen ta tadawo ta zauna a class, biscuit dinta ta dauko ta fara ci ta kalli ledan chocolate din Neena a zuciyar ta

tace’ yau ma ina kika zauna,jiya kin fada min karya yau kuma mezaki fada min ?
Kallan ta gabanta tayi ta Kai hannu ta tabo juyowa tayi ta takalleta alamar Mene? A hankali

tace’ Don Allah kinsan gidan su Neena?
Neena? Ta maimata sunan
Ganin bata gane ba yasa

tace’ i mean Amina

Ca tace’ Mata ehh nasani menene?

Idan an tashi zaki raka ni Don Allah

Da wuri ake zuwa daukana saidai ki jira idan anzo dauka na fada
Nodding kawai tayi.

Ana tashi kuwa suka fita Basu jima ba aka zo daukar dayar ta fada to kawai drivern yace.
Basu jimaba drivernta yazo suka shiga suka tafi dayar ce tafada masa inda zasu,ya kaisu unguwar tana masa kwatance har suka iso kofar gidan,

tace’ kinga gidan munzo,kallan gidan takeyi sosai gidane gidan rufin asiri Amma kuma duk a kwarkwarje gidan yake,duk da Neena bata bata fada Mata ko ita Wace ba Amma kuma a yarda take bata labari tasan bamasu kudi bane Amma batayi tunanin haka gidan yake ba ai,fitowa sukayi suka nufi gidan koda suka karaso sai suka ga Dan karamin padlock a jikin kofar katakon.

Tace’ kinga Ummusalma basa nan yanzu yaza’ayi? Kode muje mukwabtansu muji?
Kai daga bata,suka nufi gidan kusa dasu, sallama dayar tayi aka amsa masu suka shiga,wata Mata suka gani da yara hudu kanana suna cin Abinci,matar da yar fara’arta ta amsa tana tashi
Tace’ku shigo kwa tsaya daga nan?
Shiga sukayi amma Basu zauna ba,
Matar
Dayar ce ta gaida ta suka gaisa Ummusalma kuwa kawai kallo take binsu dashi musamman ma yaran,
Daga ina?matar tace

Ni suna na Aisha wannan kuma Ummusalma mu yan makarantar su Amina ne munga jiya da yau batazo ba shine muka zo muji ko lafiya kuma kinga munzo gidan a rufe?
Tunda tafara matar take kallan ta da tace Ummusalma kuwa Ummusalman take kallo ta don tanajin labarinta sosai da sosai a wurin Amina,
Ajiyar zuciya ta sauke badan ta Amina ta gargadeta kada ta fada Mata ba da ta fada Mata komai,Amma kuma tayi alkawari bazata fada Mata ba,
Cikin yake da kauda damuwa matar

tace’ ai sun tashi jiya jiya suka tashi wallahi kuma ma garin suka Bari kunji ko,
Aisha ce tace to shikenan mun gode sosai juyawa suka zasu tafi da sauri matar

tace’ Ummusalma tsaya tabada sako a baki,
Da sauri ta shige dakinta ta dauko Dan box mai kyau ta Mika Mata tace’ tace a abaki wannan dawowa tayi ta karba batare da tayi magana ba ta mikawa yaran ledar hannunta na chocolate din da tashigo dashi, suka fita.
A mota Aisha ce sai masifa take wai sunje gidan mutane batayi magana ba kuma bata gaida matar ba,da ita ce matar ma wallahi bazata bada sakon ba,ita kadai tayi ta masifar ta takalli driver tace’ tace ring road zaka kaini sannan tayi shiru.
Kallanta kawai Ummusalma duk abinda ta fada nakin magana da gaida mutane gaskiya ta fada saidai bata iya ba,batasan ma tana zata fara ba tace wai ina wuni ba’a koya Mata ba gaida babba saidai a gaidata,ba,a koya Mata komai ba na tarbiya tabbas ita an koya Mata kuma tana aiki dashi tunda har zata iya tsayawa drivern gidan su yazo tace ya fada ga inda ta tsaya tasan an koya mata
Tana tunani batasan sunzo gidan su Aisha ba har ta fita sai ji tayi Aishan na

