A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Umma bataji suba tashi tayi ta fita neman Ummusalma, sukuma suka ci gaba wannan yayi wannan yayi, suka ci gaba da abin su, daga karshe, suka cigaba da wasu harda sharri a dangin miji,

Dangin miji ba’a iya musu ????♀️

Wayarta taji tana Kara bata ga Mai Kiran sosai ba ta daga Jin ance ga ta nan ta fito yasa ta wartsake ta tashi zaune, tare da kashe wayar,ta Kira tace’ ga tannan fitowa a mota civic red,ku Shirya kar ta gane ana binta ko kadan ko alama karta gani,
Ta kashe wayar,ta ta kwanta sosai baccin ta yayi dadi, gashi anzo an katse Mata ki Azahar ba’ayi ba, kwanciya tayi ta rufe Ido, ya fara daukanta Kenan taji an bude kofa an shigo an mayar an rufe a hankali ta bude idonta gaban ne ta doka ganin Wanda ya shigo, dakyar ta hadiyw yawo ta kulle idanta kamar mai baccin gaske,shikuwa bema Kula da ita ba, gajiya sukayi da yawo shine ya dawo gida, rigar jikinshi ya cire ya rataye ta ya zauna da singlet da Wandan rigar, juyowar da zaiyi ya ganta tana bacci hankali kwance kitson ya masa kyau,ita kanta ma ta masa kyau din,gadan ya hau ya kwanta kusa da ita sosai, Allah ya taimake Shi don tunda safw da yazo Umma ta hana Shi ganinta sai gashi yanzu tazo har dakinsa kuma yasan batasan da zuwan shiba da tasani bazata zoba, kwanciya ya gyara ya daura kansa a pillown ta Yana kare Mata kallo, ita dai gabanta ne kawai yake faduwa Addu’ar ta Allah yasa kar idanta ya kifta, a hanlyya sunkuyo daidai fuskarta ya daura bakin Shi a Sama nata,a sukwane ta bude ido ta kwalalo su, yarda tayi yasa Shi dariya Amma beyi ba sai da ya Gama abunsa muryan can kasa kasa,

yace’ wannan zuwa gaisuwa ya min dadi,
Da wani irin murmushin yayi maganar,

Daure fuska tayi ta kauda kanta, juyo da fuskarta yayi,
yace’ sai da aka gama zaki daure fuskan?

Shiru tayi babu amsa, zata tashi yayi sauri ya danneta da rabin jikinsa ya daura kanta a kirginta gaba Daya ya saukar Mata da nushin Shi,
Dakyar tace’ kana da nauyi fah,

Yace’ Ba ina maki magana Kina yimin shiru ko kuma ki kumbura fuska ba?

Shiru tayi batasan meza tace ba, yace’ kuma Baki ita bada hakuri ba,

Tace’ to Ka….Ka..wannan…imm…ka… ha..ku…ri..

Yace’ taam haka ake bada hakuri? Idan an hada fa Duka ca kikace Kaka wannan imm hakuri,
Yace’ taab ban amsa ba,

To kayi hakuri,

Sai dai na roka shima hakurin ko?

To ai nabaka,Ka dagani dakyar fa nake numfashi,

Yace’ a,ah bazan daga ba,

Ya ma Kara gyara kwanciyar sa
Tace’ Wayyo kirj…….
Sai kuma tayi shiru,bata karasa ba,

Yace’ mene?

Sarai yagane me take nufi Amma ya basar,

Tace’ da zafi Ka danne ni Ka daga ni Dan Allah,

Ina yake maki zafin?

Tace’ cikina ne, kuma sosai,

Ayyyaahhhh sorry,

Tashi yayi Yana cewa raguwa kawai, itama tashi tayi tana sauke numfashi,

yace’ Yana ga kin canza ne? Ko de nan zamu dawo da Zama?

Indai zaka zauna Zan zauna,

Hmmm naji Wannan,

Baka yarda ba?

Nace fa naji,

Batayi magana ba sai ma mayafinta ta dauka zata yafa
yace’ Ina zaki je?

Kumbura Baki tayi batayi magana ba sai da ya yafa zata harta sa kafarta zata sauka ya fardota ta dawo ta tsorta ainun sabida yarda ya fincikota,

Yace’ ba ina maki magana kin min shiru ba?

Marairaice fuska tayi tace’ kayi hakuri Dan Allah bansan me zance maka ba shiyasa,

Kada Kai yayi na irin zamu hadu, tace’ Dan Allah sake ni na tafi, yanzu haka ana ta nema na a cikin gida,

Sakinta yayi ta dauki dankwalin ta da waya ta taje bakin kofa zata fita,tasamu kanta da juyowa ta sakar masa wani kasallalan murmushi na kwantar hankali ta fice,
Tunda yake da ita bata taba yin wannan murmushi ba, ya tafi dashi, yanzu ma daurewa kawai yayi ya barta Amma yaso ace bata Shi ba sun kwanta tare Shi kawai yanzu wannan kamshin yake so, na jikinta.

Ita kuwa lallabawa tayi ta ta wuce cikin parlour har daki dukda akwai mutene Amma dayake da mutene ba lalle ne a lura ba,can gadan ta samu dan waje ta kwanta kamar me bacci, bata jima ba kuwa Umma tashigo tace’ wai har yanzu Salamatu Amarya ba’a ganta bane?

