A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

tace’ ohh sannu da kokari,muna ta bacci har kin tashi kin gyara ko ‘ina bamu saniba,na gode sosai,
Batayi magana ba don batasan mezatace ba shiyasa kawai tayi shiru abinta,itama maman Sadiq din wucewa tayi ta Shiga kitchen ta cigaba da abinda takeyi.
Breakfast ta kawo masu su Duka bata ware ba,a plate daya sai cups, dumamen tuwo ne sai bread da kwai sai tea,maman Sadiq

tace’ bansani ba ko kina cin dumamen tuwo,
Ita mamaki ma taji,tana San tuwo ai ita,ca

tace’ bakomai ina cin tuwo ai,kuma ma rabona dashi tun kafin na tafi makaranta,
Daga nan ba Wanda yasake magana suna ci suna kallo,abinsu tare da yaran,sosai abin ya burgeta tana so taga family a haka bakamar gidan da ta taso ba kowa nashi yake zubawa kuma a dining suke ci.
Suna gamawa kuwa ta dauki plate din ta Kai kitchen tare da cups din,tana Shirin wankewa saiga maman nan tazo

tace’ kingan ki ko? Duk uban aikin da kika sha,bai isheki ba sai kin wanke wanna ko?
Ta karasa tana karban sponge din daga hannunta, bata tayi amma bata fita ba tsayawa tayi tana wankewa tana daurayewa,suka Gama Suka fito,yaran ta kalla

tace’ kuje ku dau ruwa kafin a dauke yau mun makara,
Tashi sukayi suna cuno Baki da’alama basa son tashi daga kallan,bayan sun tafi Ummusalma ta kalli maman Sadiq

tace’ ina San na nemi aiki a wani gida, ya zanyi?
Kallanta tayi kallan kina da wayo kuwa?

tace’ bangane ba?

I mean aikin gida kamar Shara wanke wanke haka da sauran su,

To ke me zakiyi haka da irin wannan aikin?

Wani aiki nake so na gudanar kuma dole sai tanan ne nake ganin zaiyi,

To shikenan ba damuwa Zan tambaya maki anan makociyar mu itama tana kaiwa masu aiki, kuma naji tana cigiyar idan ansamu.

Hamdala tayi tayi a zuciyar ta fatanta Allah yasa a dace,

Kallanta tayi tace’ Amma ba’a haka zaki tafi ba? Kinga gidan aiki ne dole zani zaki kesawa kuma dabam dabam,sannan kar ki nuna ke yar boko ce,idan ba haka ba za’a samu mutsala,

Kallanta tayi tace’ ya kike ganin idan naje masu a marar magana? Zasu karbeni?

Good idea,hakan yayi ma,du abinda ake ciki sai ki fada min idan kinje.
Bari ma na kirata sai tazo muyi maganar zuwa yamma sai a kaiki,
Daga Kai tayi kawai daganan ta tashi ta dauko hand bag dinta tayi rolling ta fito, sallama ta mata ta fito,tana fitowa tana hano mai adaidaita Yana shigowa layin,ita Sam Tama manta dawani mai adaidaita,tsayawa tayi kuwa taga shine ko bashi bane,aikuwa shine,tana Shiga tace’ ya kaita banki access bank,kaita yayi ta fito tace ya jirata, atm ta sake don yayi expired,kuma tana bukatar kudin, sannan ta canza dollars dinta Amma ba Duka ba, sannan ta fito gobe zata dawo ta amsa atm din,Shiga tayi suka tafi daga nan ta sai simcard ta saka a wayanta,sai bata cire dayan ba ganin kamar Yana amfanin dukda bawanda ya kirata, Amma taga akwai network..

????????????????????

Suna sauka ta nufi gate zata fita har wani sauri sauri takeyi don ta fice,sai dai kafin taje taji an damko hannunta,ya tsine fuska tayi don tasan waye,juyowa tayi

tace’ haba uncle gidan su besties zani fah,
Wani irin kallo ya Mata me cike da gargadi sannan

Yace’ inba de dusa ce taya zaki fita gidan mutane da wannan dare? Daga dawowa ko sallah bakiya ba?

Kara marairaice wa tayi,wai ko zaiji tausayinta yace taje,

Tace’ kaga ko minti daya bazanyi ba zandawo kaji ko?naje?
Maimakon taji amsar sai ji tayi an fara janta,wani takaici ne ya kamata,ta kumbura baki ta fara gunguni ciki ciki, don tasan idan yajita to Saidai wata Ummu badai ita ba, Yana rike da hannunta har suka isa cikin parlourn,suna Shiga kuwa mamanta na parlour da’alama su take jira, da sallama ya shigo,cike da fara’a ta tashi ta tarbe shi

tace’ ya hanya,?
Lafiya qalau ya amsa Mata,
Kallan ummu tayi Wanda sai a sannan ya saki hannunta,

tace’ ita kuma lafiya?? Me aka Mata haka?
Yana wuce yace wai sai taje gidan wa’ancan yaran. Shine na hanata take wanann cikar tana batsewa jira nake Naga zata fashe ko kuwa,
Kamar tayi kuka

tace’ wallahi mama sako Zan Kai masu fah, shine uncle ya hanani.
Maman ce ta kalleta

tace’ rabun kar ku hadu yanzun nan suka fita,don sai da driver ma ya fita dauko ku da jimawa sannan suka fita, na ma ji mamaki da basuje tare an dauko kuba.
Batajira me zatace ba ta dawo ta zauna,daman uncle ya Shiga ciki,itama tana tura Baki ta Shiga dakinta,dukda yunwan da take ji sallah kawai tayi ta kwanta, ko abincin ma bazata ci ba,ai taci a jirgi a haka bacci ya kwasheta.

