A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????

~Nigeria~

Yusuf da yaseer ne a dakin Ummusalma suna dauka abinda suke so na Zane da kuma hotunansu sosai suke jidar kayan sunayi suna leka window ahaka suka kwashe suka Kai mota suka dawo suna Zama kuwa mama nashigowa 

tace’ yawwa yau zamu tashi daga wannan gidan mukoma wani,ku dau abinda kuke so ku dauka,kunji ko?
Kallan juna sukayi suka ce tou
Sama tahau gani Suma tashi sukayi don su haura Saman gani sukayi tana rufe dakin Ummusalma,dakin su suka Shiga, yaseer

yace’ yanzu dabamu ji zamu tashi daga gidan nan ba shikenan ko?
Yusuf yace’sai kuma Allah yasa munji,
Zama sukayi suna buga game,abinsu
Mama ce ta leko ta gansu

tace’ au wai daman ba hada kayan kuke ba?
Kallanta sukayi yaseer

yace’ a Kira Indo ta hada mana kayan mana,ni banzan iya ba,
Yafada ya turo baki,
tace’ ehhh tunda Indo ce tasan abinda kuke so ko? To idan tazo gaba daya kayan zata kwashe ta bayar,na bata kayan duka,shiyasa nace ku debe abinda kuke so,kuma Bana San tarkace kunji ni ai?tafada tana barin wurin,kallan juna sukayi sannan suka dauko school bag dinsu suka sa games dinsu aciki sai abinda ba’a Rasa ba wasu ma a hannu suka riko,suka fito,mota suka Kai kayan suka dawo, kallan su mama tayi

tace’ kuje Driver ya kaiku gidan,
Tashi sukayi suka fita.
Gidan ya hadu iya haduwa zaka iya rantsewa ma ba’a kasar yake ba don haduwarsa yayi kyau sosai Saida muce Masha Allah,
Sun yaba tsarin gidan sosai kuma ya musu kyau bakadan ba,don harda wurin buga ball,yayi kyau sosai da sosai.
Suna gama zagaye gidan suna parlour suna Kara ganin gidan, Mama ta shigo wannan Karan dakinsu a kasa yake,da parlour aciki sai Dan karamin kitchen da toilet a parlourn,su kuma kowa da dakin shi,sukam sun Saba da Zama daki daya,tunda Basu taba rabuwa kuma basa Jin zasu rabu,fita sukayi suka dauko kayansu a mota,suka dau daki daya suka zuba kayan da suka dauka a dakin Ummusalma,dayan kuma suka saka kayan su anan zasu zauna acewar su.
Sosai suke baza hajarsu agidan suna wata yawa.Makaranta ma ancanza musu wata sunso ace sai zasu Shiga js2 asake tunda yanzu suna js1 kuma second term Amma a haka aka sake masu,basu so ba,haka sukayi mitar su suka gama,sunyi kawaye maza da mata abinsu don akwai wata yar anguwar su suna cemata Yaya wani sa’in sabida wai sunan Ummusalma ne da ita,ita kuma ba laifi akwai San girma,sosai suka shaku da ita wataran ma tare ake daukosu ko akaisu tare,har suka dawo idan aka kaisu agidan wannan to wani satin za’a kaisu a gidan wannan haka suka zama. Kuma hakan bai sa iyayen zumumci ba………

By: Hijjart Abdoul
Cwthrt????
[7/14, 3:57 PM] Hijjart????: ????A BAKIN WAWA????
Akanji magana

     8

A bangaren Ummusalma kuwa balaifi don ita yanzu ta saba sosai da hakan da take,kuma bayan wanke wanke da take a restaurant,yanzu har girki takeyi,takan gani wani sa’in yarda sukeyi da haka ta koya,aikim Zane ma ba laifi yanzu takan zana ma takai ko ba’a ce ba tunda sun fi son zanen nature,kudi sosai takeyi abinta.
Gashi yanzu sungama year one zasu Shiga ta biyu,kusan kowa sun tafi gida sai yan kadan kamar wancan lokacin. Ahaka ta cigaba da zuwa aikin ta kasancewar ta dena zuwa da weekend yasa take karatun da za’a masu nan gaba sosai kuma take ganewa.
Yau ma de tana zaune a bakin campus da yamma tana sanye da wando sai jacket datasa da baby hijab,karatu take yau weekend ba taje ko’ina ba,tana nan zaune taga wani ya zauna a kusa da ita,yana waya kuma da Hausa yake wayar wani sa’in Yana hadawa da Spanish,bata kalleshiba kawai taci gaba da abinda take kallanta yayi

yace’ Hello,
Bata tanka masa ba ta dan juyo ta kalleshi da sauri ta maida kallanta ga books dinta saidai gabanta da ya fadi,Amma Sam bata nuna ba,meke faruwa da ita ne???abinda tace a zuciyar ta Kenan,mai fuskar Baba ga kuma mai fuskar NEENA mekefaruwa???
Katse Mata tunani yayi ta hanyar