Aka fara ba’a ganta ba,tashi tayi
tace’ Umma gani fah,
Harda su kalar bacci irin daga bacci na tashi,

Umma tace’ yo mukayi fa nemanki fito kizo fitowa tayi suka fita.

Da yamma akayi kamu yayi kyau sosai da sosai ya kuma Ka yatar kowa ya yaba, washegari akayi walima,akayi wa’azi Wanda ya fadakar musamma ma su ‘yan kauye Wanda ba addinin akasa gaba ba kawai miji ya kawo ayi abinci a haihu shine kawai abin su ga bautar aure kamar kamar me,dai dai basuyi ruko da addini ba kalilan s suka San hakan damma suna yanzu suna karatu shine ma saukin abin. Sosai aka fadakar kowanne bangare kuma an Karo sosai.

Washegari da wuri suka fara shiri Wanda zasu Kai amarya, Basu wani yi gayya da yawa ba, mota biyu ce karfe tara mai kyau suka dau hanya. Awa Hudu suka diba suna tafiya direct gidan su Binaif aka wuce da ita a parlour akayi masu masauki sannan Hajiya ta fito tana wani yatsina tana cika, suka gaisa, Anty ma haka suka Dan gaisa de sama sama, Matar Baba Usman,
tace’ to Allah ya kawo mu bikin Binaif ga kuma amarya Ummusalma, ba’a bude muka ku ganta……

Manage pls….

By: ”’Hijjart Abdoul”’
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: A BAKIN WAWA
Akanji magana

  30

Dagowa sukayi suka kalle Shi Dan murmushi yayi Wanda iya fatar bakin ya tsaya beje ko ina sannan ya samu wuri ya zauna ya Dan kurbi lemu, gaban Shi faduwa kawai yake,

yace’ sannu fa,

Namijin yace’ Hi,

Karar wayar Shi yaji yasa Shi daga wa ganin ita ce,

Tace’ banga kana wani abuba sai San lemu Allah zamu tafi mu barka,

Adan wayince ya juyo ya kallesu,ya juyar da kansa,

yace’ sannu fah,

Namijin yace’ ina de lafiya?

Sameera tace’ Kawai kazo Ka samu a gaba?

Tace’ baeb mu tafi abimmu,

tashi sukayi zasu tafi Yana rike da hannunta ta gaban Shi suka zo zasu wuce mesan what comes his mind ba yade ba daga zuciyar Shi shawarar ta fito sai gani yayi ya rike hannunta, juyowa tayi ta kalle shi,

tace’ wai Kai lafiya?

Namma shiru yayi Shi kawai hannunsa yake kallo da ya rike Yama kasa magana,dakyar ya samu kalma biyu,

yace’ yi hakuri,

Cikin fasifa tace’ sake min hannu ko na zabga maka Mari a nan wurin mu jawo ‘yan kallo,

Sakinta yayi
yace’ am daman a wannan Kaduna,

Wayarsa dake hannunsa tayi kara message ne ya shigo kafin ya dago ya gansu sun gifta Shi, binsu yayi Yana Kara Karanta abinda ke ciki, ta kusanta ya je,

yace’ am daman fa a Kaduna na sanki,nazaci wacce nasani ce shiyasa ma har na rike Mata hannu,kiyi hakuri fah,

Namjin yace’ Kai tafi a anan wurin ba ita bace,

Besaurare Shi ba don beda abinda zai fada masa, shiyasa yayi shiru sai,,
yace’ kiyi magana mana koba Sameera bace?

Ja tayi ta tsaya tabbas kuwa ya Santa Amma ita batasan Shi ba ai, shima tsayawa yayi ya Dan kalli wayarsa,

yace’ Nasan kece wacce nasani ai, bazaki tuna ni ba ai, Amma ni nasanki,

Namijin yace’kar ki Rena min wayo mana, Sarai kin San Shi Ashe daman bani daya kike kulawa ba ko?

Message yaga ya shigo wayarsa,
yace’ ni zan tafi sai wataran Kenan?
Bejira amsar ta ba yayi gaba ina ruwan Shi abinda aka sashi yayi besan cewa fada tasa Shi hadawa ba,

Sameera tace’ aww daman kana tunanin Kai daya nake kulawa? Nasan cewan kana da ‘yam Mata kalata sunkai goma ko fiye dahaka bakai daya bane,

Yace’ Naji karki Kara kulani tunda ke mayaudariya ce kuma zaki sane kinyi Dani,

Tace’ nasaba Jin Kalmar nan a bakin mutane da yawa,wato ga banza ko? Kai kuma mene? Har gwara ni Bana lalata da samari Kai fa? Meye bakayi ? Waye besan halin Kaba? Kowa ya kama rabansa medame ni ba, banza kawai shasha,
Tasa Kai tayi gaba abinta,shikuwa Yana tsaye kamar gunki tunda yake da mace sai dai ya gama amfani da ita ya yar a bola bolarma wacce za’a Kona bazata anfanu ba, Amma wannan babu abinda yayi da ita niyyar Shi yau yayi duk abinda yi da it gashi yanzu komai ya wargaje beje ga komai ba, beyi tunanin ma bata sanshi haka ba,tunda suke bata taba daga masa murya ba sai yau, shima tafiya yayi ya bar wurin,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button