cewa’ godiyar ma Baki iya ba baza kiyi ba,kin bata min lokaci na rakaki Amma ba godiya kekam kinji dadin rayuwar ki wallahi mtsww
Taja tsaki ta rufe kofar ta wuce,
Runtse ido tayi sabida yarda taji bugun kofar har zuciyarta. Tabbas
Bata taba yiwa wani godiya ba,wama zata yiwa godiya bata taba neman alfarma ba a rayuwar ta har da zatayi godiya.yau ta dau karu da Abu biyu gaisuwa da kuma godiya idan an taimake ka.Ahaka suka karaso gidan tana sana’arta.
Yau Friday tasan mutenan gidan basa nan sun tafi gidan kawayen Mama,
Haka ta shige dakinta,wanka ta shiga,koda ta fito bata kalli mirror ba ta wuce tasa kaya ta dawo ta zauna ta jawo jakar ta dauko Dan box din da Amina ta bata, box din ta fara shafawa a hankali bata ankaraba taji hawaye ba ta goge ba,bude din box tayi, zobe ne na silver sai bracelet, da zanen heart a jikin su sai wata yar karamar paper aciki yayi kyau sosai,tana kuka sosai, ta dauko bracelet din tasa a hannunta kamar an gwada cib daidai hannunta,sa zoben tayi sai dai Mata yawa.
Dauko papern tayi ta warware
_TO A YOUNG GIRL WHO WILL GROW TO BE A BEAUTIFUL WOMAN…. JUST REMEMBER BEAUTY IS INSIDE AND OUT, I WISH, ONE DAY U WILL BE ALWAYS SMILING.
HAPPY BIRTHDAY TO YOU……
wani iri kuka ne ya kwace mata tana rike da paper ta karanta ba adadi tanayi tana kuka,tarasa kukan me take,kukan rabuwa da Neena ne ko kuma kukan tunawa da tayi a irin wannan Rana ne komai nata ya canja,kuka take sosai mai cike da tausayi,tana har bacci ta dauke rike da papern ta dunkule ta a hannunta…..

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
????A BAKIN WAWA????
Akanji magana

  4

Bata farka ba sai 4,da sauri ta tashi tunawa batayi sallah ba,ta shige toilet a gaban sink ta tsaya fuskar ta ta kalla taga yarda tayi wani iri da ita idanta ya kumbura sabida kuka, papern dake hannunta ta kalla ta warwareta ta kuma karantawa taji hawaye ya kuma zubo mata kallan kanta ta kumayi a jikin mirror

Tace’ a duk sanda nake tare dake inajin wani farin ciki da nishadi marar misultuwa,Amma yanzu nasan bazan kuma samun wannan farin cikin ba,kin kuma sani acikin rudani,meyasa zaki min haka ?dole kina da dalilin ki na boye min koke wacece amma meyasa? Duk Daren dadewa Zaki dawo.
Takarashe tana goge hawayen dake zubo mata, adana papern tayi gudun kar ta jike,zoben ta cire shima ta adana Shi a cikin cupboard, alwala tayi ta dauko papern har ta fito kuma ta koma ta hada papern da zoben ta tafito. Azahar tayi,tayi la’asar tagama azkhar sannan ta fito,bakowa a gidan kamar yarda tayi tsammani, kitchen ta wuce ta tsaya tana tunanin me zata ci, fridge ta bude dauko abarba ta yankata kanana,ta dauko madarar ruwa ta zuba tasa sugar,ta dau teaspoon ta fita garden,kujera tasamu ta zauna tana sha tana tunani,acikin zuciyarta tafara saka abubuwa,daga bisani

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button