A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Daddy kuwa da Umma mamaki sukayi Jin tana magana haka,Basu Kara tsinkewa da lamarin sai da ta daure su da jijiyoyin jikin su bata barsu haka back takuma nade su kawunnasu da wani zance, suna bukatar Jin labarinta, meye hadinta da su Mus’ab mene alakarta da su, sannan kuma waye wannan Wanda ya nemi wargaza farincikin da kima ta ‘ya mace??
Ganin duk sunyi shiru suna nazartar tambayoyinsu yasa

Binaif yace Bari na baku labari a takaice, daga nan ya Basu labrin komai in brief, yace’ ko Nima tabbas ko shakka banayi Brothers Yan uwanta tunda a yarda suka ce an wulgar da jariri,kunga Kenan Basu mutu ba, sannan kuma Brothers suna 6 years aka sa a kashe su Kenan ba’a kashe su ba,tunda ta masu tasa sun manta da komai Wanda aka sa ya kashe gari ya canza masu,kunga daga nan Daddy ya dauko su,inaga wannan shine daidai kuma ko shakku banayi hakanne ya faru.

Sai dai bai fada masu abinda suke shiryawa ko kuma Shi yake shiryawa don ita bata ma San sun Kai kudin ba,

Umma shiru kawai tayi tana jujjya al’amari Nan da kuma ikon Allah, Ashe har yanzu akwai mutane marasa tsoron Allah,itaka shiru tayi tama kasa magana don ta Rasa ta cewa kawai tagumi ta rafka, tana tunani ita da ta kusa shekawa Ashe zata ga abubuwa kafin ta karasa ga mahaliccinta, Kai duniya ina zaki damune.

Shima Kansa Daddy kasa magana yayi don shima ko shakka bayayi tabbas yar uwar su ce tun kallon farko da Yayi Mata ya gane hakan sai dai kuma Allah ba abin wasa bane kana naka Yana nasa,Shi bekawo komai ba a ganinsa kawai kamace.
Babu Wanda ya Kara magana sai ajiyar zuciya da take tashi, daga bisani Daddy yayi masu nasiha mai ratsa zuciyar duk wani Wanda yake sauraro tuni taji zuciyar tayi fes sai ma wani nishadi da takeji sai dai dan abinda ba’a Rasa ba.
????????????????????

Tana kwance kamar kullum rungume da hotonsu a hannun ta a halin yanzu babu abinda take sai tunanin ko suna da rai ko sun mutu? Wannan shine tambayarta Amma kuma babu mai Mata amsa sai dai ace tayi hakuri,yau da taje gidan su ma gani tayi Mama na cin abinci kamar ma abinda ya faru da ita, takaici ne yasa ko magana batayi ba ta dawo ta kwanta, sai dai yanzu ta dena kuka, ita da abinci kuwa sai kallo,sai kuma idan Uncle ne ya matsa mata to shine zataci shima bawani ci dayawa ba, bata koma sai tunani wanka ma sai Mama tacr taje tayi shima kuma bata jimawa take fitowa, wayar ta taji tagi fara ringing tana dubawa taga sunan fati, da kamar bazata daga ba sai kuma ta daga, ji tayi tace Mata suna da test Bama taji karshen zancen ba ta kashe waya,itafa ta gaji da wannan makarantar ace watan su daya da zuwa har za’a fara yi musu wani test,haka Suma zuwa aka fara Basu assignment wani ma ranar da ya Shiga ranar yabada assignment ina dalili, damuwar kanta ma kadai ta isheta itakam bare kuma tasamu tayi karatu, tsaki ta ja itadai sannan ta ajje hoton ta Shiga toilet bata jimaba ta fito daure da towel mai kawai tashafa tasaka doguwar rigar atamfa, sannan ta kawo Katon hijabinta har kasa tasa, ta zira palate takalimi tadauki jakarta ta fita, idanta kawai zaka kalla kagane ta rame kuma tana cikin damuwa, parlourn ta fito taga Babanta, da Mama suna cin abinci gaida su kawai tayi,ta wuce gaisuwar ma ba irin yarda ta Saba tayi ba, ko fada masu inda zataje batayi ba, tana fita tayi wurin driver tace’ ya kaita school.

Anty ta kalli Baban Ummu tace’ Abu Abdallah ina tausayi yarinyar bakadan ba, kaga fa yarda ta koma zaman daki, da ita idan ta fito ita da daki sai kwanciya kullum tana parlour idan karatu ne to tana waje,amma yanzu gaba dayanta ta kulle kanta a daki,

Shima numfasawa yayi yace’ Nima na lura da hakan,sai dai bansan yarda zanyi ba,duk wata hanya da zanyi,nayi na bi Amma shiru nikuma bawani mutunci muke da iyayen yaran ba, bare su fada min halinda ake ciki don nasan yanzu de duk yarda akayi an sanar dasu me ake ciki,

Anty tace’ fatana Allah yasa de lafiya suke, dakuma ace anga gawar su da abinda sauki ma,ansan sun mutu.
Bekara magana ba,itama ganin haka yasata yin shiru suka cigaba da cin abinci su.

