A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’ Dan uwan bracelet di nane, kana so?

Sai yanzu ya kalli hannunsa zoben ya kalla ya kalli bracelet din dake hannunta dake rike da nasa, banbanci kawai nata ya jima a hannun ta nashi kuma sabone amma hakan ba yana nufin idan kagan su zaka ce ba iri daya bane iri dayane komai da komai,

tace’ kyauta ce zuwa gareka amma idan kana so,
Shiru yayi hakan yasata cewa’ ohh baka so Kenan?
Namma shiru yayi,

tace’ okay nagane,
Dayan hannunta tasa tafara kokarin cirewa damke hannunta yayi cikin nasa,

yace’ kyautar rowa ko?

Ai naga naka so,

Ni na fada maki?

Gashi kuwa ina ta magana kayi shiru,

Shirun ya karayi yana kallanta,wato shi duk maganar da yake mata tana daga masa kai fa, sai ita ce taza Sami magana, murmushi a zuciya yayi,kallansa tayi kawai ta fara kokarin tashi sai dai hannunta dake cikinnasa yasa ta tsayawa janyota yayi,

yace’ ina zaki je ki bar mij…ohhh abokinki anan,

Shiru tayi ba amsa
yace’ to dawo ki zauna,dawowa tayi ta zauna taki kallansa,
to naji nagode da kyauta sosai, amma waya baki ?

Kauda kai tayi tace’ Neena,badan Yana kallan bakinta ba sai yace batayi magana ba,dukda yasan me tace amma

yace’ What? Nuzaif?
Harda su waro Ido, kallan sa tayi da dan karfi,

tace’ Neena,Neena nace,

Ohh sai naji kamar kince Nuzaif,

Da Nuzaif sunane?

Ahh nasani? Duniya fa da fadi,

Daga nan suka cigaba da hiransu dukda rabin hiran shiyakeyi amma tana bashi amsa sosai,shike lilasu har magriba sannan suka tashi don gabatar da sallah.

✨✨✨✨✨

Bayan sati daya sosai abubuwa suka canja cikin kuwa harda wata irin shakuwa tsakanin Binaif da Ummusalma sosai suka shaku, idan tana zuba zance ma zaka ce Big girl din da ce da kasani, sai dai tsantsan irin zaman da sukeyi ne, bata so yana magana tana masa shiru bata san bacin ransa batasan dalilin hakan ba, kamar yanda shima baya san bacin ranta shiyasa kowa yake kaffa kaffa kar ya batawa juna rai, ta bangaren Anty safiya kuwa shirye shirye take sosai, yaje ya kai kudin lefenta da komai, Anty safiya ta dire tace gida ma shi zaiyi to Allah ya taimake Shi yana da gidan sa tun Yana aiki ya saya daya a Abuja daya kuma a Kano,Daddy ne ya yace zai mata furnitures.
A bangaren su yusseer sun kwantar da hankalin su sun aan ba fita ba zasuyi sai dai tunanin da sukeyi ne yasa suka rame suka yi wani irin farin rama dukda suna ci suna sha kuwa,
Binaif ya fara zuwa company Yana aiki batare da ta sani ba, duk wani Abu da za’ayi anyi an kara modernizing abun da suke sarrafawa sunayin madara da kuma sugar, da yake company din hade yake da gonar shanu harda shi ya hada ya saya, Sannan ya kara da sarrafa sugar da ya fara, sosai abubuwa suka masa yawa,ga gyaran gida da ya taso masa don ma Daddy ya bashi gudunwa haka ma Baba Usman shima ya bashi,to da su ya hada yake yin aikin gida da kuma aikin company,sunan companyn ma ya canza ya dawo UMMU LTD.

Yau ya dawo a gajiye so kawai yake yaji shi a kan cinyarta ta,har wani Allah Allah yake yazo gida ya ganta, yana zuwa kuwa ko jakar Shi bai dauka ba ya shiga parlour, Umma yagani,

yace’ Hajiya Umma sannu da hutawa,

Umma tace’ a,ah dan nema Kaine Ka dawo? Ya aikin?

Lafiya,yace Yana wucewa ciki,Yana Shiga yaga bata nan duk a zatansa wannan lokacin yawanci idan ya dawo tana kwance ko tana bacci ko kuma tana danna waya, amma ganin bata nan yasa Shi zuwa kofar toilet nanma bata nan sai yayi tunanin kila tana kitchen, toilet ya Shiga yayi wanka ya kwanta har bacci ya dauke shi baisani ba,dayake yamma ne be tashi ba sai magriba a gurguje yayi alwala ya tafi masallaci koda ya dawo ya tarar da Umma da mai aikinta suna kallo suna cin abinci Zama yayi,

yace’ Umma wai ina take ne,

Umma tace’ wa Kenan?

Mata ta,da wa zan tambaya kuwa?

Umma tace’ afto danaga ba ajiyar ta kake bani ba idan zaka tafi shiyasa ai, amma dazu kamar naga ta fita I…….

