A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL
Wani irin kuka suka hade Kai da gwiwa sunayi,ita de kawai kallansu take yi itama ta Dan share hawayen ta, a ganinta farin ciki zasuyi Amma sai akasamu akasin haka,suna kuka to kukanne batasan na meye ba. Bayan ta share hawayen ta
Tace’ to wai kukan na meye haka? A ganina na farin ciki ne ai,
Yaseer ne yace'” farin ciki? Kinsan kukan da mukeyi ne? Kuka ne na danasani,kuka ne na danasani,yanzu kinji ?
Danasani kuma? Ta maimaita cike da mamaki,
Yusuf ne ya dago a zuciye
yace’ ehh danasani, Shi mukeyi don Allah ki tafi ki barmu mungode,don Allah,.
Yafada yana hade hannayensa wuri daya, ya cigaba da kukan sa,
Tace’ nifa ba inda zanje sai kun fada min, danasanin meye kuke kuka haka? Maimakon kuyi farin ciki ta dawo,Amma ku zauna kuna kuka?
Wannan Karan yaseer ne ya hada gumi sharkafi ya dago da kansa Yana jan majina
yace’ danasani ne na rashin bin drivern ku dauko ki,da’ace munje mun dauko ki kamar yarda mukeyi kullum da mun hadu da ita ai, da kuma ace munbi maganar Anty( maman ummu). Da duk haka bata faru ba,daman ance binna gaba bin Allah,gashi nan fushi da zuciya ta kaimu ta baro.yaya kiyi hakuri ki dawo don Allah,
Sai yanzu ta gane Inda maganar sa ta dosa tabbas kuwa mama ta fada Mata Amma batace tace su bi driver a dauko suba.
Tace’to yanzu ku daina kuka kunji ko? Tunda tazo basai mu fadawa umma ba(maman su) a bincka ko abada cigiyar ta ba kaga sai a samu ta dawo gida ai ko?
Da wani speed Yusuf ya dago cikin wata irin murya mai Kara
yace’ kina hauka zaki fadawa mama? Ida kika fada Mata Tou ko sun samota cazasu ce Basu ganta ba, su turata ga halaka, wannan Karan na tabbata kungurumin daji zasu kaita,damun daji su cinyeta, shikenan mu kuma kin samu a uku ko?
Kanta ne ya wani uba daurewa bata gane Inda zancen ya dosa ba, zasu Kara sa turata ga halaka??? Mekenan? Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un bata gane ba,
Tace’ kunga ku ganar Dani mana meke faruwa ? Bangane ba? Naga de sunan baban ku daya,kuma yar gidan ku ce? Ba Abba bane ya haifeta ba?
Yaseer
yace’ Yaya itace cikwan farin cikin mu,yaya itace komai namu tun muna kanana,da yaya muka fara bude ido muke gani a matsayi mai Kula damu,dukda Yusuf ya girmeni da shekara daya,itace ta reneshi har aka haifeni, ta hada Dani dashi ta rena,bata da wani buri Sama data faran tamana koda zata bakan tawa wani ko ita kanta, she’s sacrifice alot of things for us, shes can do anything for us,yaya tun muna yara take Kiran mu da Yusseer wato Yusuf and yaseer, yaya ce ta fara koya mana karatu,dukda ita bata maida hankali Akan karatunta amma kome aka yi Mata ta iya,indai har zata tsaya ta koya din,Amma kuma bata tsayawa tanayi ba ruwanta da karatu Bama taso,kuma mama bata Mata fada Amma mu tana mana fada sosai musamman akan karatu. Ada ba abinda ta iya sai mana wanka da shirya mu,suka dai mukasan ta iya don ko kunna gas da bata iya ba, Akan mu ta iya mota saboda fitar da muke any how,ita zata kaimu school sai ta dawo ta shirya taje Tata,bata damu ba don ta makara,abinda tasani shine karmu makara,daga makarata take wucewa ta dauko mu ,Idan mundawo ta samu muyi sallah tamana wanka, tasa mana kayan islamiyya, sannan ta kaimu,sai ta kaimu islamiyya sannan zata cire uniform dinta, tun muna yara tayi damu mudena fada mukaki jinta , tace nake cewa Yusuf Yaya naki fada, kullum sai tai rabiyar fada idan ba ita ba ba wanda ke iya raba mu, bata da lokacin kanta sai namu, Yaya taje cell saboda mu,ba Wanda yasani saI mu sai Allah,bata damu ba, yaya ba ruwanta,tana da tausayi,kuma bata da mutunci,don kaf ma’aikatan gidan tsoron ta suke ji.
