A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Tace’ shikenan bakomai yi hakuri zo muje na tayaka gyara dakin naka, idan yaso sai ko gobe ne sai na Shirya ma kayan Ka a drawer yi hakuri muje,
Tafiya sukayi, mas’ud ya daga murya yarda zasuji yace’ ehh din daki ne bazan hada da karamin yaro ba, ko budurwa be taba yiwa magana ba, a to ade ji dakyau,
Binaif har zaiyi magana sai kuma yaja bakinsa yayi shiru, sukuwa da suka shiga, tace’ muje dakin,
daki suka Shiga,
Tace’ kasan yaza’ayi? Kayan Shi za’a kwashe a mayar dakin naka, Kai kuma a shirya ma kayana Ka anan, idan yaso yayi aikin Shi, Shi daya,
Aikuwa haka akayi suka kwashe masa kayansa tas suka mayar dakin dake opposite da Shi, suka Shirya kayan Mus’ab komai tsab, ta kofar baya tabi ta kwaso freshener ta fesa masa a dakin, ta taya Shi gyaran parlourn ma tsab suka fesa komai, suka saki labulen suka fesa Freshener ko ina, sannan yaje yayi wanka ita kuma ta fito,
Kusa da Binaif ya zauna tace’ Ina wayana?
Banza yayi da ita tace’ bb wai ina wayana ina maka magana fah,
Dagowa yayi ya kalle ta, yace’ ai Naga Baki banbance ba, kuma mu biyu ne ana din,
Mas’ud yace’ taab karka yarda wai bb da kana da abokai ai kunya zaka ji, ina laifin tace’ maka Sweetie, sweetheart,sweetlove, sweets sugar, sweet sweet dinnan nake fada maka sunfi sweet, a kauyence ma tace maka dear Amma wani bb ai bata da maraba da kanwarka,
Kumewa tayi tana aiko masa wani irin harara sarai yasan hakan zata yi shiyasa ma yaki kallanta Kar ya kasa karasa abinda zai karasa,
Binaif yace’ hmmm rabu da ita,ko mi amor din nan bata ce min sai dazu da ta fada,
Mus’ab ne ya karaso ya mikawa Mas’ud waya yace’ ana ta kiranka, kabar waya a daki,
Yace’ to ina ruwanka da wayata,bafa nasan kananun Yara suna taba min waya, taam, bani ni, daman de wayar biyu mutum take da ita,
Ansa yayi Jin an sake Kira,kwalalo Ido yayi yacet Sameera ce, dagawa yayi,
Mus’ab ya wayarce yasa a speaker ya kuma rike gam a hannun sa ya Sami wurin ya zauna, daga can Sameera cikin muryan da ya Mata lakabi data munufukai,
tace’ hellooo! Bakaji ne?
Galla masa harara yayi yace’ am am inaji, nace ya kike?
Tace’ lafiya qalau, yau lafiya kuwa najika shiru?
Yace’ eh lafiya Nayi tafiya ne,
Ayyyaahhh ya hanya,
Ahh lafiya qalau,
Sai kuma yayi shiru, Ummusalma mezatayi ba dariya ba, haka ma mus’ab Shi kansa Binaif murmushi yake, yarda yake maganar kamar ana janyota shikadai ke basu dariya,
Tace’ kayi shiru,
Kema shirun kikayi ai,
Tace’ Amma na fada maka Abbana beda lafiya ko? Amma ko Ka tambaya ko?
Yace’ ayyyaahhhh sorry kinga mantawa nayi,Nima da nazo na tarar da sister na ba lafiya shiyasa, kiyi hakuri ko?
Tace’ Subhanallah meke damunta?
Zazzabi da ciwon kai ke komai ma,
Tace’ ayyyaahhhh Allah ya sauwake, Ka gaida ta to,
Nace Mata wa Kenan?
Ikon Allah, who am I to you?
Zare Ido ya fara Yana kallan su, yarda suke kunshe dariyar su, Ummusalma ce ta saisaita Kanata tace friend irin sautin be fito ba, Amma ya gane,
Yace’ friend,
Iya haka kawai?
Ehh mana,
To haka zakace Mata friend Dina na maki sannu kuma tana gaida ki,tunda rowar numbern ta kake min,
Shiru yayi Yana mazewa irin I did dinan, ganin yayi shiru
mus’ab yace’ ba rowa nake maki ba, yama za’ayi na maki rowa ? Ai kin wuce wurin,
Tace’ dan Allah?
Yace’ wallahi kuwa,
Yace’ me kika tana dar min?
Kamar me fah?
Komai ma, kamar hira haka,labari Mai dadi, kafin nazo zuwa zanyi fah,
Tace’ Anya kuwa zaka same ni a gida? Zani party fah,
Yace’ party ? Wanne irin party ne haka? Kinga magriba ta kusa fah,nikuma kafin Isha Zan zo kina so kice min at that time Baki gida?
Tace’ kusan hakan,
Yace’ bangane ba?
Tace’ eh za’ayi party ne a central hotel,
Yace’ biki?
