A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace’ Umma ba jimawa ba zamuyi ba,yanzu zamu dawo,

Umma tace’ ina ruwana to,mude a zamanin mu idan aka Kai mace gidan mijinta ko leka kofa batayi sai tayi shekara cis a dakinta, Kai wata ma sai ta haihu,wata kuwa bata haihuwa sai ta shekara biyu,uku,hudu Kai har shida ma sannan wasu zasu fita shima sai an zubda wanka,kuma idan mace ta fita a ranar take dawowa gidan ta ba irin yanzu ba,

Yace’ Haba Umma da kikace da da dayanzu ai ba daya bane komai ya canza,

Tace’ Allah ya Baka hakuri fada maka nayi ai,ko kaima zaka yiwa matar haka, sai kun dawo.

Ummusalma tace’ sai mun dawo,
Shikuwa ko magana beyi ba,
Ya Riga zuwa hakan yasa ya bude mata kofa shima ya zagaye ya bude ta Shi,Shiga tayi tana mamakin wannan labarin da Umma ta basu,anshe da sun shade wahala.
Bayan sun dau hanya ta fada inda zasu,suna tafiya shiru babu mai magana ita tana kalle kalle shikuma yana tuki, katse shirun yayi da cewa’

‘ Kinsan wani abu?
Sanin da ita yake ta girgiza Kai,

yace’ anfa Bani shawara,kuma shawara ce mai kyaun gaske nake fada maki,

Ganin kamar Yana so yaja da magana,kuma da alama de bayansa shirun nan nata,

tace’ Wacce shawara ?

Yace’ ahh wacce Umma ta Bani mana,

Tace’ dayaushe?

Yace’ yanzu da zamu fito,kinga daga yau bake ba fita sai kin haihu,

Kallanshi tayi dakyau tace’ sai na haihu kuma?

Yace’ yes,of course,idan kin haihu a shekara daya to kina so ki fita idan ma kin haihu a shekara biyu Kinsan fita,Amma Baki haihuba a wannan shekararun bake ba fita,wasu ma har sun manta dake,

Kumewa tayi tace’ wai maganar nan dakeyi daga zuciyar Ka take fitowa kokuma daga bakinka,nakasa fahimta,

Yace’ zuciya tamana sannan Baki na yake fada ,kinsan ana cewa abinda babba ya hango ko ya hau ina ne bazai hango ba,

Banza tayi ta kyaleshi,har suka karaso unguwar

yace’ kinde San ni ba aljani bane da Zan San ko ina ko?

Da hannu ta fara mai kwantance,samun wuri yayi,yayi parking
Kallanshi tayi dakyau
.
tace’ lafiya?

Yace’ Naga kin Zama kurma,ni kuma banzama ba,shiyasa gwara kawai mu zauna haka,

Tace’ amma de kasan ai yamma tayi yanzu ko,kuma yanzu magariba zatayi daman bamu fito da wuri ba,

Yace’ to Ashe kina magana haka,

Bata yi magana tama juya tana kallan wani wuri,motar ya tada,

yace’ Madam ina muka nufa,
Nuna masa hanya ta fara yi har suka isa, fita tayi ta Shiga gidan da yake opposite dana Maman Sadiq, Sallama tayi aka amsa sai da suka gaisa,

tace’ maman Sadiq ce ta aikonj Zan amsa key Zan dau sako,
Zasuyi sa’anni da matar gidan,

tace’ eh ta fada min Amma meye sunanki?

Tace’ Ummusalma,

Tace’ ina zuwa,
Koda Shiga sai ta Kara Kiran maman Sadiq ta shaida Mata, sannan ta dauko key din ta bata,

Fitowa tayi janye da trolley dinta da kuma wata jakar a hannun ta, fitowa yayi daga mota ya zo ya ansa jakar ita kuma ta maida key din,
Gidan dake kusa da na Maman Sadiq ta kalla da ta Shiga gidan Maman Sadiq taji haniyarsu da’alama ball suke a tsakar gida, mota ta Shiga ta zauna,

yace’ kinsan masu gidanne?

Gida nane,tace
Kuma Baki Shiga ba,tace’ su yaseer ne fa a ciki,
Kunna motar yayi ya fara tafiya,
A cikin wani store taga sunyi parking,

yace’ zaki Shiga ne?
Girgiza Kai tayi alamar a,a, fita yayi ya shiga,har ya shige tana kallansa, sannan ta maida kanta jikin kujera ta rufe Ido, ita abin ma Mamaki yake bata wai itace da Miji abinda batayi tsammani ba, gashi kuma ko kadan daga cikin mission dinta bata kammala ba, dole ta dage idan har tana so ta cimma burinta, amma taya zatayi hakan?
Kamar ance Mata ta bude ido ta juyo wurin windown ta, idan ba gizo idanta ya Mata ba Neena tagani fa, ai da sauri ta bude kofar ta fito sai dai kafin ta karasa har ta fice ta hau a daidai ta sunyi gaba tsayawa tayi tana kallan masu adaidaitar tabbas Neena tagani,dawowa tana mamakin ganinta da tayi Ashe hassashenta daidai ne Kenan ba barin garin sukayi ba,suna nan acikin garin amma ai gari da fadi a,ina ?? Security din wurin ta samu,

tace’ don Allah wacce ta wuce yanzu nan daga ita babu Wanda ya fito tana zuwa nan wurin sosai ne?