  Karfe shida,ta fito takalmi a hannu  tana sanda zata fice Dukda ba Wanda zai jita,kowa na dakin Shi,Amma haka ta fito sai sanda take abinta har ta fice daga gidan, gate ma ba kowa mai gadi Yana dakinsa, bude kofa tayi ta fice abinta sannan tasa takalmin ta, gidan su tayi knocking a hankali,Jin shiru yasata tayi da Dan karfi, ta Dan jima ba'a zoba ta Kara yin wani knocking da karfi,kawo yanzu kuwa zuciya ta ciyota zata kuma taji ana Shirin budewa,ita kadai takama Mita,Yana bude Mata ko gaisuwa da ta Saba yimasa ma batayi ba ta shige kamar zata tashi Sama Dan sauri, Saida taje kofar parlourn ta ja ta tsaya watakila ma kofar bude take,zagawa tayi ta kitchen tana addu'ah Allah yasa a bude kodan saboda masu aiki ma tasan ai a bude ne,aikuwa tana zuwa ta murda taji a bude,hamdala tayi ta Shiga,sai da ta cire takalim tukunna, sannan ta Shiga, direct part dinsu ta nufa,tana zuwa ta bude kofar parlourn Allah yasota a bude take kodan ai anyi sallahn asuba shiyasa,ta raya ranta,.

Tsayawa tayi tana doubting ta Shiga ko kar ta Shiga,tunda suke sai dai ta tsaya a iya parlourn su tun suna yara,bata taba Shiga ba,tana nan tsaye kawai ta yanke shawaran shiga, nufar bedroom din da suke kwana tayi,tasan tare suke kwana tun suna yara har yanzu. A hankali ta bude kofar dakin ta leka kanta ciki suna kwance cikin bargo suna bacci ga wani irin sanyi da dakin ya dauka saboda acn da suka kwana, Shiga tayi taje ta kashe acn ta dawo ta tsaya akansu,taya zata tashesu yanzu? Tasan ko ta Kira sunan su indai sunji itace to baza su tashiba, bottle water tagani akan center table din gabanta,dauka kuwa tayi ta je ta yayyafa masu, aikuwa a tare suka tashi don yin masifa a tunanin su sun zata Sameera ce,ganinta a tsaye yasa su Kara Shan kunu,
Basuyi mamakin ganinta don ta Riga da ta saba,indai da labari kuwa,Suma kuma suna zuwa gidan su, yaseer ne,

yace’ fice mana a daki,
Ganin ta tsaya tayi folding hannayenta ta tsaya tana kallansu yasa Yusuf

yace’ Baki ji abinda aka ce maki ba?
Sai gani sukayi ma tasamu wuri ta zauna a bakin gadan,

Yaseer yace’ wallahi idan Baki tashi ba Zan turaki ki fada daman ai bamu muka kiraki ba da zaki shigo mana daki ki tashemu a bacci banza kawai?
Daura kafa tayi daya kan daya ta bude envelope din hannunta ta zaro hoton Ummusalma guda daya ta ajje a tsakiyar su tare da cewa” kunsan wannan??
Rige rigen daukan hoton sukayi ganin kamar yaya, kowa ya rike gefen hoton suna kallo, tabbas itace ba abinda ta Kara sai farin sai kuma abinda ba za’a rasa ba.
A tare suka kalli suka furta YAYA?? sannan suka maida kallansu ga ummu da take kallansu tana wani murmushi tana kallansu ai a sukwane suka diro suka dawo gaban ta yaseer da sauri

yace’ a’ina kuka hadu?taya kukasan juna? har tabaki hoton ta? Ca kikace kin samu? Fada mana,ki fada mana ya labarin ta yake? Tana nan lafiya? Ba abinda yake damunta? Tana magana kamar da? Kunyi magana sosai da ita ne? Ki fada mana mana,
yafada ya Dan dukan kafar ta irin yi sauri dinnan.
Kallan su tayi

tace’ tace tana gaida ku,kuma zata dawo very soon,kuma ta bani wannan ba Baku,ta fada tana Mika masu envelope,
taci gaba dacewa kuma ta karbi numbern ku zata kiraku Sannan tace ko munyi fada ku dena yin fushi Dani kuma( Hajiya ummu harda Karin ),
Yusuf ne ya tashi tsaye

yace’ meyasa, meyasa,meyasa Baki karbo numbern ta ba? Ke kika bata tamu ? why,why zakiyi haka ehh?
Itakam Sam tunanin Amsar numbernta bezo mata ba,kawai numbers dinsu ta bayar harda Tata,ai tasan zata kira,

tace’ ai tare ma da ita muka……..
Sai ta tuna abinda ta fada Mata tace kar tafada tare suka dawo “ohhh God tafada kasan makoshinta, tana dafe goshi,
Da sauri Yusuf yadawo

yace’ tare da ita kuka dawo ko? Fada min ehh? Tare ne ko?
Ganin tayi shiru tana kallansa yasa

yace’ nasan tare ne ai,nasani tunda kika ki karasawa nasani,me tace maki?
Yafada kwalla ta cika idansa, shikuwa yaseer hotan kawai yake gani yana kuka, tuno rayuwar su da ita,
Kallansu tayi ganin halinda suke ciki, don kawai suna son ji labarinta,su Basu da saurin kuka koda kuwa an dakesu Amma,zata iya cewa bata taba gani sunyi kuka haka ba, numfashi taja sannan Ta Basu yarda Akayi suka hadu,da labarin da ta bata da komai da komai har kawo dauko su a airport.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page