Tace’ a,a shagali kawai,
Kallan Ummusalma yayi irin mezan ce,fada masa tayi, sannan ta dauki wayar Binaif tayi typing tura masa,
Tace’ kayi shiru,
Yace’ narasa abin fada ne, Imagine yanzu ace bazan iya yin gaba ba da relationship dimmu to next level ba ba? Shikenan bazan cika gaba da yin Aboya da me yawo ba,
Tace’ kamar ya?
.kamar yarda kika ji, shikenan bakomai daman an fada min ai ba haliku Daya da Ummusalma ba, shikenan sai anjima Kar ki Kara kirana kuma,
Ya kashe wayar, tare da sauke wata karuwar ajiyar zuciya,
yace’ ohhhh wallahi nafi ooo de,
Mas’ud yace’ me kukayi hakan?
Ummusalma tace’ hakan shine daidai abinda mukayi, na lura ta Baka wani matsayi a zuciyar ta,kaga kuwa dole sai anyi amfani da wannan damamr an hanata yawo nan Bana San Shi Sam,
Yace’ to hakan yayi, Amma ya akayi bata gane muryna ba?
Ai muryan iri dayace,idan Baka sani ba, amma ni ina ganewa,
Yace’ kekam ai Shiga uku Baki da maraba da alajanu fah,
Zatayi magana su yaseer suka shigo shida yusuf da Ummu ,gaida Binaif sukayi suka gaida su Mas’ud,
Ummu tace’ yaya yunwa nakeji daga makaranta muke,
Yaseer jita mu kuma ai bamaji ko? Salan idan an tashi zubowa a zuba maki kedaya ko?
Yusuf yace’ sankan fa?
Mas’ud yace’ Ku Baku da Baki? Ita ai tayi magana, kuma sai kuyi ai,
Ummu tace’ yawwa yayanah fada musu de,
Wani dadi yaji yau ance masa yaya har wani Kara Fadi yayi da Kara Zama, girgiza Kai Ummusalma tayi ta tashi ta Shiga ciki shima Binaif binta yayi yace’ ciwon kai zaku hada min gwara Nayi nan,
Mas’ud yace’ wai fav Amma tare da Kai zamuje ko? Kaga ni bazan iya hirar arziki ba,
Mus’ab yace’ dazu me Ka Gama fada min, baca kace zaka iya proposing kowacce yarinya ce bace?
Yace’ share dazu ai kawai kade gane
Yaseer yace’ wai tsaya karde ace kunsa zuwa wurin yarinya ne,?
Yusuf yace’ ai daga ji kasan hakanne, ni da akwai wata yarinya ma da bazan iya juya ta ba kawai Bana San Shiga sabagar Yara ne kasan Mata akwai reni,
Yaseer yace’ ai ba bakai ba koni wallahi albarka,
Mas’ud yace’ inajinka kasan ni matsalar badaga nan take ba,Amma de fada min yanzu yaza’ayi,
Yusuf yace’ Abu Mai sauki kasan matan ma kalakal ne, amma duk wata mace tana San caring to daga nan zaka fara,harda fah romantic talk kade gane,
Yusuf?? Ummusalma da Binaif ne da suka dauko abinci suka tsaya suna kallan sa, a tare kuma suka Fadi sunan sa,
Juyowa ya kalle su,ya fara Sosa keya, Binaif yace’ dole Ka fada sosai keya ai da yake kunyar anan take, ya karasa ya ajje kayan hannu Shi, ita ya karasa ta ajje nata,
tace’ Yaya salama ko? Nifa da kika ganni nan bazanyi budurwa ba, kuma ko aure bazanyi ba,
Ohh ni Salamatu ta abakin Umma, yanzu Kaine haka?
Yaseer yace’ ai Yaya ko? Kadan kikagani indai shine,
Ummu tace’ laaaa taab ai kaima gwani ne, suna fah da budurwa su dukansu, hmmm ai kubi ni a hankali,
Yusuf yace’ bana san munafinci taam,
Ummusalma tace’ to idan tayi sai Ka dakata,
Mas’ud yace’ a,a fah ya isa haka nan,
Mus’ab yace’ ai da’alama kusan halin Ku Daya,
Binaif yace’ ya isa haka nan,yanzu de ga abinci nan kuma kunji an Kira sallah Ku tashi kuje muyi sallah sai a dawo azo aci,
Mas’ud yace’ ance ci Yana gaba da sallah,
Galla masa harara Binaif yayi yace’ ai bakace zaka ciba, Ka tashi ko kuwa,
Tashi sukayi su duka a wurin sukayi alwala sannan suka wuce, Ummusalma
tace’ ummu kije kiyi sallah, aciki ,
Dan murmushi tayi sannan ta tashi, tashiga ciki, itama binta tayi,
Daki suka shiga ummu tace’ bafa abinda zanyi kawai de, sai kuma tayi shiru,
Murmushi tayi tace’ nagane,zauna to muyi magana,
Kujera sukaje suka zauna, Ummusalma
tace’ ki dauke ni tamkar Yusuf da yaseer nasan su bakyajin kunyar su, Nima Bana san kike Jin kunya ta kinji?
Ina so nazama yayarki hope za’a Bani wannan chance din,