Securityn yace’ taya za’ayi na gane Wanda suke zuwa fa dayawa,

Tace’ ehh nasani amma idan mutum Yana yawan zuwa dole zaka Santa,

Yace’ munsan wasu ma dayawa Amma gaskiya itade bansanta ba,
Numfashi taja tace’ to ku nawane masu shifting din nan wurin?

Mu uku ne,daya bezo ba ga daya can kuma daga ciki, godiya ta masa ta nufi wurin na cikin,Yana zaune taje tayi masa sallama

tace’ am wacce ta wuce nace don Allah ko kasanta ? Tana yawan zuwa haka?

Yace’ Wacce Kenan Aminatu?
Ita kadai ta wuce ai,yanzu sai kuma Maza da suka fita yanzu,

Tace’ ehh Kasan tane?

Yace’ ai unguwar mu daya da kafin su tashi, ni kuma ana nake aiki, to gaskiya kwanan ina yawan ganinta tana zuwa kuma indai tazo tana zuwa mu gaisa,indai ina nan.

Tace’ to shikenan yanzu zaka Bani numbern Ka duk ranar da na samu lokaci Zan kiraka,
Numbern Shi ya bata tasa a wayarta,ta Ciro kudi ta bashi,sosai yayi godiya mota ta dawo ta zauna har yanzu be dawo ba,
Ji tayi an bude kofa an shigo,gani Shi da ya ajje kayan hannunsa a baya,

Tace’ ice cream,

Yace’ da kinsan kina San ice cream kikayi shiru ban siyo ba kuma bazan koma ba, kuma kema bazaki fita ba,

Kumbura Baki tayi tace’ da nace Zan fita ne?
Batasan a fili tayi maganar ba,

yace’ me kika fita yi? Naga kina magana da wancan security din?

Tace’ Neena na gani fa, Amma ban Mata magana ba ta hau abin hawa ta wuce, shine na tambayi security yace tana Dan zuwa akai akai kwanan, shine na amsa numbern sa watakila yasan inda suka koma ko?

Gingina Kai yayi yace’ hakan yayi,Amma kar ki sake magana da wani sai da izinina kinji ai?

Daga masa Kai kawai tayi, alamar taji,
Suna tafiya aka fara Kiran magriba, suna zuwa gida wasu masallaci sun idar,Kayansa ta kwasa ta fita da su,bakowa a parlourn sai Tv shikuma masallaci ya wuce daga nan,
Itama sallah tayi ta zauna tana Azkhar bayan ta Gama kuma ta tashi ta Shiga wanka tana fitowa Yana shigowa da akwatinta bata ma lura dashi ba ita sai da tazo tsakiyar dakin ta ganshi, murtuke fuska tayi ta janyo hijabinta a Kan gado ta rufe jikinta, ta wuce wurin mudubi,

Yace’ ikon Allah, to mene na rufe jikin kuma? Ke kina sani de,ya ajje mata Jakarta har zai fita sai kuma ya dawo ya bude ledar da ta shigo da Shi, comp ya dauko da main kitso da ribbon yazo ta bayanta

yace’ tunda Allah ya hadani da wacce batasan gyaran gashi,ni Bari na gyara mata,
Ta jikin mirror take kallansa bata iya musu ba,ita kuwa zata ga ikon Allah Namiji da gyaran gashi…..

By:Hijjart Abdoul
Cwthrt ????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ???? A BAKIN WAWA ????
Akanji magana

          24

Yace’ thanks,

Haka nan ta ji dadi a zuciyar ta tare da wani farinciki, bayan ya Shiga wanka,itakam tasan indai tana tare dashi ji take gaba daya damuwar ta yayewa take baza ta iya fassara yarda take ji ba, kitchen taje ta zubo masa abinci har lokacin bai fito ba ajiyewa tayi a akan center table din dakin komawa tayi ta dauko ruwa tare da cup ta dawo ganinsa daure da towel yasa ta saurin dauke kanta taje ta ajje zata fita taji ya rike hannunta, gabanta taji ya fadi janyota yayi,

yace’ ina zaki kinga mijinki ya fito a wanka shine zaki fita ko?
Fuskarsa ya daura a kan wuyanta ya zagoyo da hannunsa ta cikinta,

yace’ ina magana,

In ina tafara tace’ am zan dauko wani abu ne fa,
Tana yi tana kyafta Ido,
Zaiyi magana wayarta tayi kara sakinta yayi taje ta dauko wayar amma yana sakinta tayi waje harda hadawa da gudu, murmushi yayi yaje zai shirya jin wayar na kara har yanzu yasa shi zuwa ya dauka, yasata a silent Chatty yagani a jiki, dauka yayi ya kara a kunne muryan Wanda yaji yasa shi sakin boyayyiyar ajiyar zuciya daga can bangaren akace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button