Ta fita, ya katseta,
Yacigaba to ina taje? Da zata fita? Sata nayi kome? Kuma kina kallanta ko?

Umma tace’ ehh wallahi kuma baza ta dawo ba sai nan da sati uku shiyasa ma ta tafi,

Umma banfa gane ba,

Ai bazaka gane ba ina magana Ka katsene sai Ka samu wanda zai karasa maka ai,

Saukowa yayi yace’ ummi don Allah kiyi hakuri ina taje?

Uwarka ta zo ta dauke ta tafi da ita bani da ikon hanawa tunda uwarka ce,

Yace’ bangane ba kina nufin Anty safiya ta tafi da ita?

Zancen kake so yaro, ta fada tana kai lomar tuwo bakinta, bata Kara kulashi ba,shima tashi yayi ya Shiga daki,dukda a azababbiyar yunwar da yake ji haka ya hakura baici ba,juyi kawai yake yi akan gado, Yana tuna idan yazo kwanciya ko ya zaiyi? Wayarza yaji tana ringing dauka yayi batare da ya kalli sunan ba,jin mus’ab na cewa”‘ bb kazo ka dauke mu,tun dazo muke jiranka amma shiru,kama manta da mu gashi kuma kasan wurin uban nisan masifa babu mai adaidaita kazo please,

Tsaki yayi ya kashe wayar ya tashj ya dauki key ya fita,a mota kuwa ya jera tsaki yafi dubu kafin yaje airport fita yayi yana hangosu ya nufa wurinsu suna ganinsa suka rungume shi, shima rungume su yayi amma bayi magana ba sune sukayi ta haukar su don yau hauka zaice masu basu birgeshi ba dukda kowa yayi missing dinsu,sakin shi sukayi suka nufa wurin mota, Mas’ud

yace’ wai bb me yake faruwa ne?
Naga kayi shiru ko wani abu muka maka ne?

Girgiza masu kai kawai yayi yana shiga mota suma shiga sukayi yafara ja, suna tafiya Mus’ab yace’ to ko wani abu Hajiya tama,
Nanma dai girgiza masu kai yayi daga nan shiru sukayi basu kara magana ba, suka ci gaba da tafiya har suka iso. Suna shiga sukayi kan Umma gaba dayan su rungume ta sukayi suka sa ta a tsakiya,

tace’ ‘yan albarka sun dawo,sannunku sannu,ya hanya

Mas’ud yace’ lafiya qalau Umma,ya kafarn naki,

Kayya dan nan kafa ai daman ta tafi tsufa ne fa da kuka samu ma ban tsofeba ina dad dan jika Wanda ya kusa candy ai dole kuga haka daman,

Daga nan kuma hira ta barke tsakanin su,Shi daman binaif be shigo ba masallaci ya wuce, sai tara ya dawo Koda ya dawo suna nan suna hiran su,sai dai sun canja Kaya Kenan har sunyi wanka sunyi sallah bai kulasu ba ya wuce daki,

Mas’ud yace’ wai Umma me aka yiwa bb ne?

Ummu ta tabe Baki tace’ matar Shi aka dauke shine yake cika yake batsewa ko magana ma yaki yayi,

Mus’ab yace’ yaushe akayi auren bamu sani ba?

Tace’ ai da yake auren kawai aka daura bakowa ya sani ba sai Nanda sati uku za’ayi tariya ai, Nima gobe zanje kauye a can ma za’ayi bikin ai al’adar can za’ayi Wanda zaije yaje Wanda baze jeba ya zauna huta roro,

Mus’ab yace’ habade hajjaju kema kinsan zuwa dole ne ai, daga can ma kika Sani ko mu San kamo maki sirika?

Kai amma wallahi da nafi kowa Jin dadi,daman ita wannan daga ita har mijin nata, yarda kuka san mezan ce haka suke basa dariya Kai ko ita ko magana batayi,amma Naga yanzu tana Dan murmushi shima iya kan lebe ne, wani lokacin kuma zaka ga wani abu ya Loma idan tayi Kenan tayi dayawa, ahakan, amma ni naga hakori da sunan dariya bade ZAINABU ABU mai tagwayen suna ba,

Dariya sukasa mas’ud yace’ Kenan itama matar haka take?

Mus’ab yace’ taab zanso nake zuwa gidan nan ko zanci dariya ita dikim shima dikim,

Umma tace’ su haifo yara dikim Kim,
Suna cigaba da dariya abunsu suna hira, duk Yana jiyo su haushi su ma yake ji Suma din, da aka Basu dalilin kinyin maganar sa Amma suke masa dariya, tsaki yaja ya dau waya wai zai Kira amma beda numbern ta ai, tsaki yaja ya garar da wayar Akan gado, daga nan kuma yadena jiyo maganar su kenan ma suna sane sukayi da karfi,kwafa yayi ya kuma juya kwanciyar sa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page