Ummu kuwa a Mota shiru kawai tayi tana tuna ranar Monday dazasu je makaranta dramar da sukayi tayi Akan su koya Mata mota, har suka iso bata San sun iso ba sai dataji Yana tambayan ta ina zasuyi, Ashe fa driver be taba kawo ta ba,hanya ta nuna masa har suka isa, lecture theatre din ca tace ya jirata gata nan fitowa.
Tafiya take amma gabadaya batajin dadi sabon kewansu take ji,ji tayi hawaye na zuba a idanta hannu tasa ta share sannan tacigaba tafiya,kowa kallanta yake Wanda suka san ansace su su tausaya Mata wasu sukuma da Basu saniba suce ko ina yan uwanta oho,
Koda ta shiga bata zauna inda suka saba Zama ba sai ta tafi can Baya taje ta zauna abinta babu Wanda tayiwa magana, handout ta Ciro tafara karantawa dukda a takure take Amma ahaka tade ta daure take karatu, ta jimaba a wurin sannan lecturer yazo shi. Allah ya taimaketa Dan abinda ta karanta ya wasu sun fito wasu kuma tayi da kanta ta hada, Gashi awa dayane kuma ba laifi tana da saurin note kuma uku za’a amsa sai dai kuma gabadayan su suna da ‘ya’ya. Itace zata fara forwarding gaba haka yasa tayi ta fito bata jira sai kowa ya Gama bayarwa ba.

✨✨✨✨✨✨

Bayan sunyi sallahn Isha, mai aikin Umma wacce take Kula da ita ta kawo masu abinci, suna zaune suna kallo Umma

tace’ sai yanzu kikaga dama wato ko? Tun dazu inajin yunwa sai yanzu ne zaki kawo mana abinci ko?
Ita dai mai aiki shiru tayi don tasan tayi lefi,ganin Umma ta fita yasa itama ta fita kuma batayi abinci ba sai da ta dawo bayan magariba.
Itama Umman shiru tayi batace komai ba,ta fara cin abinci,

tace’ salamatu ki matso muci tare kinji ko?
Matsowa tayi zataji Binaif da yake Ka kujera ya diro,

yace’ a,a kamar ya ku matso kuci tare? Mutum da matar Shi ai tare zaiji da ita ko? Ni ko tayin ma ba a min ba wannan ai ba adalci bane.

Ko kallanshi batayi ta lura shima wannan beda ta ido zata kuwa nuna masa itama bata da ta idon,ita kuwa Ummusalma kunya ma taji daga yin auren,ko kamar ko a jikinsa yarda ma ta gani kamar son auren yake, ita kunyar shima takeji shiyasa ko kallansa bata Kara yiba,
Ganin sun fara cin abinci su hankali kwance yasa Shi Kara matsowa shima ya dauki spoon ya fara ci, ita gaba daya takura tayi tama kasa sakewa don haka kadan taci dukda yunwar da takeji kuwa sai kunun ayar da tasha,
Umma ce tafara Mita,

tace’ arasa me za’a min sai abincin yara,yanzu wannan abinci ne iye?

Binaif yace’ Taliya ce abincin yaran?

Yo itace mana kawai a kafa barina da yunwa?
Tace ni na koshi ma, tafada tana cire hannunta daman da hannu take ci sune suke ci da spoon.
Babu Wanda ya Kara magana har ya Gama shima ya tashi ya tafi gida,kwashe kayan tayi itama takai kitchen inda taga mai aikin ta fito.
Umma tace’ kije ki kwanta,kuma kinga ya tafi ai da ya kawo maki kayanki,Kai wannan Mantuwa, kinga kirashi a waya ta kinji ko?
Mika Mata wayar tayi ta karba,

tace’ mene sunan?
Ni nasan me aka samin, zade kiga kan mutun guda biyu da mota bata sha wahalar ganin sa ba kuwa, dannawa tayi ta Mika Mata, sai da takusa katsewa yadaga tace’ Ka taho Mata da kayanta da motar Adamu, baji mezai ce ba ta kashe,

tace’ kinga ni na fara Jin bacci,kama ni na tashi na tafi daki,idan yazo ki Shiga dakin kusa Dani wannan ki kwanta wancan dakin ta nuna wani daki dake gefe nasu Yan albarka ne( mas’ud da mus’ab) sunma wai kusa dawowa haka suka ce de.
Tashi tayi ta kamata ta,har daki ta rakata sannan ta dawo ta zauna tana channel ta canza ta Kai Bollywood suna Dhoom 2 suke dukda taga film din Amma tana San Kara gani,hakan San ta Mike kafa Akan kujera tana cigaba da kallo. Har suka gama bashi ba alamar suka fara series tana nan zaune ba lefi series din ya Mata kyau,shima suka gama suka fara wani,tayi bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page