Watarana zata kaimu islamiyya har mun Shiga ta manta bata dauko kudi ba kuma bamu dauko abinci ba, wataran muna tafiya dashi sai tabi ta kofan baya don ta dauko abincin,komawan da zatayi bata dawo ba sai gajiya mukayi muka taho don mu ganta,Jin numfashi a garden yasa mukaje wurin,muka Kira mama,tundaga wannan rashin lafiyan ta koma wani rin shiru bata magana,dazaki Mata magana dubu to nodding Kai zata maki sau daya,tun muna damuwa har muka saba, da shirunta,ta kuma rage kaimu park da duk Friday da Thursday idan an dawo daga school Bama Zama muna park,da can ita ma bata San zuwa gidan kawayen Mama, shiyasa wani zabin muke wuni a park wani zubin kuma mu yi a gidan kawayen ta,
Alokacin da zata tafi karatu mama tace mana idan ta tafi bazata dawoba,koda na fada Mata tace min zata dawo,amma kar na fadawa kowa sai Yusuf, munyi kuka har Abba Saida ya zane mu,a lokacin Yusuf ke fada abinda mama tafada lokacin muna bacci tace,wai yaya bazata dawo ba kuma zamu manta da ita a rayuwar, abinda Yusuf yayi tunanin zata mana irin abinda akayiwa wani abokin mu,muka dena yarda tana zuba mana abinci sannan kome tabamu bamu ci,ko ta tambaye mu yaya sai muce bamu Santa ba, saboda ita aka tashi daga wancan gidan muka dawo wannan gidan.
Ya kifa kansa Yana cigba da kuka,
Yusuf yace’ Akan me zaki ce mu fada mata, cewar yaya ta zo?
Kwallan dake zuba a idanta ta share
tace’ me zai Hana to mu nemota?
. taya zamu ne mota? Ya tambaya,
Zamu ne mota mana indai a fadin garin nan take?
Yaseer yace’ ehh haka ne zamu iya nemota,amma dole sai ta temakon Isiya driver (drivern ta)
Isiya kuma ? Wayeshi) ta tambaya tana kallansu,
Yusuf ne yace’ drivern yaya ne,Amma meyasa kace haka,
Ya tambaya Yana goge hawayen idan sa yana kallan yaseer shima yaseer din hawaye yake gogewa
yace’ lokacin da zata tafi London tana yawan fita,idan zaka tuna har tambayanta muka sha yi Amma bata Kula muba, Shi zai tamaka mana,
Amma de kasan baya gidan ai ko?
Wannan duk mi sauki ne,zamu iya nemansa ko ta wurin mai gadi ne ,nasan suna gaisawa ai.
Tashi tayi tace’ ni Bari na tafi ,kunsan tare da uncle mukazo,idan anjima kuzo ku gaisa dashi,daman Baku taba ganin sa ba bako?
Wanda mukace Yana kama da yaya? Yaseer ya tambaya
Ehh,Shi sai kunzo,ta fice.
????????????????????
Gida ta dawo lokacin wacce zata kaita aiki ta zo,gaisawa sukayi ta fada Mata bukatar ta,dakuma unguwar da takesanyin aiki da gidan idan za'a samu, matar mai suna Ladi
tace’ to kinga gidan da kike fada de Gaskiya yan gidan basu da kirki, don nasha Kai mutane Amma suna guduwa bazasu iya ba,bare ace ke, kuma a matsayin kurma ko nace bebiya kinga kwa ai da matsala, Amma Idan zaki iya bakomai duk mai sauki ne,
Jinjina Kai tayi sannan iya ladi taci gaba da fadin, yanzu zanje gidan Idan tana nema, to kobata nema ma zanyi yarda zatayi ta dauke ki aiki.
Kudi ta Ciro ta bata tace tayi kudin adaidaita, godiya tayi ta fice, tace'” naji damus ai yanxu zanje nadawo ma ina dalili taab,watakil ma a karamin,ni ina ruwana koma yar leken asirice be dame ni ba.
Maman Sadiq ce tace' Allah yasa de asamu,
Ameen tace, su nan suna hira matar ta dawo bata jima ba,
Tace’ ai anyi dace,amma wai aikin ki gyaran Parlour ne Sama da kasa sai daki idan ance kiyi,da kuma aiki haka de,Amma fa Gaskiya akwai wulakanta mutum ato Gaskiya ce,
Ca tace’ bakomai,yaushe kuma zamuje ?
Yau da yamma nace Zan kawoki,sai ki hada kayanki,Idan kun Gama zuwa yamma sai ki kirani Fatsima(mama Sadiq),amsa Mata tayi sannan ta fice,
Maman Sadiq tace’ to yanzu bari na hado maki Yan tsuffin kayana da zan bayar sai ki tafi dasu ko?
Bata jira amsar ta ba ta Shiga daki ta kwaso kayan,ta ajje,waje ta fita wani store ta dauko tsohuwar Ghana most go ta goge ta tas ta zuba kayan a ciki
tace’ kuma Riga daban zani daban sannan dankwali ma daban,haka masa aikin keyi,wayanci de, bansan mezaki je yi ba Amma koma meye nasan ba abin cutarwa bane dukda Baki fada min ba. ta bude Baki zatayi magana