cewa” hey can I ask u?
Shiru tamasa,sai ma Kara Dan kallansa da tayi,zuwa yanzu taji zuciyar ta tadena bugawa shiyasa ma ta Kara kallansa,tabbas sunyi kama da ita sosai,amma Neena farace bata Kai hasken shiba,shikuma ja kuma jikinshi ya samu hutu, sabanin Neena. Ganin ta tafi tunanin ya kuma

cewa” please,
Dauke kanta tayi daga kallansa ganin haka yasa Shi cewa a fili” To ko kurma ce ne bata magana??
Daman tasan za’a rina indai cewa kurma badaga kanshi aka fara ba,sabida ko haushi ma bataji bare kuma tayi magana.
Joyuwar da zatayi taga ya fara Mata zancen kurame ikon Allah haka ake zancen kuramen?
Ganin irin kallan da take masa na irin mekakeyi?
Yasa Shi sararawa ya Ciro wayarsa ya kira wani bata sai ji tayi Yana

cewa” Nidai yunwa nake ji,ni banga kowa ba,sai wata kurma kuma nayi nayi ta gane takasa ganewa Itakam wannan a kurman ma ina ga ajin karshe ce,
Ita dariya yaso bata wai a kurman ajin karshe ce,hmmm kawai tace,batajin me aka fada amma da duk kan alamu lallashinsa ake,ganin yarda yake hade fuska, kallanta yayi,ya dauke yaci gaba da fadin bazaka gane ba ne yarinyar daman tayi kama da ifiritu gata da manyan ido kwala kwala da su irin na twiny gata da dan wani matsitsin bakinta in fada maka wannan badan kurma bace marar kunya za’ayi inaga ma ko a kurman ma bata da kunya,nifa tana min kama da twiny wallahi,Dan kamar ta baci ma,ya kareshe yana wani ya tsine fuska,
Batasan me aka ce Saida ganin yarda ya hade Rai Ya nuna fada ake masa, bayan ya kashe wayar ya juyo ya kalleta,

yace’ yunwa nakeji ki taimaka min kifada ko ki nuna min cafeteria ko restaurant ni bako ne masters aka kawo mu yi nida Dan uwa kuma baida lafiya yana can adaki kuma wai shine aka kawo mu tun yanzu don an tsanemu please ki taimaka kinga ni Yayanki ne ko? Duk maganar da Hausa yakeyi irin ita tace tana Jin nan yazage yana surutu,ita ta tambayeshi me yakawo shine ko kuma de kawai San asani wai gaida uwar miji a kasuwa,saida ta tattara kayanta na wurin, jakarta ta bude ta ciro wata leda,sai da ta tashi ta Dora masa a kan ciyarsa,har tayi gaba sai kuma ta dawo

tace’ bakai na bawa ba Dan uwanka na bawa.
Kawao tai gaba ta barshi a wurin,Baki a sake yake binta da kallo bai taba tunanin ta iya Hausa ba kuma daga ji ba wai koya tayi ba can dama ta iya,baid daina kallansa ba har ta hau sama ta Shiga dakinta sannan ya saki wata ajiyar zuciya,
yace’ Ashe ba kurma bace, Kenan taji duk abinda nace taaab,kawai sai yasaki wata dariya,

yace’ Allah sarki ohhh wataran tabbas Zan sha Duka idan na cigaba dayin abinda nake,
Ya jima a wurin Yana yiwa kansa dariya,daga nan kuma ya tashi ya tafi.
Tana kallansa yana magana Shi kaidai Yana dariya, dariyarsa iri daya da Neeena,ita mamaki ma abin yabata duk abinda ya fada akanta bata ji wani haushi ba. Koda ya tafi tajima a tsaye a wurin, balcony ta nufa ko zata sha iska,Zama tayi ta rufe idonta tana hango abinda ya faru tsakaninta dashi,tashi tayi ta zauna sannan ta kalli kayan Zane jitayi tana sha’awar zana shi,tashi kuwa tayi dauko kayan ta fara zane,mutane Biyar ta zana, kuma duk sai taga suna kama da juna, sunaye ta saka asaman kowanne,Neena ce ta farko sai Baba sai AA da Chatty(Wanda suka hadu) sai ita kuma a karshe,kallan Zane ta tsaya yi,tabbas sai yanzu taga kamar su suna kama da AA sosai haka nan da Baba Neena kuma nakama da Chatty,ta jima tana kallan wa’yanna fuskokin, zuciyar tace ta fara saka bata wani abu da sauri ta kauda tunanin tana girgiza kai,tana cewa bazai mata ba iyuwa ba hakan baza faru ba. Tana zaune a wurin har lokacin magriba, tashi tayi tai sallah tayi karatun Qur’ani, har lokacin Isha, fridge dinsu ta duba ganin bakomai lemo yasata Jan tsaki,kuma ita yunwa takeji gashi tayi burgar aiki ta bayar da nata, da hijabin jikinta har kasa ta ta fita Wanda tayi sallah dashi, tafiya take a hankali harta iso cafeteria, tagama siyan abinda zata siya juyowar da zatayi kuwa sukayi Karo da Chatty lemon dake hannunshi ya zubar Mata a hijabi shi besan ita bace kawai ya dago zai bada hakuri har ya bude baki sai kuma yayi shiru ya tsaya kallanta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page